Yadda za a riƙa raba kuɗi tsakanin jihohi a ‘sabuwar dokar harajin’ Najeriya

Asalin hoton, X/Nigeria Governors Forum
Ana ci gaba da zazzafar muhawara a Najeriya kan sabon ƙudurin yin gyaran fuska ga dokar harajin ƙasar da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya gabatara wa majalisar dokoki.
A farkon watan Oktoba ne shugaban ya aika wa majalisar ƙudurin, wanda ya ƙunshi manyan ɓangarori guda huɗu, domin neman amincewa.
Sai dai wani ɓangare da ya fi jan hankalin al'ummar ƙasar, musamman daga ɓangaren Arewa shi ne batun rabon harajin cinikayya na VAT.
Wasu daga cikin muhimman ɓangarorin da suka yi adawa da dokar su ne: Majalisar Tattalin Arziƙin ƙasar, wadda ta buƙaci a jinkirta miƙa dokar ga majalisar dokoki.
Sai gwamnonin jihohin arewacin Najeriya, waɗanda suka buƙaci a jingine dokar.
Akwai kuma Majalisar Malamai ta Najeriya wadda ita kuma ta nuna adawa ga ɗaukacin dokar.
Sai dai duk da haka, shugaban ƙasar ya tura dokar ga majalisar dattijai, kuma har an yi wa ƙudurin karatu na biyu kuma an miƙa shi ga kwamiti domin yin nazari.
Zazzafar muhawarar da aka tafka a zauren majalisar dattijan ta ƙara tayar da ƙura game da dokar, inda wannan ya zamo babban batun da ake tattaunawa kansa a faɗin ƙasar.
Mene ne bambancin tsarin raba harajin VAT da ake amfani da shi a yanzu, kuma mene ne bambancinsa da tsarin da ke cikin ƙudurin dokar da shugaba Tinubu ya gabatar wa majalisa?
Tsarin da ake bi a yanzu wajen rabon VAT

Asalin hoton, Getty Images
Ana raba kuɗin da ake tattarawa na harajin VAT ne a tsakanin matakan gwamnati uku a ƙasar - Tarayya, da Jihohi da kuma Ƙananan hukumomi.
Gwamnatin tarayya tana samun kashi 15 cikin ɗari na kudin yayin da jihohi ke karɓar kashi hamsin cikin ɗari, su kuwa ƙananan hukumomi suna tsira da ragowar kashi talatin da biyar ne cikin ɗari.
To idan aka dunƙule abin da jihohi da ƙananan hukumomin ke karɓa wato kashi 85 cikin ɗari, to ana bin wani tsari ne na rabon a tsakaninsu.
Idan aka baje kuɗin gaba ɗaya a faifai ana ɗaukar raba daga ciki wato kashi 50 cikin ɗari a raba a tsakanin jihohin da ƙananan hukumomin.
Sai a ɗauki kashi 30 cikin ɗari a raba daidai da yawan al'umma, yayin da sauran kashi 20 cikin ɗari za a duba inda aka samu wannan kuɗi na haraji sai a ba su.
Sabon tsarin rabon VAT
A cikin sabon ƙudurin da ake taƙaddama a kai ya bayyana cewa:
Ba tare da la'akari da duk wani tsarin da kowace irin doka ta ayyana ba, harajin da aka tara ta hanyar abubuwan da aka bayyana a Babi na shida na ƙudurin dokar Najeriya, za a raba shi ne kamar haka:
Kashi 10 cikin ɗari zai tafi ga Gwamnatin Tarayya
Kashi 55% zai tafi ga gwamnatocin jihohi da Babban birnin tarayya.
Sai kashi 35 cikin ɗari wanda zai tafi ga ƙananan hukumomi.
Sai bayanin ya ƙara da cewa "kashi 60 cikin ɗari na kuɗaɗen da za a bai wa jihohi da ƙananan hukumomi za a raba su ne bisa tsarin inda aka samo kuɗaɗen.
Wannan na nufin cewa an ƙara kason da ake rabawa bisa dogaro da gudumawar da kowace jiha ta bayar daga kashi 20 cikin ɗari zuwa kashi 60 cikin ɗari.
Me ya sa ƴan arewa ke kokawa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Gwamnonin arewa sun bayyana adawarsu da sabon ƙudurin, inda suka buƙaci shugaba Tinubu ya jingine shi har sai an ƙara tattaunawa a kai.
Gwamna jihar Borno, Umara Babagana Zulum na daga cikin waɗanda aka fi jin amonsu wajen adawa da dokar.
Ya bayyana wa BBC cewa "Idan aka amince da dokar a yadda take, to kuwa gwamnoni ba za su iya biyan albashi ba."
Sabon tsarin rabon haraji ya nuna cewa tabbas jihohin arewa, waɗanda ba su cikin manyan masu bayar da gudumawa a yawan harajin da ƙasar ke tarawa za su samu tasgaro a yawan kuɗin da suke samu ƙarshen kowane wata, kasancewar kashi 60 cikin ɗari na kuɗin da aka tara za a raba shi ne bisa la'akari da gudumawar da kowace jiha ta bayar.
Ba jihohin Arewa kaɗai ne za su samu raguwa a yawan kuɗaɗen da suke samu duk wata ba, har ma da wasu jihohin kudancin Najeriya irin su Imo da Abia, waɗanda kuɗaɗen harajin VAT da suke tarawa bai taka kara ya karya ba.
Sai dai tsarin zai bai wa jihohin da suke bayar da gudumawa sosai a ɓangaren haraji tagomashi a wajen rabon, inda za su tafi da kaso mafi tsoka.
A yanzu haka Legas ce ta fi bayar da gudumawa wajen tara haraji a faɗin Najeriya, kasancewar ta jihar da ta fi kowace tarin masana'antu da kuma tara manyan ofisoshin kamfanonin da ke aiki a faɗin ƙasar.
Sai jihar Ribas wadda ke biye mata a matsayi na biyu yayin da Abuja, babban birnin Najeriya ke a matsayi na uku.











