Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mece ce makomar Kabiru Turaki bayan INEC ta jingine shugabancinsa na PDP?
A wani sabon rikici da ya sake kunno kai a jam'iyyar PDP, hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta, INEC ta ce ta jingine shugabancin Kabiru Tanimu Turaki na jam'iyyar PDP, inda ta ce ta yi hakan ne bisa amfani da shari'o'i da ke gaban kotu.
INEC ta ce ta ɗauki wannan matakin ne bayan wasiƙu da ta samu daga lauyoyin jam'iyyar PDP cewa ta gyara bayanan jam'iyyar da ke rumbun bayananta.
PDP ɗin ce ta buƙaci hukumar ta sauya sunayen shugaganninta ƙasa domin saka sababbin da aka zaɓa a babban taron jam'iyyar a jihar Oyo a watan Nuwamban da ya gabata.
To sai dai hukumar ta Inec ta ce ta yi duba da nazari kan buƙatun lauyoyin bisa dogaro da "abin da yake na gaskiya, da dokoki da kuma hukunce-hukuncen kotuna dangane da batun."
Ta ce hukunce-hukunce sun hana hukumar sa ido ko kuma amincewa da sakamakon abin da ya fito daga taron na ranar 15 ga watan Nuwamban 2025.
Tun daga lokacin ne masu sharhi kan harkokin suke yi hasashen za a iya fuskantar matsala irin wannan ganin yadda ta kaya kafin gudanar da babban taron jam'iyyar na Ibadan.
Martanin PDP
Sai dai a wani martani da tsagin Turaki na jam'iyyar ya fitar, jam'iyyar ta ce babu wani tsagi ko bambanci a jam'iyyar, inda suka sake nanata cewa Kabiru Turaki ne shugaban jam'iyyar.
A wata sanarwa da sakataren watsa labaran jam'iyyar na tsagin Turaki, Ini Ememobong ya fitar, ya ce an zaɓa shugabannin ne a babban taron jam'iyyar da aka yi a Ibadan, wanda a cewarsa ya samu sahalewar wata babbar kotun tarayya.
Ya ce an ɗaukaka ƙarar shari'ar, sannan suka nemi a dakata da yanke hukunci, "amma kwanan nan muke sa ran kotun ɗaukaka ƙara za ta saurara shari'ar sannan ta yanke hukunci."
Sanarwar ta ce INEC ta halarci zaɓen fitar da ƴan takarar na PDP a Ekiti da Osun, "waɗanda kuma tsagin Turaki ne suka shirya. Duk da mun san matsin lambar da hukumar ke fuskanta, muna tunatar da ita cewa sauke alhakin ƴan Najeriya ne babban aikinta na karewa da tabbatar da dimokuraɗiyya."
Sanarwar ta ƙara da cewa Kabiru Turaki ya samu goyon bayan kwamitin amintattu da na gwamnoni da ƴan majalisa da tsofaffin gwamnoni da sauran ɓangarorin jam'iyyar.
"Kuma ya kamata INEC ta tuna cewa dimokuraɗiyya da jama'a ake tunƙaho, don haka ɓangaren Wike da abokansa ba su kai a kira su da tsagin PDP ba."
Haka kuma sakataren watsa labaran ya zargi INEC ta nuna ɓangarenci, sannan ya yi kira ga ƴan Najeriya da su kwantar da hankalinsu.
"Sannan muna buƙatar goyon baya a ƙoƙarin da muke yi wajen sake dawo da martabar jam'iyyarmu domin samun nasara a zaɓukan da suke tafe."
Makomar Turaki da PDP
Domin jin ko me hakan ke nufi, BBC ta tuntuɓi Dokta Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano, inda ya ce wannan sabuwar matsalar ba ta zo a mamaki ba.
Masanin harkokin siyasar ya ce akwai tunanin hakan zai faru ganin abubuwan da suka faru baya, musamman gabanin babban taron babbar jam'iyyar hamayyar da aka yi a Ibadan.
Sai dai idan na so a samu sauƙin lamarin, akwai wasu zaɓi da yake tunanin sun rage wa Kabiru Turaki:
- Komawa kotu: Sufi ya ce kasancewar Kabiru Turaki masanin shari'a ne, ya san abin da ya fi dacewa. "Zai ii kyau su koma kotu domin neman wani umarnin kotun ko shari'a."
- Neman sulhu: Ɗaya zaɓin da masanin harkokin siyasar ya bayyana shi ne ɓangaren Kabiru Tanimu Turakin ya nemi sulhu da ɗaya ɓangaren da suke takun-saƙa. "Ka ga idan aka neme su, aka tattauna suka amince suka janye ƙara, shi ke nan magana za ta iya mutuwa.
Sai dai masanin shari'ar ya bayyana cewa akwai aiki a ja gaban cigaban dimokuraɗiyya a Najeriya, inda ya bayyana cewa akwai buƙatar kotunan ƙasar su daina sauraron ƙara iri ɗaya a lokaci ɗaya matuƙar ana so siyasar ƙasar ta inganta.
Rawar jam'iyya mai mulki
A duk lokacin da rikici ya turnuƙe wata jam'iyyar hamayya a Najeriya, ƴan ƙasar sukan nuna wa babbar jam'iyyar ƙasar mai mulki yatsa, inda ake yawan zarginta da hannun a rikice-rikicen da ke faruwa, zargin da ta daɗe tana musantawa.
Sai dai Kabiru Sufi ya ce duk da cewa babu hujja a fayyace kan irin rawar da APC take takawa a rikicin da PDP ke ciki, ya ce biri ya yi kama mutum.
A cewar masanin siyasar, "zai yi wahalar gaske ka iya cire hannun babbar jam'iyyar saboda rikice-rikicen na zuwa ne a daidai lokacin da ita kuma take ƙara samun tagomashi. Amma bincike mai zurfi tare da samun hujjoji masu ƙarfi ne za su iya tabbatar da hakan."
An daɗe dai ana zargin APC ta taka rawa wajen hana PDP da sauran jam'iyyun hamayya rawar gaban hantsi, musamman tun bayan da Wike ya amince da zama minista a gwamnatin na APC, duk da cewa ya musanta tare da cewa shi ɗan PDP ne na gaskiya.
Rikicin PDP
Jam'iyyar PDP ta daɗe tana fama da rikice-rikice, musamman tun bayan zaɓen fitar da ƴan takara da Atiku ya doke Wike, lamarin da ya sa Wike da wasu gwamnoni suka ware, suka yi tallata Atiku a babban zaɓen.
Amma wannan rikicin ya samo asali daga babban taron jam'iyyar da aka yi a watan Nuwamba, inda babbar jam'iyyar ta zaɓi Kabiru Tanimu Turaki a matsayin sabon shugabanta, duk da irin jimirɗar da aka yi fama da ita gabanin zaɓen.
An samu umarnin kotu har guda uku da suka nemi jam'iyyar ka da ta gudanar da taron nata na ranar 15 ga watan Nuwamba a jihar Oyo.
Sai dai kuma wata kotun a jihar Oyu ta yanke nata hukuncin daban, inda ta ba kwamitin shirya babban taron umarnin ya gudanar da taronsa, lamarin da tsagin Wike ya ƙi amincewa da shi.