'Manchester Utd ko Barca' - ina Osimhen zai nufa?

    • Marubuci, Rob Stevens
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Kocin Najeriya Eric Chelle na tunanin cewa manyan ƙungiyoyin Turai za su yi rububin Victor Osimhen bayan da ɗan wasan ya taimaka wa Galatasary lashe kofin ƙungiyoyin Turkiyya.

Ana sa ran ɗan wasan mai shekara 26 a duniya zai koma ƙungiyarsa Napoli bayan cin ƙwallo 37 a wasa 41 da ya buga tsawon kaka ɗaya da ya tafi aro a ƙungiyar da ke birnin Istanbul.

Har yanzu yana da sauran shekara ɗaya a kwantaraginsa da Napoli, amma ana sa ran zai bar ƙungiyar saboda rashin jituwar da ke tsakanin sa da koci Antonio Conte.

Kasancewar har yanzu bai san makomarsa ba, Osimhen ba ya cikin ƴan wasan da aka zaɓa domin buga wasan sada zumunta tsakanin Najeriya da Rasha a ranar Juma'a.

"A ganina, Victor ne ɗan wasan gaba mafi kyau a duniya," kamar yadda Chelle ya shaida wa sashen wasanni na BBC.

"Abu ne mai wahala ya buga wannan wasa kasancewar ya kwashe kakar da ta gabata yana wasa cikin matsi.

"Yanzu an buɗe kasuwar musayar ƴan wasa. A irin wannan lokaci ba zai iya natsuwa domin buga wasa ba ɗari bisa ɗari.

"Dole ne in ba shi kariya ta kowane ɓangare, domin ƙila zai tafi [sauya ƙungiya].

"Ƙila ƙunyoyi kamar Manchester United ko Chelsea ko Barcelona ko Real Madrid. Saboda haka ya kamata ya tsayar da hankalinsa wuri guda."

Osimhen na son cin ƙwallo 'ko da yana bacci'

Osimhen, wanda ke cikin tawagar Najeriya da ta lashe kofin duniya na ƴan ƙasa da shekara 17 a shekarar 2015, shi ne na biyu a jerin waɗanda suka fi ci wa Najeriya kwallo, inda yake da ƙwallo 26.

Shi ne ya jagoranci ƴan wasan gaba na tawagar Super Eagles a gasar cin kofin Afirka na 2023, inda Najeriyar ta zo ta biyu kuma yana taka muhimmiyar rawa a farfaɗowar da ƙungiyar ta yi a yunƙurinta na samun gurbin buga gasar cin kofin duniya na 2026.

Najeriya ta samu maki uku ne kacal daga wasanni huɗu da ta buga na farko a lokacin da Osimhen ke fama da rauni, amma lokacin da ya dawo wasa a watan Maris ya samu nasarar zuwa ƙwallo uku a lokacin da Super Eagles ta lallasa Rwanda sannan ta yi canjaras da Zimbabwe.

Chelle ya ce bai "taɓa ganin zaƙaƙuri" kamar ɗan wasan ba, wanda ya taɓa buga wa ƙungiyoyin Wolfsburg da kuma Lille.

"Yana son ya yi nasara a koda yaushe. Abin ba a cewa komai," in ji Chelle.

"Ko da an kammala atisaye yana so ya tsaya ya sake zura ƙwallo a raga.

"Ina ganin yana son cin ƙwallo ko da a cikin bacci ne."

Rusha 'babbar ƙasar ƙwallon ƙafa'

Najeriya za ta je Moscow bayan lashe kofin sada zumunta na 'Unity Cup' a ranar Asabar.

Super Eagles ta lallasa abokan hamayyarta na Ghana 2-1 a ranar Laraba sannan ta doke Jamaica 5-4 a bugun fanareti bayan an kai ƙarshen lokaci ana 2-2 a wasan ƙarshe.

Har yanzu akwai haramcin shiga gasannin duniya a kan Rasha bayan mamayen da ta ƙaddamar kan Ukraine a watan Fabarairun 2022, amma duk da haka Chelle na sa ran karawar za ta yi zafi yayin da yake shirin ci gaba da karawa a wasannin neman gurbin gasar cin kofin duniya ta 2026 a watan Satumba.

Karawar da Najeriya za ta yi a gida da Rwanda da kuma ziyartar Afirka ta Kudu, na da muhimmanci sosai yayin da Najeriyar ke neman cike giɓin maki shida da ke tsakaninta da Afirka ta Kudu da ke ta ɗaya a rukunin C.

"Rasha babbar ƙasar ƙwallon ƙafa ce," in ji Chelle.

"Suna buƙatar buga wasanni da ƙasashen duniya kasancewar yaƙin ya sa abubuwa sun yi musu tsauri. Suna da ƙwararrun ƴan wasa a gasar ƙungiyoyi ta cikin gida.

"Ina ganin mutane da yawa za su zo su kalli wasan.

"Abin da ke faruwa shi ne muna shiri ne kafin Satumba, lokacin da za a sake karawa a wasannin neman gurbin gasar cin kofin duniya. Wannan ne abin da muke hari."