Me ya sa ake ce-ce-ku-ce kan shari'ar Musulunci a tsakanin Yarabawa?

Shari'a

Asalin hoton, KAGENMI/BBC Pidgin

Lokacin karatu: Minti 4

Batun shari'ar Musulunci na ci gaba da tayar da ƙura a kafafen watsa labarai da na sada zumunta tsakanin al'ummomin yankin kudu maso yammacin Najeriya da ke da jihohi shida da suka haɗa da jihar Legas da Ogun da Oyo da Ekiti da Osun da kuma Ondo.

Wani abu da ya ƙara fito da al'amarin fili shi ne martanin Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci kan batun, inda Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III ya yi gargaɗi kan ƙoƙarin daƙile wa wata al'umma ƴancinta na addini.

Kamar kowane yanki na Najeriya, Kudu maso yammacin ƙasar dai na da mabiya addinai daban-daban kuma hakan na da tasiri dangane da rayuwarsu ta yau da kullum duk da cewa al'ummar yankin na kambama fifikon al'ada kan addini.

Yadda al'amarin ya fara

Shari'a

Asalin hoton, Others

Cece-kucen dai ya fara ne sakamakon wani ƙudiri da Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci ta jihar Oyo, ta yi na kafa kwamitin shari'ar Musulunci domin yin hukunci kan batutuwan da suka shafi Musulmi bisa tanade-tanaden addinin Musulunci a garin Oyo da ke jihar.

To sai dai kuma a yanzu haka an dakatar da duk wani yunƙurin ƙaddamar da kwamitin a garin na Oyo, sakamakon yadda masu suka musamman mabiya addinin Kirista da na gargajiya suka harzuƙa dangane da batun.

Sai dai kuma batun ya ƙara fitowa fili a makon da ya gabata lokacin da gwamnatin jihar Ekiti ta karɓi baƙuncin kwamitin shari'ar Musulunci a babban masallacin birnin Ado Ekiti da ke jihar ta Ekiti domin ƙaddamarwa tare da zaman farko na kwamitin.

Kwamitin dai na da manyan alƙalan kotun shari'ar Musulunci guda uku da suka haɗa da Imam Abdullahi Abdul-Mutolib da Imam Abdulraheem Junaid-Bamigbola da Dr Ibrahim Aminullah-Ogunrinde.

Hakan ne kuma ya tayar da hankalin wasu masu raji a yankin suka fara kiraye-kirayen cewar yankin na Yarabawa ba zai amince da kowane irin kwamitin kafa shari'ar Musulunci ba.

To sai dai umarnin da Sarki Ewi na Ado Ekiti, Oba Rufus Adeyemo Adejugbe ya bayar a karshen mako na a rushe kwamitin sannan ya nemi babban limamin Ao Ekiti ya je fadarsa ya bayar da bahasi, ya ƙara janyo cece-kuce.

Ewi na Ado Ekiti ya saki kafa kwamitin na shari'ar Musulunci ne bisa dalilin cewa hakan zai sa sauran mabiya addininai su ma suka fa nasu.

"An rushe kwamitin. Idan muka ƙyale irin waɗannan kwamitoci, to Kiristoci za su kafa nasu a coci-cocinsu, haka su ma masu bin addinin gargaji, saboda haka kafin a ankara , abin zai haifar da rikici." In ji Ewi na Ado Ekiti.

Rushe kwamitin na shari'ar na Sarkin na Ado Ekiti, Oba Rufus Adeyemo Adejugbe ya yi ne ya janyo martani daga ƙungiyoyin Musulmi na yankin Yarabawa da ma Najeriya baki ɗaya.

Martanin gwamnatin jihar Ekiti

Abiodun Oyebanji

Asalin hoton, BIODUN OYEBANJI/FACEBOOK

Gwamnatin jihar Ekiti ta ce ba ta da hannu a al'amarin kafa kotunan addinin Musulunci a jihar kuma ba su da masaniya ko kaɗan dangane da kafa kwamitin shari'a mai zaman kansa da "wasu mutane suka kafa."

Wata sanarwa da kwmaishinan shari'a na jihar, Dayo Apata ya fitar ta ce "kafa majalisar shari'ar Musulunci ba ya cikin kundin dokokin jihar Ekiti."

"Tsarin dokokin jihar Ekiti walau ƙaramar kotu ko babbar kotu ko ma kotun ɗaukaka ƙara duka na sauraron al'amuran da suka shafi addini na Musulunci ko kuma na Kirista." In ji sanarwar.

Martanin Majalisar Ƙoli ta Musulunci

Sarkin Musulmi

Asalin hoton, Daular Usmaniyya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci ta Najeriya, NSCIA ƙarkashin jagorancin Sarkin Musulmi, Abubakar Sa'ad III ta yi kakkausar suka dangane da rushe kwamitin na shari'ar Musulunci a jihar Ekiti, inda ya gargaɗi gwamnonin yankin da daƙile yunƙurin Musulmin yankin na tafiyar da rayuwarsu a Musulunce.

A sanarwar da majalisar ta fitar ta bayyana rushe kwamitin na shari'a da saɓa wa kundin tsarin mulki na Najeriya.

"Majalisar Ƙli ta Addinin Musulunci ƙarƙshin Sarkin Musulmi ta damu ƙwarai kan irin rashin haƙuri da juna da rashin martaba ƴancin Musulmai musamman a yankin kudu maso yamamcin Najeriya." In ji sanarwar.

Ita ma Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci a jihar Ekiti a wata sanarwa da ta fitar mai sa-hannun shugabanta, Dr Hammed Afolabi Bakare, majalisar ta ce "za mu ci gaba da ɗabbaƙa addininmu bisa doron tsarin mulki."

"Ba a kafa kwamitin ba a matsayin kotu, an kafa shi ne a matsayin kwamitin sasanci da zai yi hukunce-hukunce dangane da al'amuran da suka shafi rayuwar Musulmi a jihar Ekiti, kuma gwamnati ce kawai take da ikon kafa kotunan shari'a." In ji sanarwar.

Sanarwar ta Majalisar ƙoli ta Addinin Musulunci ta Najeriya, NSCIA ba ta yi wa wasu mutane daɗi ba a yankin na Yarabawa irin su Aare Ona-Kakanfo na ƙasar Yarabawa, Iba Gani Adams- wanda ya ce "abin takaici ne Sarkin Musulmi ya goyi bayan wani abun da zai tayar da tarzoma a yankin da ke da kwanciyar hankali."