Gwamnonin Najeriya sun amince da sabuwar dokar haraji tare da yin sauye-sauye

Asalin hoton, X/Nigeria Governors Forum
Gwamnonin Najeriya sun fitar da sabon tsari na rabon haraji a ƙasar, bayan wata ganawa da suka yi da kwamitin da aka kafa domin yin nazari kan ƙudurin sabuwar dokar haraji ta ƙasar.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne ya gabatar wa Majalisar dokokin tarayyar ƙasar ƙudurin yin gyaran fuska ga dokar haraji ta ƙasar, lamarin da ya haifar da zazzafar muhawara da raba kawunan shugabanni a ƙasar.
Batun ya kai ga cewa shugaba Tinubu da Majalisar Dokokin Tarayya sun jingine batun muhawara da amincewa da dokar har sai bayan an sake yin nazari a kanta.
A zaman da suka gudanar a Abuja, gwamnonin sun yi gyare-gyare ga ƙudurin harajin na shugaba Tinubu, musamman ɓangaren rabon harajin cinikayya na VAT, wanda shi ne ya fi janyo cece-ku-ce.
Shawarar da gwamnoni suka yanke

Asalin hoton, X/Nigeria Governors Forum
Sabon tsarin rabon harajin VAT da gwamnonin suka gabatar shi ne:
- Kashi 50 cikin ɗari za a raba daidai-wa-daida tsakanin dukkanin jihohi.
- Kashi 30 cikin ɗari za a raba gwargwadon gudumawar da kowace jiha ta bayar.
- Kashi 20 cikin ɗari za a raba gwargwadon yawan al'ummar kowace jiha..
Sanarwar bayan taro da ƙungiyar gwamnonin Najeriyar ta fitar, wadda ta samu sa hannun shugabanta, kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ta kuma ce ba ta goyon bayan ƙarin harajin VAT a wannan lokaci.
Sannan kuma ta bayar da shawarar cire sashen sabon ƙudurin dokar da ya shata lokacin dakatar da ware wa Gidauniyar tallafa wa manyan makarantu da takwarorinta da sabuwar dokar ta ambato kuɗi.
"Mambobin wannan ƙungiya sun amince cewa kada a yi ƙari a harajin VAT, ko rage harajin kamfanoni na CIT a wannan lokaci, domin tabbatar da daidaiton tattalin arziƙi," in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa "muna bayar da shawarar kada a sanya wani ɓangare a dokar da zai iyakance kuɗaden tafiyar da lamurra da ake ware wa TETFUND, NASENI da NITDA".
A ƙarshe, sanarwar ta ce tana goyon bayan cewa a yanzu Majalisar dokokin tarayya za ta iya ci gaba da muhawara kan dokar domin samun amincewa.
Mene ne bambancin ƙudurin da Tinubu ya gabatar da matsayar gwamnoni?

Asalin hoton, State House, Nigeria
Shawarar da gwamnonin suka cimma na nuna cewa sun rage yawan kuɗin harajin VAT da za a raba tsakanin jihohi bisa la'akari da gudumawar da kowace jiha ta bayarwurintara harajin.
Sai dai kuma shawarar gwamnonin ta ƙara yawan kason kuɗin a kan yadda yake tun asali.
Tun farko, sabon tsarin rabon harajin VAT da ke ƙunshe a ƙudurin yin gyara ga dokar haraji da shugaba Tinubu ya gabatar wa Majalisar dokoki ya buƙaci a ware kashi 60 cikin ɗari ne domin rabawa gwargwadon gudumawar da kowace jiha ta bayar.
Wanda hakan ya nunka har sau biyu a kan asalin tsarin da ake amfani da shi na kashi 20 cikin ɗari.
Shawarar da gwamnonin suka yanke na nuna cewa an ƙara kashi 10 cikin ɗari a kan tsarin da ake amfani da shi a yanzu, yayin da aka zabtare kashi 30 cikin ɗari daga abin sabon tsarin da shugaba Tinubu ya gabatar wa Majalisa.










