Ƙasashen Yamma sun zargi Rasha da yi wa EU da Nato kutsen intanet

Kutsen intanet

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu kamfanoni da dama a Turai sun bayar da rahoton yi musu kutse a shafukansu
Lokacin karatu: Minti 2

Hukumomin leƙen asirin Birtaniya da Amurka da wasu ƙasashen Yamma sun yi gargaɗin cewa hukumar leƙen asirin Rasha ce ke da hannu a jerin kutsen intanet da ake yi wa ƙasashen ƙungiyar tsaro ta Nato da kuma ƙasashen Tarayyar Turai.

Sun ce hukumar leƙen asirin Rasha ta kai wa ƙasashen hare-hare ta intanet.

A shekarar 2018 ce dai aka zargi hukumar leƙen asirin Rashar da sanya wa tsohon jami'in leƙen asirin ƙasar - wanda kuma ya taɓa yi wa Birtaniya aiki -tare da 'yarsa guba a birnin Salisbury na Birtaniya.

Ƙasashen Yamman sun ce hare-haren intanet da Rashar ke kai musu, sun haɗa da yi wa shafukansu na intaten leƙen asiri da maƙarƙashiya da lalata wasu bayanan shafukan da kuma wallafa bayanan da aka jirkita.

Gargaɗin nasu na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara samun fargabar kutsen da leƙen asirin Rasha a ƙasashen Turai, tun bayan fara yaƙin Ukraine shekara biyu da suka gabata.

Ƙasashen da suka fitar da gargaɗin sun haɗa da Birtaniya da Amurka da Jamus da Australia da Ukraine da Canada da Jamhuriyar Czech da Latvia da Estonia da kuma Netherlands.

Ƙasashen sun kuma ce tun 2020, hukumar leƙen asirin Rashar - wadda suka zarga da hannu a yunƙurin juyin mulki da maƙarƙashiya da kuma yunƙurin kisan kai - na ƙoƙarin mayar da ayyukanta zuwa kutsen intanet.

Kamfanonin da suka shafi ayyukan kuɗi da zirga-zirga da makamashi da fannin lafiya, suka bayar da rahoton yi musu kutse a ƙasashe mambobin ƙungiyar Nato da Tarayyar Turai da Amurka da kuma ƙasashen yankin Asiya.

An dai yi amanna cewa manufar hukumar shi ne kawo cikas ga kai kayan agaji zuwa Ukraine.

Ƙasashen Yamman, sun kuma yi gargaɗin cewa hukumar leƙen asirin Rashar ce ke da hannu kan jerin hare-hare intanet da aka kai wa Ukraine a 2022.

A watan Mayun da ya gabata, Jamus ta zargi Rasha da ƙaddamar da jerin hare-haren intanet kan hukumar tsaro da kamfanonin jiragen samanta da kuma dimokraɗiyyarta.