Akurkura: 'Maganin' da wasu matasa ke ƙauna, NDLEA ke farauta

Akurkura

Asalin hoton, Sadiq Muhammad NDLEA Kano

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

"Ranar da na fara kuskura akurkura, ji na yi kamar Ma'laikan mutuwa ya tunkaro ni. Na ga duniya tana juyawa, komai yana canjawa," in ji wani matashi da ya daɗe yana ta'ammali da akurkura.

Matashin wanda ba ya so ambaci sunansa ya ce a ranar farkon da ya yi amfani da abin da ya kira da maganin, ya ce sai da ya yi fitsari da zawo, sannan ya matuƙar shan wahala kafin ya warware.

Mene ne akurkura?

Akurkura dai wani sinadari ne na ruwa da ake sayar da shi a cikin kwalba da sunan magani amma kuma wanda ke ƙara wa masu shansa kuzari sannan ya sa su maye.

Yanzu haka wannan sinadarin ya fara zama ruwan dare musamman a arewacin Najeriya, inda ake ganin mutane na ta'ammali da sinadari.

Asali shaƙe aka fara, inda mutane suke shaƙar wata hoda, sai su yi atishawa, wanda a cewarsu, daga wannan atishawar suna samun waraka daga zazzaɓi ko wata cutar da suke fama da ita.

Daga bisani ne aka koma akurkura, inda wasu suke haɗawa, wasu kuma suka koma amfani da akurkura kaɗai, wasu kuma suka tsaya a shaƙensu, suna masu cewa akurkura ta fi ƙarfinsu.

Yanzu dai an koma wasan ɓuya tsakanin masu sha da fataucin akurkura da jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya, inda har holensu dillalan hukumar ke yi.

'Abin da ya sa nake akurkura'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A game da abin da ya sa ya fara akurkura, matashin ya ce shi dai yanayin rayuwa ce kawai ta sa yake kukurawa, ba wai domin wani abu ba.

"Wasu sun ce akurkura na maganin zazzaɓin maleriya da typhoid, wasu sun ce tana maganin ciwon sukari. Amma dai maganar gaskiya idan muka kuskura, ƙarfin jiki take saka mana," in ji shi.

Ya ce a duk lokacin da ya shiga damuwa, ya kan nema akurkura, ya kuskura, sai kawai ya ji komai ya wuce, "sai hankalina ya kwanta. Za ka ji tamkar ka dawo aiki, ka yi wanka."

"Ni dai gaskiya zan iya cewa ta zama tamkar ƙwaya. Kuma tana da sabo, yadda idan mutum ya fara, za ta zama tamkar masifa ta yadda barinta yake da matuƙar wahalar gaske."

Matashin ya ƙara da cewa yanayin rayuwar da ake ciki ma na taka rawa, "domin mu ƴankasuwa ne, wasu lokutan muna zuwa kasuwa amma babu ciniki. Don haka idan hankali ya ɗaga, sai mu kuskura akurkura kawai mu manta da komai," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa ya saba sosai.

A game da yadda hukumar NLEA ke farautar akurkurar, da masu ta'ammali da ita, matashin ya ce, "ban yi mamaki ba gaskiya."

Ya ce duk da cewa wasu na cewa tana musu magani, ''tana da illoli sosai, saboda ko ma babu komai, yawan shan ma matsala ce."

A ƙarshe matashin, wanda ya ce shi mai kishin matasa ne, ya yi kira ga matasa da su guji kuskura akurkura.

"Yawanci ana kuskurawa ne domin matsalolin yau da kullum da kuma sabo. Ina kira ga matasa da su riƙa mayar da komai ga Allah kawai. Waɗanda ba su fara, kada su fara, mu da muke yi kuma mu haƙura," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa shi ma yana fata nan gaba kaɗan zai daina.

"Duk da na san akwai wahala, amma zan yi ƙoƙari saboda yanzu haka ma da ban sha ba, wani iri nake ji," in shi, sannan ya ƙara da cewa akurkura ta riga ta zama ruwan dare a tsakanin matasa da ma dattawa.

Abin da ya sa muke kamawa - NDLEA

A game da wannan ne BBC ta tuntuɓi hukumar NDLEA, inda babban jami'in hukumar na Kano, Abubakar Idris Ahmad ya ce sun fi mayar da hankali kan dillalan sama da masu kuskurawa.

Ya ce a cikin akurkura ɗin sun gano cewa ana cakuɗawa da wasu sinadarai waɗanda a dokokin Najeriya da ma na Majalisar Ɗinkin Duniya ta'ammali da su laifi ne da masu yi za su iya fuskantar doka.

"Yawanci idan muka kama akurkura, muna zuwa ɗakinmu na gwaje-gwaje ne, sai a bincika abubuwan da ke ciki. Idan sakamakon binciken ya nuna akwai sinadaran tabar wiwi a ciki ko na codein ko kuma wasu sinadaran da akwai doka a kansu a Najeriya da ma Majalisar Ɗinkin Duniya, akurkura ɗin ta zama ƙwaya ke nan," in ji shi.

Ya ce bayan sakamakon binciken ya fito ne sai su ƙara faɗaɗa bincike, "sai mu miƙa waɗanda muka kama zuwa kotu, sai mu gabatar da hujjojinmu da ke tabbatar da akwai sinadaran da amfanin da su laifi ne, sai alƙali ya yi hukunci daidai da laifin sinadarin da aka gano a ciki."

Babban jami'in hukumar ya ce idan suka gano sinadarin tetrahydrocannabinol wato babban sinadarin da ke cikin tabar wiwi, "to hukuncin akurkura ɗin daidai yake da mai fataucin tabar wiwi. Idan kuma sun cakuɗa su ne da sinadarai masu yawa na laifi, sai mu gabatar da hujjoji a kotu, sai alƙali ya yi hukuncin da yake ganin ya fi dacewa da su," in ji shi.

'Masu akurkura abin tausayi ne'

Babban jami'in hukumar ya ce komar kamensu ta fi komawa kan masu dillancin akurkurar saboda a cewarsa, "cutar masu sha ake yi, ana yaudararsu cewa magani suke sha."

Ya ce sun fahimci cewa masu fataucin suna cutar da masu ta'ammali da akurkura ɗin ne, "saboda ba ana sayar musu da ita ba ne a matsayin abu mai bugarwa. Ana sayar musu ne a matsayin maganin wasu cututtuka. To kuma akwai abin da muke kira da dependence, wato dogaro wanda masu kuskurawa suke faɗawa, wanda hakan ke sawa su kasa dainawa idan sun fara."

Ya ce akurkura ɗin na taɓa hankali da ƙwaƙwalwa da ƙoda da hanta, "ka ga ke nan ana cutar masu sha ana karɓe musu kuɗi da sunan suna shan magani, alhali suna amfani ne da abin da ke cutar da su."

Ya ce hakan ya sa suka ƙuduri aniyar yaƙi da fataucin akurkura ɗin, "domin mu fitar da masu sha ɗin daga cikin damuwa, domin idan muka daƙile fataucin, masu sha ɗin za su huta. Za ka ga waɗanda suka fara ɗin suna cikin damuwa, amma sun kasa fita saboda tarkon da suka faɗa."

Sai dai ya ce suna da ƙwararru da suke taimakawa wajen wayar da kan mutane hanyoyin daina kuskurawa da ma daina shan dukkan wata ƙwaya mai cutarwa ga lafiyarsu.

Ya ce duk da cewa akwai doka a kan masu ta'ammalin, "amma yawancin bincikenmu ya gano yaudararsu ake yi, sannan da zarar sun fara sai su kasa fita, suna ta kashe kuɗi, masu fataucin na cinye musu kuɗi. Kuma abin mamaki yawancin dilolin ba sa yi."

A game da yadda suke yi da tulin akurkurar da suka kama, Abubakar Idris Ahmad ya ce lalata suke yi.

"Idan muka gabatar a kotu, kotun ce take faɗa mana yadda za mu yi, amma mafi yawan lokuta cewa take yi mu lalata. Yawancin miyagun ƙwayoyi ƙonawa muke, kuma muna gayyatar ƴanjarida a kotun da ma mutanen gari domin su shaida yadda muke ƙonawa."