Ana zargin malamin Islamiyya da yin lalata da yara huɗu a Gombe

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta ce ta kama wani matashi mai shekara 38 malamin Islamiyya bisa zargin lalata da wasu yara mata guda huɗu duka ƴaƴan mutum ɗaya.
Rundunar ta tabbatar da kama malamin kamar yadda mai magana da yawunta, DSP Mahid Mu’azu Abubakar ya yi wa BBC ƙarin bayani.
A cewarsa yaran da abin ya rutsa da su ƴan shekara 12 ne da tara da kuma takwas.
"Ba asalin malaminsu ba ne, yana zaune ne a makarantar Islamiyya ɗin, idan suka zo biya karatu, babban malami zai ce su je wajen wanda ake tuhuma da laifin domin su biya masa, sai yake amfani da wannan dama wajen yin lalata da yaran." in ji kakakin rundunar.
Ya ce an ɗauki lokaci matashin yana cin zarafin ɗaliban kasancewar yaran ƙanana ne da ba sa iya yi wa iyayensu bayanin abin da ke faruwa da su a makaranta.
Kakakin rundunar ya ce an kai ga gano lamarin ne bayan da aka samu; "ƙorafi da aka samu cewa akwai wata daga cikin ƴaƴan mutumin ƴar shekara 16 da wani mutum daban ya yi mata fyaɗe.
"Wanda ana fara wancan binciken ne har shi wannan ya fito wanda shi matashin mai shekara 38 ya kasance ya bayyana cewa yana lalata da yara ƙanana idan suka zo biya karatu a wajensa."
DSP Mahid Mu’azu Abubakar ya ce malamin ya bayyana musu cewa wannan ne karon farko da aka same shi da aikata lamarin a kan yaran, ’ba wannan ne karon farko ba, ya yi aƙalla sama da biyu, sama da uku ma.''
A cewarsa, an kai yaran asibiti domin gudanar da bincike kan lafiyarsu yayin da shi wanda ake zargin aka tasa ƙeyarsa kotu domin fuskantar shari'a.
Kakakin ya kuma shawarci iyaye da su kasance masu jan hankalin ƴaƴansu tare da jansu a jika domin yaran su riƙa sakin jiki da su su faɗa musu halin da suke ciki.
"Ko da ɗa namiji ne ka san ina ya je kuma me yake tafiya da shi, idan ba ka janshi a jika, ba za ka samu bayanin da za ka samu tattare da shi ba." in ji kakakin.











