Harin jirgin sama ya kashe mutane 78 a masallacin Sudan

Asalin hoton, X
- Marubuci, Barbara Plett-Usher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa correspondent
- Marubuci, Peter Mwai
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
- Lokacin karatu: Minti 3
Wani babban ma'aikacin lafiya ya shaidawa BBC cewa mutane fiye da 70 harin jirgin sama marar matuƙi ya kashe a wani masallaci da ke a yankin Darfur na Sudan.
Ana zargin mayaƙan RSF da kai harin na ranar Juma'a a birnin el-Fasher, amma ƙungiyar ba ta sanar ko tana da hannu a ciki ba.
Fiye da shekara biyu kenan ana fafata ƙazamin yaƙin basasa tsakanin RSF da dakarun gwamnatin ƙasar.
Ƙungiyar masu ɗauke da makaman tana ƙara samun ƙwarin gwiwa a ƙoƙarin da ta ke yi na ƙwace iko a birnin el-Fasher, wajen da dakarun gwamnati suka fi ƙarfi a Darfur kuma inda fararen hula fiye da dubu ɗari uku ke zaune cikin ɗar-ɗar saboda yaƙin da ake yi.
Wani ganau ya tabbatar wa BBC cewa an kai harin ne ana cikin sallar asuba, kuma nan take aka kashe gomman mutane.
Majiyar ma'aikatan lafiya ta ce mutane 78 suka mutu kuma wasu 20 suka samu raunuka, yayin da ake ci gaba da zaƙulo gawarwaki.
BBC Verify ya tantance ingancin bidiyon da aka yaɗa da ke nuna gawarwaki aƙalla 30 a kusa da masallacin a yammacin birnin.
A makon nan, RSF ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a El Fasher, birnin da ya kasance a ƙarƙashin ikon ta na fiye da shekara ɗaya. Rahotanni sun ce daga cikin hare-haren harda wanda aka kai a sansanin ƴan gudun hijira na Abu Shouk da ke a kusa da birnin.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sashen bincike na jami'ar Yale ya ce hotunan tauraron ɗan Adam da aka naɗa sun nuna cewa a yanzu mayaƙan RSF ne ke da iko a sansanin ƴan gudun hijiran.
Ya kuma bayyana cewa mayaƙan sun shiga hedikwatar rundunar haɗin gwiwa ta ƙawayen dakarun Sudan.
Bidiyon da BBC ta tabbatar da ingancinsa ya nuna yadda mayaƙan RSF ke zirga-zirga a harabar hedikwatar, sai dai babu tabbacin ko sun ƙwace iko baki ɗaya a sansanin.
Wannan yunkuri zai sa mayaƙan su ƙara kusantar filin jirgin sama na el-Fasher da kuma hedikwatar dakarun sojin Sudan ta yankin.
An yi hasashen mayaƙan za su ƙwace iko a birnin el-Fasher idan har dakarun Sudan ba su samu ƙarin ɗauki ba.
Idan hakan ta tabbata, mayaƙan RSF za su samu cikakken iko da yammacin Sudan yayin da dakarun gwamnati ke da iko a Arewa da gabashi. .
Masu sharhi a Sudan na fargabar mayaƙan za su kai farmaki kan fararen hula da ke a birnin, kasancewar mafi yawan su ƴan ƙabilun da RSF ke yi wa kallon maƙiya ne.
Ƙungiyar likitocin ƙasa da ƙasa ta zargi RSF da ƙoƙarin rushe el-Faher, wani zargi da ƙungiyar ta sha musantawa.

Asalin hoton, Getty Images/BBC











