Hotuna 10 kafin rayuwa ta sauya sakamakon yakin Ukraine

Rayuwa ta sauya ɓakatatan a Ukraine ranar 24 ga watan Fabrairun 2022, lokacin da Rasha ta ƙaddamar da yaƙi a ƙasar.

Ga wasu hotuna 10 da wasu ƴan Ukraine suka ce su ne hotunansu na ƙarshe a kan wayarsu kafin ƙasarsu ta sauya - sun kuma yi bayani abin da ya faru da su tun bayan nan.

Hotunan ɗauki-da-kanka

.

Asalin hoton, ANGELINA CHABAN

An ɗauki wannan hoton ranar 23 ga watan Fabrairun 2022 kuma yana nuna yadda nake tattaki a Gundumarmu. An kasance cikin kyakkyawan yanayi a ranar sai dai akwai fargabar wani abu na iya faruwa.

Na ɗauki hoton saboda kyakkyawan yanayin da aka tashi da shi saboda kuma na yi kwalliya. Yana wajen Kramatorsk a Gabashin Ukraine. Waje ne da nake son zuwa.

A makonnin farko-farko bayan mamayar Rasha, na kasance a gida, amma ranar 7 ga watan Afirilu, mun koma Yammaci - Vinnytsia daga nan kuma muka koma Kyiv.

Lokacin da na ɗauki hoton, na ji kamar daga wata rayuwar ta daban ce.

Angelina Chaban, mai shekara 24

Aiki daga gida tare da kyanwata

.

Asalin hoton, ANNA

Na kasance ina aiki daga gida a ranar 22 ga watan Fabrairu, ina amsa kiran waya tare da kyanwata a kusa da ni, ina jin daɗin rayuwata. Na ɗauki hoton saboda kyanwata ta kasance abin alfaharina.

Sunanta Fura. Ƴar uwata ce ta tseratar da ita daga bakin babbar hanya lokacin da take ƙarama.

A lokacin akwai kafafen yaɗa labarai da ke ɗaukar rahoto, alama da ke nuna cewa wani abu zai faru kuma mutane na ta magana a kai. Amma ina da yaƙinin cewa idan har lamarin ya ɓaci, ba zai shafi al'ummar farar hula ba.

A ranar 25, muka yanke shawarar barin Kyiv. Mun tafi da magen zuwa arewa maso yammacin Ukraine. A lokacin bazara, muka dawo.

Anna, mai shekara 32

Aikin makaranta

.

Asalin hoton, IHOR BEZRUKYI

Ɗiyata, Marta, ce ta haɗa wannan kyandir ɗin a makarantar ƙananan yara kuma ta kawo shi gida a ranar 22 ga watan Fabarairu. Ina tuna yadda na kasance cikin farin-ciki cewa yara suna da basirar ƙirƙirar wani abu kuma na yi alfahari da ita saboda ta yi ƙoƙari sosai wajen haɗa kyandir ɗin.

A lokacin ban san abin da zai je ya zo ba.

Ɗiyata za ta cika shekara bakwai a Maris amma tun 24 ga watan Fabrairun bara, rabonta da makaranta. Matata ta ƙi barinta.

Tun farko, na shiga damuwa cewa idan yaƙi ya ɓarke, iyalina da ni dole su rabu. Amma har yanzu muna nan.

Ihor Bezrukyi, mai shekara 51

Ci-maka tare da ƙawaye

.

Asalin hoton, VALERIIA DUBROVSKA

Ta kasance rana ce kamar ko yaushe kuma bayan aiki, na yanke shawarar leƙawa shagon ƙawata domin mu ci mu sha. Bayan nan, mun fita tare da su domin shan barasa da cin abincin gargajiya da barasa nau'in vodka.

Ba zan iya tuna takamaimai abin da nake ji ba amma na san muna ta yin abin dariya. Mun yi magana kan yiwuwar Rasha ta mamaye Ukraine amma sai dukkanmu a lokacin muka nuna wuyar haka ta faru.

Ƴan kwanaki bayan mamayar, na haɗu da wasu maza biyu da muka kasance tare. Muna ta taimaka wa sojoji kafa shingaye a tsakiyar Odesa.

Idan na kalli hoton yanzu, ina jin daɗi game da yadda na kasance a baya.

Ƙarshen mako mai tsawo a Lviv

.

Asalin hoton, SOFIIA DOROSHENKO

Wata ƙawata ta kawo min ziyara a Lviv a ranar da take ƙara shekara a duniya kuma shi ne ƙarshen mako mai tsawo na farko da na kasance ba na aiki.

Mun yi rangadi a birnin, mun kuma je duba wani wuri daga cocin Sts Olha and Elizabeth

Mune masu ziyara na ƙarshe a ranar, sai suka buƙaci mu rufe ƙofa idan muka gama.

Na yi matuƙar farinciki a ranakun. Na kasance ina murna tare da ƙawayena da kuma aikina. Amma akwai wani abu - tunanin wani abu iya faruwa kuma komai na iya sauyawa.

Har yanzu ina Lviv amma ban cika ɗaukan hotuna da wayata ba. Yanzu ina ɗaukar hoto da kyamara domin tattara abubuwan da ke faruwa.

Sofiia Doroshenko, 30

Lokacin iyali a gida

.

Asalin hoton, IEVGEN PEREVERZIEV

Na ɗauki wannan hoton na yarona na farko, Yaroslav ranar 19 ga watan Fabrairu a gidanmu da ke Dnipro. A lokacin watansa shida. Kariyata ma na nan - ta kasance babbar ƙawa ga ɗana.

Mun fice daga gidanmu ranar 24 ga watan Fabrairu. Na yi tuƙin kwana uku zuwa Yammacin Ukraine domin kai iyalina waje mai tsaro.

Gidanmu a Dnipro har yanzu yana nan amma babu kowa a ciki. Sai da na tambayi abokaina su gyara gidan saboda a lokacin da muka fice, firjin cike yake da kayan abinci.

Na kasance ina da wani kamfanin zirga-zirga amma a yanzu, babu batun yawon buɗe ido. A yanzu, na yi tayin yin aiki da sojoji, ina kai motoci ga sojoji daga iyakar kasar zuwa tsakiyar Ukraine. Kullum ina cikin tuƙi, tuƙi, tuƙi.

A tsukin lokacin nan, yara suna saurin girma. Wasu lokutan bana tare da su tsawon kwanaki 10 kuma idan na dawo sai na ga ya koyi wani abu sabo.

Ievgen Pereverziev, mai shekara 40

Wasan kusa da ƙarshe

.

Asalin hoton, BORYS SHELAHUROV

Mun ɗauki hoton nan ne bayan mun yi rashin nasara a wasan kusa da ƙarshe na gasar ƙwallon ƙafa a Kharkiv. Ni ne na ci mana ƙwallo ɗaya tilo da muka jefa a raga a karawar.

Duk da cewa an doke mu to amma ba mu damu ba sosai saboda mun taka leda sosai, ba mu da nasara ne kawai.

A lokacin ban taɓa yarda cewa yaƙi zai ɓarke ba.

Ina fatan cewa ga wani lokaci da zan sake taka leda da sauran 'yan ƙungiyarmu.

Borys Shelahurov, mai shekara 28

Koyon tuƙin mota da shan gahawa

.

Asalin hoton, OLEKSANDR POPENKO

Na ɗauki wannan hoton ne da kofin nan, na gahawa, wanda aka rubuta cewa ''Paris ina kaunarki'', a ranar 22 ga watan Fabarairu 2022 bayan darasin koyon tukin mota da na fito. Hoton yana daga cikin wani aiki nake yi na tara hotuna.

Muna zaune ne a Bucha inda muka shafe mako biyu a wani ɗakin ƙarkashin ƙasa na wata makarantar yara da ke kusa da gidanmu, bayan mamayar da Rasha ta yi. na rame sosai a tsawon makonni biyu nan.

Da ƙafa muka tsere wa mamayen na Rasha ranar 10 ga watan Maris, inda muka yi tafiyar nisan kilomita 22 wato mil 14. Lokacin da muka isa wajen bincike na jami'an tsaron Ukraine na farko, kaɗan ya rage na yi kuka.

Duk da wannan yaƙi da ake yi har yanzu ina ƙoƙarin hada wannan aiki da nake na tara hotuna. Kuma har yanzu ban kammala darasina na koyon tuƙin mota ba.

Oleksandr Popenko, mai shekara 29.

Wasa da abokai

.

Asalin hoton, ANDRII RYBKA

Ina aiki ne a cibiyar adana kayan fasahar al'ada ta ƙasa ta Lviv National Art Gallery. A kowace shekara a irin wannan lokaci na tsananin hunturu, gidan kayan na tarihi yana ƙawata wurin har zuwa lokacin ƙarshen hunturun, kuma ina jin dɗin hakan.

Kowa a birnin yana magana a kan yuwuwar ɓarkewar yaƙi. Ƴan kwanaki kafin ranar 24 ga wata, a lokacin ba mu san abin da zai iya faruwa ma sai na sa abokina ya ɗauke ne wannan hoton- domin kawar da hankali daga fargabar.

Har yanzu ina aiki a wannan gida na adana kayan tarihi amma fa abubuwa sun sauya ba kamar da ba. Ji kake kamar shekara 100 ta wuce, mun yi fama da abubuwa da abubuwa.

Andrii Rybka, mai shekara 43

Kayan wasan yara a gidan adana kayan tarihin

.

Asalin hoton, ZHENYA MOLYAR

An ɗauki wannan hoton ne a lokacin gabatar da wani sabon littafi a gidan adana kayan tarihin a Kyiv. Yayin da manya suke tattaunawa, 'ya'yana da na ƙawata sun haɗu suna wasa.

A ranar 6 ga watan Maris na ɗebi 'ya'yana a mota muka nufi kan iyakar Hungary, inda na bar motar muka ci gaba da tafiya da ƙafa.

Idan na kalli hoton nan sai na riƙa tunanin yadda yaran suke cikin walwala, da kuma yadda cikin ɗan lokaci al'amura suka sauya muka yi wannan tafiya cikin tashin hankali, ba su san inda za mu nufa ba, yayin da iyayensu mata ke kuka.

Zhenya Molyar, mai shekara 41