Ƴan Najeriya na bambami kan buƙatar wasu na son a soke shari'ar Musulunci a Arewa

Musulmi na sallah

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

A Najeriya, martani na ci gaba da fitowa daga mutane daidaiku da kungiyoyin addini da na farar hula daga sassan arewacin kasar, bayan wani zama da 'yan majalisar dokokin Amurka suka yi, inda wasu ƴan Najeriya suka yi kira ga 'yan majalisar da su yi matsin lamba ga Najeriya ta soke shari'ar Musulunci da hukumomin Hisbah a arewacin kasar.

Kwararrun sun yi kashedi cewa wadannan tsare-tsare na shari'ar Musulunci da hukumomin Hisbah ana zargin suna bayar da gudunmawa wajen zaluntar Kiristoci a yankin na arewacin Najeriya.

Martanin farko dai a kan kiran da 'yan majalisar dokokin Amurka suka yi, cewa a shiga matsin lamba ga hukumomin Najeriya, don su soke shari'ar Musulunci da hukumomin Hisbah a jihohin arewacin kasar, ya fito ne daga majalisar koli ta tabbatar da shari'ar Musulunci a Najeriya (SCSN).

Majalisar ta yi Allah-wadai da kiran, kamar yadda babban sakatarenta, Nafi'u Baba- Ahmed ya bayyana a tattaunawarsa da BBC:

''Na farko dai shari'a ita ce ruhin Musulmi saboda haka a ce wai wata kasa ko wasu mutane suna yekuwar cewa a kauda shari'a wannan mafarki suke yi,'' in ji shi.

Ya kara da cewa : ''Duk wanda ya ce zai kauda shari'a a Najeriya to ya sani cewa duk Musulmi na gari sai inda karfinsa ya kare, rayuwarmu ce shari'a.''

Dakta Nafi'u ya kuma ce, ''maganar shari'ar 'yansiyasa da shari'ar ba 'yansiyasa ba duk yaudara ce da makiya Musulmi da Musulunci da shari'a suke kawowa.''

''Wanda abin da ya kawo siyasa a ciki, idan da da gaske suke yi da an tsaya an karfafa ta.

''To amma ta yi rauni amma duk da haka muna fatan in sha Allah nan gaba shuwagabannin da za su zo duk wani dansiyasa da zai zo ba zai yi kokarin ya dabbaka ko ya karfafa shari'ar Musulunci ba, ba mu ba shi.

''Ballantana wata kasa ta zo tana mana wai kurin cewa wai sai a kauda shari'a - a kauda shari'a to suna so su maida mu jiha ta 51 ta Amurka ba su isa ba.''

Dangane da bukatar rushe hukumomin Hisbah a arewacin Najeriyar kuwa, sai Nafi'u Baba Ahmad ya ce ai in aka taba Hisbah, shari'ar Musulunci aka taba:

''Saboda haka mu wannan waje ne da ba mashiga ma. Yanzu in dai ta kai ga haka to si a yi rafaranda kenan. Amma za mu fara rafaranda da wannan gwamnatin wadda take neman ta kawo mana wadannan fituntunun za mu yi rafaranda da ita a 2027 in sha Allah.''

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ita ma gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya ta CNG, ta mayar da martani ta bakin shuganta, Kwamared Jamilu Aliyu Charanchi:

''Yau duk abin da ke faruwa a Najeriya gabadaya mene ne ya dauke shi ya alakanta shi da maganar shari'ar Musulunci?''

''Kuma wane ne shari'ar nan ta je ta iske shi ta tsokane shi ko kuma ta taba shi ta yanke masa hukuncin da ba daidai da shi ba ne?''

''Shari'ar nan da Musulmi take. Ko an taba ganin wani mutum wanda ba Musulmi ba wanda aka je aka kamo shi aka kai shi kotun shari'ar Musulunci, shari'ar kuma ta hukunta shi, ko ta yi masa wani abin da ba daidai ba?''

Kwamared Aliyu ya kara da cewa: '' Saboda albarkatun da Allah (SWT) Ya yi mana a Najeriya Amerika ta sa mana ido da kuma wasu batagari da ke akwai a Najeriya wadanda suke da kiyayya da ita kanta kasar da kuma wasu al'umma na wannan yanki na kasar su ne kullum suke tashi suke wancan tsugune-tsugune.''

Ya kara da cewa, ''shawara ita ce ya kamata al'umma su sani cewa wannan abin da ke faruwa ana yi ne domin a muzguna wa al'ummar arewacin Najeriya.''

''In zabe ya zo dole mutumin Arewa ya tashi ya zabi mutumin da zai kare mutuncinshi da kimarshi da darajarshi,'' ya ce.

Tun fiye da shekara ashirin ne dai jihohi da dama na yankin arewacin Najeriya, suka kafa shari'ar Musulunci, da nufin kyautata doka, da kuma magance kalubalan tarbiyya da zamantakewar al'umma a yankin.