Alfanun shan ruwa biyar ga lafiyar jiki

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Mene ne ruwa?

Ruwa wani abu ne tsururu mara launi da ke dauke da sinadaran hydrogen da oxygen.

Ruwa dai yana da muhimmanci ga rayuwar mutane. Shan ruwa mai yawa ko kuma zama ba tare da kishirwa ba, abu ne da yake nuna cikakkiyar lafiyar mutum.

Jikin dan adam zai iya kasancewa ba tare da abinci ba har na tsawon makonni, amma hakan ba zai yiwu idan babu ruwa.

Hakan ya kara tabbata ne ganin cewa jikin ɗan adam na ɗauke da kashi 60 na ruwa, inda rashin ruwan kan shafi yanayin lafiyar jiki da kuma ta kwakwalwa.

Amfanin shan ruwa wajen gina jiki

Amfanin shan ruwa don gina jiki ga lafiyar mutane ya ta'allaka ne daga wajen da aka samo ruwan, kama daga koguna ko kuma na lemu, wadanda galibi ake samu daga ma'adinai na ƙarkashin ƙasa da sauransu.

Irin wannan na'u'i na ruwa kan samar da sinadaran calcium da kuma magnesium.

Amfanin shan ruwa biyar ga lafiyar jiki

1. Zai inganta yanayi da kuma lafiyar kwakwalwa

Bincike ya nuna cewa kasancewa cikin kishirwa kan janyo rashin kyawun yanayi da kuma tunani ga kowa kama daga yara har zuwa manya.

Shan isasshen ruwa na inganta lafiyar kwakwalwa da kuma jiki, inda binciken ya kuma nuna cewa rashin shan ruwa kan shafi yanayin tunanin mutum.

Har ila yau, rashin shan ruwa na janyo ƙaruwar barazanar kamuwa da ciwon kai da sauran su ga mutane.

2. Zai taimaka wajen rage kiba

Kwakwalwar dan adam ba ta iya bambance tsakanin yunwa da kishirwa, inda a yawan lokuta ake kasa bambance hakan; a duk lokacin da ka ji kana bukatar shan wani abu kamar cakuleti, to ka fara da shan kofin ruwa.

Shan ruwa na kuma taimakawa wajen kula da nauyin jiki. Bincike ya nuna cewa shan ruwa kafin cin abinci, zai iya cika wa mutum ciki, inda hakan ke taimaka wa wajen rage kiba.

An kuma lura da hakan ne a wani bincike a 2015, inda ake sauya cin abinci da shan ruwa. Sakamakon ya nuna cewa hakan zai rage kiba da kuma ƙara inganta lafiyar jiki.

3. Zai inganta motsa jiki

Bincike da aka gudanar kan amfanin shan ruwa da kuma rashin sha a kan 'yan wasa, ya nuna cewa rashin shan ruwa kan shafi yanayin kwazo na 'yan wasa, har ma da ta rayuwarsu.

4. Zai taimaka wajen yin bayan gida

Ruwa na taimakawa wajen yadda abubuwa suke a cikin jiki, inda shan ruwa zai iya taimakawa domin kauce wa rashin yin bayan gida ga yara da matasa da kuma tsoffi. Akwai alfanu kuma na shan ingantaccen ruwa.

5. Zai taimaka wajen yin fitsari

Rashin shan ruwa, zai iya ƙara barazanar kamuwa da ciwon koda ga wasu mutane.

Bincike ya kuma nuna cewa shan isasshen ruwa, kan iya rage barazanar kamuwa da cutukan mara da kuma zafi yayin fitsari ga mata.