Yadda yaƙi da Isra'ila zai taɓa ƙimar jagororin Iran

Asalin hoton, Pacific Press via Getty
- Marubuci, Kasra Naji
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Special Correspondent, BBC Persian
- Lokacin karatu: Minti 6
Bayan shafe kusan mako biyu a wani gidan ɓuya a Iran saboda yaƙin da ƙasarsa ta yi da Isra'ila, shugaban addini Ayatollah Ali Khamenei ya fito a karon farko ya yi wa al'ummar ƙasar jawabi.
Sai dai duk da tsagaita wutar, tabbas za a ba shi shawarar ya yi taka-tsantsan. Duk da an ruwaito cewa Shugaba Trump ya gargaɗi Isra'ila kada ta kashe shi, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu bai kawar da yiwuwar hakan ba.
A yanzu ya taya al'ummar ƙasar murna tare da ikirarin cewa "Iran ta bai wa Amurka kunya a idon duniya", lamarin da ake ganin zai ba shi damar farfaɗo da farin jininsa.
Rashin jituwa daga sama
A lokacin yaƙin, Isra'ila ta karɓe iko da sararin samaniyar Iran cikin gaggawa inda ta dinga kai wa sansanonin soji hare-hare. Ta kashe manyan kwamandojinta.
Har yanzu babu tabbas game da irin ɓarnar da aka yi wa rundunar sojin ta Iran, amma irin ruwan wutar da aka yi wa sansanoninsu tabbas ta rage musu ƙarfi bayan kashe kuɗaɗe masu yawa a fannin soji.
Yanzu tashoshin nukiliyar ƙasar da aka sani - waɗanda suka jawo mata takunkumai daga manyan ƙasashen duniya - Amurka ta lalata su a harin da ta kai musu, wanda zai jawo koma-baya, kodayake dai babu tabbas game da ɓarnar da aka yi a wuraren.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu 'yan Iran za su zargi Khamenei da alhakin jawo ɓarnar da Isra'ila da Amurka suka aikata, wanda ya fara zama shugaba a shekarar 1989.
Za su zarge shi da nacewa kan ganin bayan Isra'ila, abin da wasu da yawa a ƙasar ba su goyon baya.
Ga kuma burinsa na samun makaman nukiliya, abin da ya sa ƙasar mai arzikin man fetur ta koma talaka.
"Abu ne mai wuya a iya hasashen lokacin da gwamnatin Iran za ta faɗi a irin wannan yanayin, amma dai da alama an kama hanya," a cewar Farfesa Lina Khatib, wata malama a Jami'ar Harvard.

Asalin hoton, Getty Images
An ɗan samu bambancin fahimta a ɓangaren shugabancin ƙasar. A daidai lokacin da aka tafka yaƙin, wani kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya ruwaito cewa wasu tsofaffin jami'an gwamnati sun nemi wasu shugabannin addini a birnin Qom - daban da Khamenei - da su saka baki domi sauya shugabancin.
"Akwai ranar hisabi," in ji Farfesa Ali Ansari, shugaban cibiyar nazarin harkokin Iran ta Institute of Iranian Studies da ke Jami'ar St Andrews.
"A bayyane take cewa akwai rashin jituwa mai yawa a tsakanin shugabannin, da kuma ɓacin rai zukatan 'yan ƙasa."
'Fushi da ɓacin rai'
Cikin mako biyu da suka wuce, Iraniyawa da yawa sun yi ta fama da tunanin kare ƙasarsu.
Mazauna garuruwan da ke wajen birane sun bai wa waɗanda suka gudu mafaka, masu shaguna sun rage farashin kayayyaki, maƙwabta suka dinga duba maƙwabtansu domin jin ko suna buƙatar wani abu.
Amma da yawa suna sane da cewa burin Isra'ila shi ne kifar da gwamnatin Iran. Da ma wasu da yawa na neman sauyin a Iran, amma ba lallai su bi tsarin wata ƙasar waje ba wajen cimma burinsu.

Asalin hoton, Getty Images
A mulkinsa na kusan shekara 40, Ayatollah Khamenei - ɗaya daga cikin waɗanda suka fi daɗewa a mulki a duniya - ya murƙushe duk wasu 'yan'adawa.
Ko dai an kulle su a gidan yari ko kuma sun fice daga ƙasar.
Da a ce yaƙin ya ci gaba, wasu na ganin ko da gwamnatin ta fadi ba lallai 'yan'adawa su kafa tasu ba illa kawai ƙasar za ta faɗa cikin ruɗani da rashin doka.
"Abu ne mai wuya 'yan'adawa su iya kifar da gwamnatin. Har yanzu gwamnatin na da ƙarfi a cikin gida kuma za ta ƙara nuna ƙarfi wajen murƙushe 'yan'adawa," a cewar Farfesa Khatib.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu 'yan Iran na fargabar sabon salon matsawa daga gwamnati.
Aƙalla mutum shida aka aiwatar wa hukuncin kisa tun bayan fara yaƙi da Isra'ila saboda zargin su da taya Isra'ila leƙen asiri. Hukumomi sun ce sun kama mutum 700 kan wannan zargi.
Wata mace ta faɗa wa sashen BBC Parsian cewa abin da ta fi tsoro sama da yaƙin shi ne matakin da gwamnatin za ta ɗauka bayan wulaƙanta ta da aka yi a yaƙin.
"Idan gwamnatin ta gaza samar da ababen more rayuwa, to tabbas ɓacin rai da fushi zai yi yawa," a cewar Farfesa Ansari.
"Ina ganin zai faru ne mataki bayan mataki. Ba na jin abu ne zai faru nan kusa har sai bayan gama yaƙin da lokaci mai tsawo."
Ma'ajiyar makaman Iran masu linzami
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka tsira daga hare-hare Isra'la shi ne rumbunan ajiyar makamai masu linzami na Iran da ta kasa ganowa saboda yadda ta baza su a lungu da saƙo na ƙasar kuma a ƙarƙashin duwatsu.
Babban kwamandan rundunar sojin Isra'ila Eyal Zamir ya ce sun ƙaddamar da hare-haren ne da sanin cewa "Iran ta mallaki makamai masu linzami kusan 2,500".
Waɗannan makamai da Iran ta harba sun haddasa mace-mace da ɓarna a Isra'ila.
Yanzu Isra'ila tana nan tana fargaba kan makaman roka 1,500 da ake tunanin sun rage a hannun Iran.
Haka nan, akwai babbar fargaba a Amurka da Isra'ila da ƙasashen Yamma cewa yanzu Iran za ta iya yin sauri ta ƙera makamin nukiliya, abin da ta sha musanta cewa tana yunƙurin yi.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kodayake akwai yiwuwar an haddasa koma-baya a shrin Iran na nukiliya, ta ce ta kwashe makamashin da ta riga ta inganta na Uranium zuwa wani wuri daban kafin harin Amurka.
Wannan makamashin na Uranium da ta inganta kashi 60 cikin 100, idan ya kai kashi 90 - wanda abu ne mai sauƙi - ya isa ta haɗa makamin nukiliya ƙwara 9 da shi, kamar yadda ke bayyanawa.
Jim kaɗan kafin fara yaƙin Iran ta sanar cewa ta gina wata sabuwar masana'anta a ɓoye da take sa ran fara aikin inganta Uranium ɗin nan gaba kaɗan.
Majalisar wakilan ƙasar ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da yanke hulɗa da hukumar kula da makamin nukiliya ta duniya IAEA.
Amma duk da haka sai gwamnatin ƙasar ta amince, wanda idan ta tabbata to Iran ɗin za ta fice daga yarjejeniyar non-Proliferation Treaty (NPT) yayin da masu kakkausan ra'ayi ke son ta fice domin samun damar ƙera makamin.
Yanzu Ayatollah Khamenei zai iya samun ƙwarin gwiwa cewa gwamnatinsa ta tsira.
Amma saboda ya shekara 86 kuma ba shi da lafiya, jaridar New York Times ta ruwaito cewa ya zaɓi magada a rundunar sojin ƙasar ko da za a sake wasu daga cikin kwamandoji.












