Dalilan da suka janyo yawan mace-mace a aikin Hajjin Bana

.

Asalin hoton, Getty Images

Aikin Hajjin Bana ya gamu da iftila'i daban-daban, inda akalla mahajjata 922 waɗanda suka fito daga ƙasashe da dama suka rasu, yawancinsu sun rasu ne sakamakon tsananin zafi da aka samu, a cewar alkaluman kamfanin dillancin labarai na AFP.

Miliyoyin mutane ne daga faɗin duniya ke ziyara zuwa Saudiyya a kowace shekara domin sauke farali.

An kammala aikin Hajjin Bana wanda ake so Musulmi ya yi ko sau ɗaya a tsawon rayuwarsa muddin Allah ya hore masa ranar Laraba.

Sai dai BBC ba ta tabbatar da sahihancin alkaluman waɗanda aka ruwaito mutuwarsu ba.

A ranar 19 da 20 ga watan Yuni, BBC ta buƙaci hukumomin Saudiyya su yi magana kan mace-macen da kuma sukar da ake yi musu, sai dai ba ta samu martani daga gare su ba.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mata na rike da wani fanka ta hannu domin bai wa wani mutumi iska lokacin jifan shaiɗan

Sai dai, Masarautar Saudiyya ta bayyana irin nasarori da ta samu a bangaren kiwon lafiya yayin aikin Hajjin Bana.

"Ba a samu ɓarkewar wani cuta ba ko barazana ga lafiyar al'umma a aikin Hajjin Bana, duk da irin ɗimbin mahajjata da kuma kalubale da aka fuskanta sakamakon yanayi na zafi," kamar yadda minsitan kiwon lafiya na Saudiyya Fahad al-Jallayel ya bayyana a cikin wata sanarwa.

Hukumomin ƙasar sun kiyasta cewa mutum miliyan 1.83 ne suka halarci aikin Hajjin Bana, inda miliyan 1.6 suka fito daga ƙasashen waje. Mahajjatan ketare sun kunshi na Pakistan, Jordan da kuma Tunisiya.

BBC ta duba dalilan da suka janyo mutuwar mahajjata da dama a aikin Hajjin Bana:

.

Tsananin zafi

An yi imanin cewa tsananin zafi da aka fuskanta a Saudiyya, wanda ya kai maki 51.8 na ma'aunin Celsius, na cikin manyan abubuwa da suka janyo mutuwar alhazai da dama.

Duk da irin gargaɗi da ma'aikatar lafiya ta Saudiyya ta yi na cewa a riƙa shan ruwa akai-akai da kuma kaucewa shiga wurare masu zafi, mahajjata da dama sun gamu da tsananin zafi.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan wata mata ce wadda ta fuskanci tsananin zafi ake tura wa kan keken-zama yayin da mahajjata suka isa Mina domin jifan shaiɗan

Wani Balarabe jami'in diflomasiyya, ya ta'allaka mutuwar mahajjatan Masar da suka kai 658 da tsananin zafi. Yawancin mahajjatan ba su da cikakkun takardun yin aikin Hajji, abin da ya takaita su samu taimako da ta kamata.

"Allah ne kaɗai ya sa na rayu, saboda na fuskanci tsananin zafi," in ji Aisha Idris, wata mai aikin Hajjin daga Najeriya, yayin da take magana da shirin Newsday na BBC.

"Sun kulle dukkan kofofin Kaaba. Ya kasance sai dai muka yi amfani da samansa wajen kare kai daga tsananin zafi."

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Musulmi na hallara zuwa Saudiyya daga sassan duniya daban-daban domin yin ibada a Kaaba, wanda ke tsakiyar masallacin Harami mai Tsarki

"Na yi amfani da lema da kuma zuba ruwan Zamzam a kaina lokaci zuwa lokaci.

"Akwai wani lokaci da na ɗauka cewa zan suma, sai da wani ya taimaka min da lema. Ban taɓa tsammanin cewa zafin zai kai haka ba," in ji ta.

Haka ma, an ruwaito mutuwar wata Hajiya, mai suna Naim saboda tsananin zafi, inda ta bar iyalanta cikin zullumi.

"Hanyar sadarwa tsakanina da mahaifiyata ya katse nan take. Mun shafe tsawon kwanaki muna nemanta, inda daga karshe muka samu labarin cewa ta rasu lokacin aikin Hajji," kamar yadda ɗanta ya faɗa wa sashen BBC Arabic, inda ya ce za su cika mata buri na ganin an binneta a Makkah.

.

Mahajjata sun fuskanci matsaloli na irin zafin da ba a saba gani ba, buɗadɗun wurare, da kuma yawanci da suka kasance tsofaffi ko kuma rashin lafiya.

Mutane da ke mutuwa sakamakon tsananin zafi lokacin aikin Hajji dai ba sabon abu bane, kuma an fara fuskantar haka tun shekarun 1400.

A bara, jami'an Saudiyya sun ruwaito alhazai 2,000 da suka fuskanci tsannain zafi.

Masana kimiyya sun yi gargaɗin cewa ɗumamar yanayi na duniya zai ƙara tsananta al'amura.

.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Hukumomi sun bijiro da matakai daban-daban na samar da yanayi na sanyi

"An gudanar da aikin Hajji a lokacin zafi sama da ƙarni, sai dai matsalar sauyin yanayi na tsananta al'amuran," kamar yadda Carl-Friedrich Schleussner shugaban wata ƙungiya kan sauyin yanayi ya shaida wa Reuters.

Bincikensa ya nuna cewa ƙaruwar zafi a duniya da maki 1.5 na ma'aunin celcius da barazanar tsananin zafi lokacin aikin Hajji zai ƙaru sau biyar.

An yi kiyasin cewa duniya za ta fuskanci ɗumi na maki 1.5 a shekarun 2030, abin da zai ƙara saka kalubale kan masu niyyar zuwa Hajji.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A nan mahajjata ne rage zafin da suke ji ta hanyar fesa ruwa lokacin da suka ziyarci dutsen Arfat

Cunkoso da rashin tsaftar muhalli

A cewar bayanai da dama, rashin iya tsari na hukumomin Saudiyya ya ƙara ta'azzara batun tsananin zafi, abin da ya janyo matsaloli a wurare da dama da aka ware wa mahajjata.

Sun ce ba a kula da gidajen mahajjata yadda ya kamata ba, inda tantuna suka cika da cunkoso da kuma rashin abubuwan sanyaya su da na tsaftace wuraren.

Amina (wanda ba shi ne sunanta na aini ba), mai shekara 38 daga Islamabad, ta ce: "Babu na'urorin sanyaya tantuna lokacin zafi a Makkah. Na'urorin da aka samar sun kasance ba su da ruwa a lokuta da dama.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu mahajjata sun yi korafin cewa na'urorin sanyaya tantuna sun yi ƙaranci a wasu masaukansu

"Mun gamu da rashin iska a gidajenmu inda ta kai sai gumi muke fitarwa, abun babu kyawun gani," in ji ta.

Ita ma, wata mai aikin Hajji daga Jakarta mai suna Fauziah, ta ce, "Mutane da dama sun suma saboda cunkoso da tsananin zafi a tantunansu.

"Ba mu samun abincin dare kan lokaci, don haka mutane sun kasance cikin yunwa," in ji Amina.

Matsalar sufuri

Mahajjata sun kasance sai sun yi tafiyar kafa mai nisa a cikin zafi, inda wasu ke ɗora alhakin haka kan rashin tsari mai kyau na sufuri da kuma toshewar hanyoyi.

Wata Hajiya daga Pakistan wadda ba ta so a bayyana sunanta ba, ta ce: "Muna tafiya ta tsawon kilomita bakwai ba tare da ruwa da kuma inuwa ba. Ƴansanda sun kafa shingayen bincike, abin da ke tilasta mana yin tafiyar kafa mai isa ta gaira babu dalili. "

A cewarta, gwamnatin Saudiyya ta tanadi ababen hawa, sai dai ba a yi amfani da su wajen ɗaukar mahajjatan da ba su da lafiya saboda tsananin zafi.

"An ajiye mutane kamar kaji ko dabbobi a gona cikin tantuna, babu isasshen wurin wucewa tsakanin gado zuwa gado, kuma wuraren yin wanka sun yi kaɗan wa ɗaruruwan mutane."

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hukumar Sufuri ta Saudiyya ta ce ta samar da motocin bas sama da 27,000 domin jigilar mahajjata

Rashin bayar da kulawar lafiya da wuri

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hukumomin Saudiyya sun ce sun samar da ƙarin jami'an lafiya domin kula da masu aikin Hajji

An ruwato cewa Alhazai da dama ba su samu kulawar lafiya da ta kamata ba.

A cewar wasu mahajjata, sun ce motocin ɗaukar marasa lafiya ba su zuwa kan lokaci domin kula da waɗanda ke fama da tsananin zafi ko kuma ciwo a jikinsu.

Amina ta tuna lokacin da wani mahajjaci ke buƙatar na'urar taimakawa wajen yin numfashi, inda sai da aka shafe mintuna 25 kafin motar ɗaukar marasa lafiya ta isa wajen duk da irin yanayi da suke ciki.

"Daga karshe, motar ta isa kuma likitan bai duba mutumin ba na wasu dakikai, sannan ya ce 'babu abin da ya faru da shi' sai kawai ya yi tafiyarsa," in ji ta.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsananin zafi da ya kai maki 51.6 ya taimaka wajen galaibatar mahajjata

Sai dai, ministan lafiya na Saudiyya ya bayyana irin kuɗaɗe da aka ware domin tabbatar da alhazai sun kasance cikin koshin lafiya.

Wata sanarwa da gwamnati ta fitar, ta ce an tanadi asibitoci 189, da kuma na tafi da gidanka wanda ke da gadaje da ba su gaza 6,500, da kuma likitoci, ma'aikata da masu taimako kusan 40,000.

Baya ga wannan, akwai kuma motocin ɗaukar marasa lafiya 370, da motocin kai kayayyaki guda 60 da sauransu.

.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Musulmi sun taru domin yin ɗawafi a Kaaba, inda suke zagaya ɗakin sau bakwai, wanda kuma ya kasance wuri mai tsarki na addinin Musulunci

Tsofaffi da mara lafiya

Mahajjata da dama na zuwa aikin Hajji ne idan suka manyanta, bayan tara kuɗi na tsawon lokaci, tare da fatan cewa idan za su mutu, su mutu a can.

Alal misali, al'ummar Musulmi a Bangladesh na ganin abu mai kyau ne mutum ya rasu yayin aikin Hajji.

Wannan ne ɗaya daga cikin dalilai da suka sa ake samun mace-mace a kowace shekara a aikin Hajji.

Mahajjata 200 ne suka rasu a aikin Hajji a bara.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An ruwaito cewa Annabi Muhammad (S.A.W) ne ya gina Makabartar Al-Baqi da ke Saudiyya, inda ta kasance ɗaya cikin makabartu mafi tsarki