Napoli ta umarci Kvaratskheli ya bar ƙungiayr nan take

Lokacin karatu: Minti 1

Napoli ta umarci Khvicha Kvaratskhelia da ya bar ƙungiyar da ke kan teburin Serie A na bana nan take, in ji koci Antonio Conte.

Mai shekara 23, wanda ake akalanta shi da Paris St Germain da Liverpool da Chelsea - yana cikin ƴan wasan da suka taka rawar da ta kai Napoli ta lashe Serie A kakar 2022/23.

''An bukaci Kvaratskhelia da ya bar Napoli,'' in ji Conte.

''Na tattauna da Khvicha, wanda ya tabbatar min da yana son barin ƙungiyar nan take.

''Akwai ƙunshin yarjejeniya da ya kamata a sabunta, amma sai aka kasa cimma matsaya tsakanin ƙungiyar da ɗan wasan. Daga nan sai na janye hannu na, saboda ba zan tursasa ɗan wasan da baya son ci gaba da zama tare da mu ba.''

Kvaratskhelia - wanda yana cikin ƴan wasan tawagar Georgia da ta zai zagayen ƴan 16 a Euro 2024 - magoya bayan Napoli sun yi masa lakabi da 'Kvaradona' wato magajin Diego Mardona a kakar da ƙungiyar za ta lashe kofin Serie.

Ya je Napoli yana da shekara 21 kan £9m daga club Dinamo Batumi ta Georgia, tun daga lokacin ya zama kashin bayan ƙungiyar, wanda jimilla ya ci ƙwallo ya kuma bayar aka zura 54 a raga a wasa 107.

A kakar nan Kvaratskhelia ya ci ƙwallo biyar ya bayar da uku aka zura a raga a babbar gasar tamaula ta Italiya.

Napoli wadda ta kare a mataki na 10 a kakar 2022/23 tana ta ɗaya a kan teburin Serie A na bana da maki 44 daga karawa 19.