Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da zai hana Chelsea sayen Osimhen
Har yanzu Chelsea na yunƙurin ɗaukar ɗan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen a ranar ƙarshe, amma kuma Al-Ahli ta Saudiyya na neman yi mata fancale.
Ƙungiyar mai buga gasar Saudi Pro League ta cimma matsaya da Napoli kan Osimhen kan kuɗin da suka kai fan miliyan 60, inda ɗan ƙwallon zai dinga karɓar fan miliyan 25 zuwa 30 duk shekara a matsayin albashi.
Kazalika, an ce yarjejeniyar ta shekara huɗu ta ƙunshi saɗarar barinsa ya koma Turai da taka leda idan yana so.
Asusun gwamnatin Saudiyya da ke taimaka wa kulob huɗu fiya girma a ƙasar ya yi duk mai yiwuwa domin ganin ya kai Osimhen mai shekara 25 ƙasar.
Sai dai kuma, ya fi so ya koma Chelsea matuƙar dai za su cika masa buƙatun da ya nema.
A gefe guda kuma, biyan albashinsa ne babbar matsala ga Chelsea saboda irin sababbin 'yan wasa da ta ɗauka kafin fara kakar bana.
Wannan ta sa rahotonni ke cewa Chelsea za ta nemi ta karɓi aronsa tukunna amma da sharaɗin sayensa a 2025 ta yadda kafin lokacin ta sayar da ƙarin wasu 'yan wasa.
Ɗanjarida kuma masanin gasar Serie A ta Italiya, James Horncastle, ya ce matsalar da ta sa ƙungiyoyi ba su rububin Osimhen ita ce "yana yawan jin rauni" kuma "a kaka ɗaya kawai ya haska".
"Idan ka kalli ƙoƙarinsa, kafin ya ci ƙwallayen da ya taimaka wa Napoli ɗaukar Serie A, ƙwallo 14 kawai ya ci a kakar kuma kashi ɗaya cikin uku kawai ya buga na kakar. Idan ba za ka iya buga wasa 30 zuwa 38 ba a kaka ɗaya, sannan kuma za ka tafi buga gasar Afcon a watan Janairu lokaci-lokaci, wannan su ne abubuwan da ƙungiyoyi ke dubawa.
"Za ka iya jaddada abin da ka yi a kakar da kuka ɗauki kofi? Shi dai bai yi ba kuma ina ganin wannan ce matsalar idan ƙungiyoyi suka duba shi a wannan kakar."