Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muna godiya ga waɗanda suka yafe wa mahaifinmu - Hanan Buhari
Yayin da ake ci gaba da alhinin rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhamamdu Buhari, Iyalansa sun bayyana yadda ya tarbiyantar da su.
A wata hira da BBC karon farko tun bayan rasuwarsa, ƴaƴa da jikokin marigayin sun bayyana yadda mu'amala ta kasance tsakaninsu da tsohon shugaban na Najeriya.
Muhammadu Buhari ya rasu ne ranar Lahadi a wani asibiti a Landan, bayan ya yi fama da jinya.
Makusantan marigayin sun bayyana shi da mutum mai son zumunci da ƙaunar danginsa.
Lamarin da ya sa wasu ke ganin ya koma Daura bayan saukarsa daga mulki a 2023.
'Ya hore mu da gujewa cin abin da ba namu ba'
Ɗaya daga cikin manyan ƴaƴan nasa, Hadiza Muhammadu Buhari da aka fi sani da Nana, ta bayyana wa BBC wasu kyawawan halayen mahaifin nata ''waɗanda ba kowa ne ya sani ba''.
Nana - wadda ƴa ce ga tsohuwar matan marigayin - ta ce mahaifin nata ya cika da ƙaunar ƴan Najeriya a ransa.
''A wannan jinyar da ya yi na je Landa domin duba shi, bayan ya samu na ƙudiri aniyar komawa Najeriya, da na ce masa Baba zan tafi, sai ya ce ina za ki tafi?''
''Na ce masa Najeriya zan koma, sai ya ce to ki gaida ƴan Najeriya'', kamar yadda ta bayyana.
Nana Hadiza ta bayyana yadda mu'amala ta kasance tsakaninta da mahaifin nata.
''Yakan kirani da Madam Nana, mukan yi hira da wasa da dariya tsakaninmu'', in ji ta.
Ta ce marigayin ya tarbiyyantar da su game da guje wa haƙƙin da ba nasu ba.
''Bana mantawa muna ya taɓa ba mu kudin domin sayen wasu littattafan karatu, bayan na saye chanji ya ragu sai na sayi alewa....''.
''Bayan na dawo na faɗa masa, na kuma ba shi sauran chanji, sai ya ce min Nana ba a haka, idan an aike ki sayen abu da kuɗi, idan kin dawo ki kai wa wanda ya aike ke chanjinsa, idan ya ɗauka ya ba ki sai ki karɓa, amma duk abin da ba naki ba kada ki yarda ki taɓa, ki riƙe amana kar ki ci haƙƙin wani'', in ji Nana Buhari.
Ta bayyana mahaifin nata da mai barkwanci da son jama'a da kuma saukin kai.
''Mutum ne mai haƙuri da juriya ga mutane, baba ba ya son hayaniya, ba za ka zage shi ba ya rama, sai da ya sa muku ido'', in ji ta.
Nana Buhari ta ce a duk lokacin da suka haihu yakan aika wa jikan da aka haifa kunkuru biyu mace da na miji domin ya kiwata.
'Mun gode wa waɗanda suka yafe wa mahaifinmu'
Ita ma Aisha Hanan Buhari, da aka fi sani da Hanan Buhari, wadda ke cikin ƴaƴansa masu ƙananan shekaru ta bayyana irin damuwar da ta ji bayan rasuwar mahaifinta.
Hanan Buhari ta ce rashin mahaifin nata tamkar rasa wani fanni ne na jikinta.
''Abin da zan fi kewa daga gare shi shi ne barkwancinsa, ina kalallonsa amatsayin wani ɓangare nawa'', kamar yadda ta bayyana.
Hanan ta kuma gode wa ƴan Najeriyar da suka bayyana yafe wa mahaifin nasu.
''Babu abin da za mu ce musu sai godiya, alhamdulillahi'', in ji Hanan.
Ta ƙara da cewa marigayin na da kyakkyawar niyya kan ƴan Najeriya, tana mai bayyana shi da ''na kowa''.
''Hakan hore ni da yin karatu da yin addu'a da kuma yin abubuwan da ke sanya mu nishadi'', in ji ta.
'Sau uku yana bani kunkuru'
Jikar marigayin, Sa'adatu Muhammad ta bayyana yadda suka ji kan yadda 'yan Najeriya suka yi ta cewa sun "yafe masa" bayan ya rasu.
''Wannan baiwa ce mai girma, wanda yake da haƙƙi a kansa ya ce ya yafe maka, kuma akwai bidiyon neman afuwa da ya yi bayan kammala mulki, wanda ya yaɗu sosai jama'a sun gan shi'', in ji Sa'adatu.
Ta ƙara da cewa mutum ɗaya yake bai cika goma ba, don haka kowane ɗan'adam da irin tasa gazawa.
''Ko ya kake ba za ka ce wa baba ɓarawo ba, ba kuma za ka ce masa azzalumi'', in ji ta.
Kasancewa marigayin kan yi wa jikokinsa kyautar kunkuru a duk lokacin da aka haife su, Sa'adatu Muhammad ta ce ita har sau uku ya ba ta kyauta kunkuru.
''Ya bani suka mutu, ya sake bani wasu su ma suka mutu, ya ƙara min na uku, amma ya ce daga su ba zai kara min ba'', in ji ta.