Real Madrid za ta kara da Celta a Copa del Rey zagayen ƴan 16

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta karɓi bakuncin RC Celta a zagayen ƙungiya 16 a Copa del Rey a jadawalin da hukumar ƙwallon kafar Sifaniya ta bayyana.
Wasa ɗaya za a buga a makon, inda Real Madrid da Celta za su fafata ranar 14 ko 15 ko 16 ga watan Janairu.
Real Madrid ta kawo wannan matakin ne, bayan da ta doke Deportiva Minera 5-0 ranar Litinin, ita kuwa Celta zuwa ta yi ta samu nasara a kan Racing Club 3-2.
Wannan shi ne karo na 18 za a fafata tsakanin Real da Celta a Copa del Rey, inda ƙungiyar Bernabeu ta yi nasara takwas aka doke ta biyar daga ciki.
Real Madrid za ta fafata da Mallorca ranar Alhamis a wasan farko a daf da karshe a Spanish Super Cup a filin wasa na King Power a Saudi Arabia.
Ranar Laraba Barcelona ta kai karawar karshe a kofin na bana, bayan da ta doke Athletic Club 2-0.
Wasannnin ƙungiyoyi 16 da za a kara a Copa del Rey:
- Real Madrid da Celta
- Pontevedra da Getafe
- Ourense da Valencia
- Almería da Leganés
- Elche da Atlético
- Barcelona da Betis
- Real Sociedad da Rayo Vallecano
- Athletic da Osasuna






