Su wane ne masu fafutukar kafa ƙasar Yarabawa zalla a Najeriya?

..

Tun dai bayan harin da masu fafutukar kafa ƙasar Yarabawa da ake kira Yoruba Nation suka kutsa sakatariyar gwamnatin jihar Oyo da ke Ibadan da manufar ƙwace ragamar ikon jihar, kungiyoyi da ɗaiɗaikuwa suka yi tatofa albarkacin bakinsu.

A ranar Asabar ɗin ƙarshen makon nan ne 'yan ƙungiyar da ke iƙrarin kafa ƙasar Yarabawa cike a cikin motoci da babura ɗauke da makamai sannan fuskokinsu a rufe suka shiga sakatariyar gwamnatin.

Bayan shigarsu ne kuma sai suka karkasa kansu zuwa uku inda kashin farko ya kafa ya tsare kofar ofishin gwamna, wani kason kuma ya tsaya a ƙofar shiga majalisa, inda ɗaya kason ya tsare babbar ƙofar shiga farfajiyar sakatariyar.

Duk da dai 'yan ƙungiyar sun haɗu da fushin jami'an tsaro musamman 'yan sanda, sun ta yin yunƙurin ganin sun kafa tutar da suka kira ta ƙasar Yarabawa.

To sai dai rundunar soji a jihar ta Oyo ta sanar da kama 'yan kungiyar guda tara, inda da dama suka tsere.

Jami'an tsaro sun ce suna gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar al'amarin da kuma haƙiƙanin su wane ne 'yan kungiyar.

Wa ke kitsa yunƙurin?

Bayan harin na masu fafutukar kafa ƙasar ta Yarabawa kuma sai wata mace mai suna Modupe mai matsakaicin shekaru ta fito a wani faifan bidiyo, wanda kuma ta ce ita matar marigayi Mashhood Abiola ce, ta yi iƙrarin cewa tana magana ne da yawun wani.

A bidiyon, cikin harshen Yarabanci ta ce "shi wannan mutumin matashi ne. Mutum nawa ne suke ganin za su iya abin da yake yi? Ya riga ya sadukar da kansa kan wannan aiki. Ya ce ba zai taɓa tsayawa takara ba ko kuma ya karɓi riƙon ƙwarya ba. Mu mutane ne masu tsari, mutane ne masu 'yanci sannan muna gudanar da ayyukanmu a tsare. Mun yanke hukuncin ficewa daga Najeriya. Mun ma fice daga Najeriya tun Nuwamban 2022." In ji matar.

Ta kuma ci gaba da cewa " muna ayyana wannan rana da cewa mu yanzu ba ma cikin wannan ƙasar. Bisa ƙarfin ikon ubangiji mahallicin giragizai da wata da taurari, ni Modupe Onitiri Abiola, nake ayyana jamhuriyar dimokradiyyar Yarabawa. Yarabawa sun zama masu ƙasar kansu.....Yau, 12 ga watan Afrilun 2024, ƙasa mai ƴanci ta Yarabawa ta fara aiki."

Masu fashin baƙi dai sun ce wannan mata ba a san ta ba kuma ba a Najeriya take ba.

Me masu rajin kafa ƙasar Yarabawa ke cewa?

Kawo yanzu dai babu wani wanda aka sani yana kira da kafa ƙasar Yarabawa da ya fito fili ya nuna goyon bayansa ga 'yan ƙungiyar awaren Yoruba Nation.

Mutane irin su Professor Banji Akintoye da Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho duk sun yi allawadai da abin da 'yan ƙungiyar Yoruba Nation suka aikata na kustawa cikin sakatariyar gwamnati.

Harwayau mutanen biyu sun bayyana ƙungiyar da ta marasa kishin ƙasa, inda kuma suka bayyana da Modupe da wadda ta ke kitsa duk abin da ke faruwa.

Afenifere ta yi allawadai da abin da ya faru

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙungiyar kare haƙƙn Yarabawa a Najeriya ta Afenifere ta bukaci hukumomi da su hukunta 'yan ƙungiyar ta Yoruba Nation bisa abin da suka yi a ƙarshen makon.

Ƙungiyar a wata sanarwa da ta fitar ta hannun sakatare janar ɗinta, Comrade Jare Ajayi, ta ce ya kamata gwamnati ta yi bincike kan abin da ya faru sannan ta hukunta duk wanda aka samu yana da hannun a al'amarin domin zama izna ga 'yan baya.

Sanarwar ta kuma barranta ƙungiyar ta Afenifere da masu fafutukar kafa ƙasar yarabawa.

" Yankin Yarabawa yanki ne a ƙarƙashin Najeriya, kamar dai yadda tsarin yake".

Ƙungiyar ta ƙara da cewa "tana da cikakken ƙwarin gwiwa da imanin a gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu

Masana dai na ganin cewa batun yunƙurin kafa ƙasar Yarabawa ba yanzu ya fara ba kasancewar an samu lokacin da kungiyoyi da dama suka yi ta kiraye-kirayen ɓallewa daga Najeriya.

Kafin kasancewar shugaba Bola Tinubu shugaban Najeriya, da dama ƙungiyoyin Yarabawa sun ta bayyana damuwar ta ci gaba da zama a Najeriya duk da dai ba sa ɗukar matakai irin wanda 'yan awaren ƙungiyar Yoruba Nation suka yi ba.

Yanzu dai za a iya cewa ƙungiyar awaren Yoruba Nation ta zama irinta ta biyu a Najeriya, bayan ƙungiyar ƴan awaren ƙasar Biafra ta IPOB wadda Mazi Nnamdi Kanu ke jagoranta.