Me ya sa har yanzu sanyi bai kankama ba a arewacin Najeriya?

Lokacin karatu: Minti 3

A wani yanayi da ba a saba gani ba, an shiga watan Janairu na sabuwar shekara, amma har yanzu yanayin sanyi bai kankama ba a wasu sassan ƙasar, musamman a arewacin Najeriya.

A ƙa'ida, a duk ƙarshen shekara irin haka, yawanci watannin Disamba da Janairu, a kan yi fama da yanayin sanyi sosai, inda sanyin yake bayyana hazo a wasu biranen yankin arewacin ƙasar.

Wannan ya sa wasu suke nuna damuwarsu, yayin da wasu kuma suke tambayar me yake faruwa ganin wani yanayi ne da ba a saba gani ba.

A daidai lokacin da wasu ke ganin sauyin yanayi ne kawai da babu wata matsala, wasu kuma suna ganin akwai wasu abubuwan da ke faruwa.

Sai dai masana na ganin dole akwai wasu abubuwa da suka danganci sauyin yanayi da suka jawo hakan, waɗanda kuma suke cewa suna da alaƙa da wasu ayyukan da ƴan'adam suke aikatawa.

Alaƙa da sauyin yanayi

Domin jin me ke faruwa, BBC ta tuntuɓi daraktan ƙungiyar harkokin sauyin yanayi ta Climate Change, Umar Saleh Anka, wanda ya ce jinkirin da aka samu yana da alaƙa ne da sauyin yanayi da duniya ke fuskanta.

A cewarsa, ''jihohin arewacin Najeriya irin su Yobe da Benue da Adamawa da Sokoto da Katsina da Kano da Kano da Jigawa sun fuskanci jinkirin yanayin sanyi, ko kuma sanyin bai kankama ba.''

Ya ce a ƙa'ida, yanayin jihohin yankin an fi sabawa ne da samun sanyi a tsakanin Nuwamba zuwa cikin watan Maris, ''amma yanzu an samu gagarumin sauyi, wanda alama ce da ke nuna sauyin yanayi.''

A game da babban dalilin da ya jawo haka, Umar Anka ya ce a shekarar 2025 ruwan sama ya ja har zuwa lokacin da aka saba ganin rani a wasu sassan arewacin ƙasar, "Wanda hakan ya sa sararin samaniya ya ci gaba da kasancewa cikin yanayin damshi," in ji shi.

Masanin sauyin yanayin ya ce wannan ne kuma hana bushewar da ake buƙata domin iskar hunturu ta fara ƙadawa.

"Sannan kaɗawar wannan iskar na da alaƙa da rashin samun yanayin sanyi da sauri," in ji shi.

Masanin ya ƙara da cewa akwai wasu abubuwa da suka haɗa da ɗumamar yanayi da sare itatuwa da share dazuka da sauran "abubuwan da suke gurɓata muhalli da ke jawo sauyin yanayi," in ji shi, inda ya ƙara da cewa suna taimakawa wajen ƙara ta'azzara duk wani canji da aka gani.

"A taƙaice an samu canjin ne saboda ɗumamar yanayi da sauyin da ake samu a yanayin lokacin damuna da kuma yanayin kaɗawar iska a sararin samaniya,'' in ji shi, inda ya ƙara da cewa yanzu rabe-raben lokutan yanayin zai canja.

Me za a iya yi?

A duk lokacin da aka samu abu irin wannan da ba a saba gani ba, hankali yakan koma ne kan ko akwai abun da za a iya yi domin gyara, da ma hanyoyin da za a bi domin magance matsalar a gaba.

A game da wannan, Umar Saleh Anka ya ce matsalolin da aka samu a sanadiyar sauyin yanayi ba abu ba ne da za a iya gyarawa nan take.

"Ba a gyarawa ko canja abubuwan da sauyin yanayi ya janyo cikin ƙanƙanin lokaci, sai dai a rage a hankali ko kuma a rage illolinsa."

Masanin ya bayyana wasu matakai da ya ce suna da muhimmanci a ɗauka kamar haka:

  • Dasa itatuwa
  • Rage sare itatuwa
  • Noman zamani da ba ya gurɓata muhalli
  • Amfani da iri mai jure fari
  • Wayar da kai
  • Samar da dokoki kan sauyin yanayi

Anka ya ce akwai buƙatar gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen tsara dokoki da suka danganci sauyin yanayi da rage tasirinsa.

"Mu dai a ɓangarenmu na ƙungiyoyi masu zaman kansu, tuni mun fara ayyuka da za su rage illolin ko tasirin sauyin yanayi. Muna kuma fata za mu haɗa ƙarfi da ƙarfe da gwamnati domin samun nasara."