Rawar da ƴanwasan Afirka suka taka a gasar Premier League

Lokacin karatu: Minti 6

An kammala gasar Premier League ta Ingila ta 2024-25, inda Mohamed Salah ya taka rawar gani a bajintar da Liverpool ta yi ta lashe kofin gasar.

Shi aka ayyana ɗanwasan gasar mafi hazaƙa saboda ƙwallaye 47 da zira a raga da kuma taimakawa wajen cin 18, adadin da ya sa ya kamo bajintar da Alan Shearer ya yi a shekarun 1990 da kuma Andy Cole.

Ɗan ƙwallon Kamaru Bryan Mbeumo ma ya yi ƙoƙari sosai, inda ya ci ƙwallo 20 da bayar da bakwai a ci - mafi yawa a sana'arsa - kuma ana sa ran zai koma Manchester United.

Ko su wane ne sauran 'yan Afirkan da suka taka rawar gani a Premier da aka kammala? BBC Sport Africa ta yi nazari kan hakan.

'Yanwasan gaba - Salah da Mbeumo

A 'yanwasan gaba, magana ce Mohamed Salah.

Ɗanwasan mai shekara 32 ne kan gaba a jerin mafiya saurin cin ƙwallo mai maki 25.4. Ya buga jimillar shot 130, masu haɗari a cikinsu 61, sannan ya taɓa ƙwallo a da'irar yadi na 18 ta abokan hamayya sau 394.

Damarmaki 89 da ya ƙirƙira wa abokan wasansa na cikin mafiya a gasar, yayin da Mbeumo ya zo na biyar da damarmaki 70 da ya ƙirƙira.

Ƙwallaye 20 da Mbeumo ɗin ya ci kuma sun zarta waɗanda aka sa ran zai ci na 12.3.

Ya haɗa kai da Yoane Wissa na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo wanda ya ci ƙwallo 19 shi ma, abin da ya sa zama na biyu mafi kokari cikin 'yanwasan Afirka na Premier League.

Antoine Semenyo ma ya taka rawar gani saboda ƙwallo biyun da ya ci a wasan ƙarshe sun sa ya ci wa ƙungiyarsa Bournemouth ƙwallo 11 kenan a karon farko.

Iwobi ya fi kowa ƙoƙari a Fulham

Ɗanwasan Najeriya Alex Iwobi ya fi abokan wasansa ƙoƙari a Fulham da ƙwallayensa tara da ya ci da kuma taimakawa wajen cin shida.

Ya ɗan ɗara Amad Diallo na man United (wanda ya ci takwas kuma ya bayar aka ci shida). Amma Iwobi ya fi shi buga wasanni.

Iwobi ne dai kan gaba wajen ƙirƙirar damarmaki (59) da kuma bayar da cikakken fasin (508) a cikin ɓangaren abokan hamayya, inda shi kuma Thomas Partey na Ghana ya fi yawan tura cikakkun fasin (1,631).

Shi kuwa Idrissa Gana Gueye ya nuna bajintarsa ne wajen taimka wa Everton samun damar ci gaba da zama a gasar.

Ɗan Senegal din mai shekara 35 ya cim ma mafi girman bajintar dakatar da abokan hamayya sau 133 kuma ya ɗauke ƙwallo daga abokin hamayya sau 221, inda ya zarta kowane ɗan ƙwallo daga nahiyar Afrka.

Bassey ya kankane daga baya

'Yanwasan baya uku ne suka yi zarra.

Aaron Wan-Bissaka, shi ne ya fi kowa tare ƙwallo (66) kuma ya fi yawan yin yanka (64) a 'yanwasan bayan Premier League - hakan ya sa magoya bayan West Ham suka zaɓe shi gwarzonsu a bana.

Ɗan Ajeriya Rayan Ait-Nouri ya nuna bajintar kai hari duk da matsayinsa na ɗanwasan baya ta gefe, inda ya ci wa ƙungiyarsa ta Wolves ƙwallo huɗu kuma ya bayar aka ci bakwai.

Ola Aina ya taka rawa mafi kyau a tarihi sana'arsa a Nothingham Fores, inda ya dinga ƙwalo daga ƙafar abokan hamayya sau 190 - mafi yawa kenan da wani ɗanwasan baya ya taɓa yi.

Ɗan Najeriyar mai buga baya a ɓangaren dama ya cire ƙwallo daga kan layin shiga raga sau uku, wanda 'yanwasa shida ne kawai suka iya yin irin wannan bajintar cikinsu kuma har da Iliman Ndiaye na Senegal.

Calvin Bassey na Najeriya ya taɓa ƙwallo sau 2,536 a Fulham - fiye da kowane ɗanƙwallon Afirka kenan a gasar - da cikakken fasin 1,926 da ya bayar, da tsige ƙwallo sau 113, da hana ƙwallo wucewa sau 17.

A gefe guda kuma, Noussair Mazraoui ya tare abokan hamayya sau 115 da kuma ɗauke kwallo sau 216 daga abokin hamayya a man United.

Matsalar da Onana ya samu

Andre Onana, mai tsaron raga ɗan Afirka tilo a Premier League, ya fuskanci ƙalubale mai girma a kakar bana yayin da Man United ta shiga tasku mafi muni cikin shekara 50.

Golan na Kamaru ya buga wasa tara ba tare da an zira masa ƙwallo a raga ba, amma kuma an ci shi kwallo 44 cikin wasa 25.

Hana kwallo shiga raga sau 90 da ya yi shi ne karo na 12 kuma mafiya yawa, inda adadin ya zama kashi 66 cikin 100 kuma na 15 kenan a tsakanin gololin da suka buga wasa 10 ko fiye da haka.

Ɗanwasan mai shekara 29 ya yi kuskure uku da suka jawo zira masa ƙwallo a raga - 'yanwasa uku ne kawai suka yi fiye da hakan.

Tarihi maras amfani

Ɗanwasan da ya fi kowa yin ƙeta a kakar Premier ta 2024-25 shi ne Semenyo na Bournemouth, wanda aka busa wa laifi sau 73. Adadin ya zarta na kowane ɗan Afirka.

Samy Morsy na Ipswich Town da ƙasar Masar, shi ne ya fi kowanne ɗan Afirka samun katin gargaɗi (10), sai Gueye da Semenyo da ke da 9 kowanne.

An ƙwace kwallo daga ƙafar Mohammed Kudus na Ghana da West Ham sau 93, sannan ya buga kwallon da ta daki turke sau shida. Salah da Jackson da Palmer ne kawai suka zarta shi.

Ɗanwasan gaban Chelsea da Senegal Jackson ya yi satar gida fiye da kowa har sau 23. Chris Wood, da Dominic Calvert-Lewin, da Jamie Vardy ne kaɗai suka ɗara shi.

Taiwo Awoniyi ya fi kowanne ɗanƙwallon Afirka shiga wasa daga baya a Forest, inda Jack Taylor na Ipswich ne kawai ya ɗara shi zama a bencin.

Wasa 23 cikin 26 da ɗan Najeriyar ya buga ya shiga ne bayan fara wasa.

An samo alƙaluman ne daga shafin opta da kuma Premier League