Yadda Amurka ke korar Kiristocin Iran duk da iƙirarin kare na Najeriya

Mai wa'azin Kiristanci Ara Torosian ya ce Kiristocin Iran na fargabar abin da zai faru da su idan aka mayar da su gida

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mai wa'azin Kiristanci Ara Torosian ya ce Kiristocin Iran na fargabar abin da zai faru da su idan aka mayar da su gida
    • Marubuci, Leyla Khodabakhshi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wata ranar Litinin a tsakiyar watan Oktoba, shekara ɗaya bayan tsare shi, jami'an tsaron shige da fice na Amurka suka dira a gidan Majid da ke Texas.

Sun faɗa masa cewa ya "tattara kayansa" - cewa za a tafi da shi - duk da cewa wani alƙali ya ba shi kariyar hana korarsa daga Amurka wata biyar da suka gabata.

Aka sanya masa ankwa a hannu da ƙugu da ƙafafuwa, kuma aka tafi da shi zuwa wani sansanin soja a Louisiana.

Majida - wanda ba shi ne sunansa na gaskiya ba - ya gudu daga Iran ne a watan Oktoban 2024 bayan yawan tsare shi da kuma azabtarwa, na farko saboda shiga zanga-zangar kisan Mahsa Amini, da kuma fita daga Musulunci zuwa Kiristanci.

Jami'ai sun saka shi cikin jirgi zuwa birnin Managua na ƙasar Nicaragua tare da wasu mutum 149, inda shi kaɗai ne ba ɗan Latin Amurka ba a cikinsu. Isarsa ke da wuya aka ƙara saka masa ankwa, aka hana shi damar neman mafaka, aka saka shi cikin tsarin da zai kai shi Venezuela da Turkiyya har zuwa ƙasarsa Iran.

Daga baya ya yi nasarar samun gidan ɓuya a Istanbul saboda tsoron abin da zai faru da shi a Iran.

Yana ɗaya daga cikin 'yan Iran da suka yi ridda zuwa Kiristanci kuma suka yi magana da BBC - akasarinsu a ɓoye saboda fargaba. Da yawansu ba a ba su mafaka ba a shekarar da ta gabata.

Lamarinsu ya ƙara fito da matsalar baki biyu a tsarin ƙasashen waje na Amurka yayin da Shugaba Donald Trump ke yawan bayyana takaici kan kisan Kiristoci a ƙasashen waje, har ma ya yi barazanar tura dakaru Najeriya "idan gwamnatin ƙasar ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci".

Wani jami'in fadar White House ya faɗa wa BBC cewa duka waɗanda aka kora daga ƙasar sai da aka nazarci takardunsu a gaban kotu kafin a fitar da su.

Jiragen korar mutane

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yayin da Amurka ke ci gaba da korar 'yan cirani marasa cikakkun takardu, ta yi gagarumin sauyi a tsarinta kan 'yan Iran da ke neman mafaka.

A watan Satumba aka ɗauki wani jirgi cike da 'yan Iran aka mayar da su ƙasar su ta hanyar Qatar, karo na farko tsawon shekaru saboda rashin alaƙar difilomasiyya tsakanin Iran da Amurka. Hakan ya nuna cewa a wannan karon an samu haɗin gwiwa tsakaninsu.

An ce gomman 'yan Iran ne a cikin jirgin ɗaure da sarƙa. Wani mai suna Sina ya bayar da labari yadda masu gadi ke tasa ƙeyarsu zuwa Tehran daga Qatar, kuma bayan sun sauka aka fara yi musu tambayoyi game da zamansu a Amurka.

Cikin fasinjojin akwai matar Ali, wani Kirista da ya bar Musulunci kuma yake zaune a Amurka a yanzu. Jami'an leƙen asiri na Iran sun tuntuɓe ta kuma suka gayyace ta.

"Sun mayar da matata Iran duk da cewa Kirista ce," in ji Ali, wanda muka sauya wa suna saboda mu kare shi da matarsa. "Yanzu jami'an leƙen asiri na Iran na nemanmu ni da ita."

Lauya Ali Herischi da ke kare Ali da matarsa da wasu da aka kora daga Amurka a cikin jirgin na watan Satumba, sun ce ba a cire muhimman bayanai ba daga takardunsu kafin a mayar da su Iran, kamar addininsu, da aƙidar siyasa, da dalilan da suka sa suka nemi mafaka.

Me ya sa komawa Iran ke da haɗari ga Kiristoci?

Masu yin ridda zuwa Kiristanci na da yawa sosai cikin Kiristocin Iran su 800,000, in ji Steve Dew-Jones na ƙungiyar Article 18 mai mazauni a Birtaniya, wadda ke bibiyar halin da Kiristci ke ciki a Iran.

Yayin da ake kaffa-kaffa da coci-cocin da gwamnati ta amince da su, mutane sun fara ƙirƙirar coci a gidajensu a faɗin ƙasar. Amma an ci gaba da muzguna wa masu ibada, a cewar Dew-Jones.

Iran na kallon ficewa daga Musulunci a matsayin ridda, inda ake kama masu yin hakan har ma a yanke musu hukuncin zama a gidan yari.

Yawan mutanen da ake tsarewa sun ninka sau shida tsakanin 2023 da 2024, kamar yadda cibiyar kare haƙƙi ta Human Rights in Iran ta bayyana.

"Tun bayan yaƙin baya-bayan nan tsakanin Isra'ila da Iran, jami'an Iran na yawan amfani da kalmar "Zionist Christianity" wato Kiristoci masu biyayya ga ƙasar Isra'ila. Ƙasar na ayyana addinin mutane a matsayin masu kawo wa tsaron ƙasa barazana," a cewar Dew-Jones.

Da yawan Iraniyawan da ke neman mafaka a ƙsashen waje kan ambaci addini a matsayin dalilin yin hakan, yayin da jami'ai a ƙasar ke zargin su da kuzuzutawa ko ma yin ƙarya sauya addini domin samun mafakar.

Sai dai ba za a iya tantance masu bayar da labarin gaskiya na guje wa azabtarwa ba da kuma masu yin ƙaryar sauya addini domin neman mafaka cikin sauƙi ba.

"Ba zai yiwu a gane gaskiyar addinin mutum ba - saboda babu hanyar shiga zuciyar mutum," in ji Dew-Jones. "Tabbas za a iya munafuntar tsarin, amma mun ga mutane da yawa da aka muzgunawa amma kotuna ba su ɗauki bayanansu da muhimmanci ba."

Rayuwar rashin tabbas

Masu neman mafaka kan samu sakamako daban-daban hatta 'yan gida ɗaya, a cewar wasu 'yan Iran da ƙwararru kan harkar shari'a.

A ƙarshen watan Yuni, jami'an ICE sun isa gidan Marjan da Reza a Los Angeles. An ga Marjan cikin wani bidiyo da fasto ɗin cocinsu ya ɗauka tana kwance a sume yayin da suka tsare mijinta.

Ma'auratan 'yan Iran da suke bar Musulunci kuma suka nemi mafaka a Amurka. makonni bayan haka, an bai wa Marjan mafaka a California, shi kuam Reza aka tsare shi a New Mexico kuma aka bayar da umarnin fitar da shi zuwa wata ƙasa.

Bayan kama su a watan Yuni, hukumar kula da tsaron cikin gida ta zarge su da kasancewa "ba bisa ƙa'ida ba da kuma ayyana su a matsayin barazana ga tsaron ƙasa" cikin wani saƙo a dandalin X.

Hoton wani bidiyo da Fasto Ara ya ɗauka na lokacin da jami'an tsaro ke kama Marjan da mijinta Reza

Asalin hoton, Submitted photo

Bayanan hoto, Hoton wani bidiyo da Fasto Ara ya ɗauka na lokacin da jami'an tsaro ke kama Marjan da mijinta Reza

Pastor Ara Torosian, wanda ya ɗauki bidiyon, ya ƙalubalanci iƙirarin jami'an tsaron cikin gida cewa ma'auratan sun shiga Amurka ba bisa ƙa'ida ba.

Ya ce sun shiga bisa doka ta hanyar wani shirin jin ƙai. "Ta yaya za a kama mijin amma a ƙyale matar?" kamar faston ya tambaya. Shi ma ya gudu daga Iran a 2010 bayan tsare shi saboda zargin safarar littafi mai tsarki na Linjila.

Majid da ya yi nasarar kuɓuta daga hannun jami'an tsaro a filin jirgi na Turkiyya, ya ci gaba da zama a ɓoye tun daga lokacin. Matarsa wadda har yanzu ba a kammala duba takardun mafakarta ba, na zaune a Los Angeles da 'yarta mai shekara ɗaya da rabi, wadda ba ta taɓa haɗuwa da mahaifinta ba har yanzu.