Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mene ne tanadin doka kan zaɓen shugabannin majalisa?
A watan Yunin 2023 ne ake sa ran rantsar da sabuwar Majalisar Dokokin Najeriya.
Sai dai a yanzu, hankali ya fi karkata ga zaɓen waɗanda za su jagoranci majalisun biyu.
Najeriya dai tana da zauruka biyu a ƙarƙashin Majalisar Dokoki ta Tarayya.
A ɓangaren farko, akwai Majalisar Dattawa mai sanatoci 109, wato mutum uku daga kowacce jiha, sai kuma Babban Birnin Tarayya mai sanata ɗaya.
A gefe ɗaya kuwa, akwai mambobi 360 a cikin Majalisar Wakilai.
Sai dai saɓanin majalisar dattawa, kowacce jiha na da ƴan majalisar tarayya ne dai-dai da yawan al’ummar da ke cikinta.
Waɗannan mambobi su ne ke haɗuwa su zaɓi shugabannin majalisar, da suka haɗa da shugaban majalisar da mataimakinsa da kuma sauran manyan shugabanni.
Yadda ake zaɓen shugabannin majalisa
A ranar farko dai dukkanin zaɓaɓɓun mambobin za su hallara a zauren majalisar, inda a nan za su sha rantsuwar kama aiki.
Da farko, dokar majalisar ta fi bai wa yan majalisun da suke dawowa a karo na biyu ko sama da haka damar neman shugabancin, duk da dai hakan bai haramta wa sabbin ƴan majalisa neman shugabancin ba.
Daga nan ne kuma, sai ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun sanatocin zai gabatar da buƙatar zaɓen ɗaya daga cikin takwarorinsa a matsayin shugaba.
Idan dai akwai masu neman kujerar sama da ɗaya, sai magatakardan majalisar ya gudanar da ƙuri'a, inda sanata da ya samu ƙuri'a mafi rinjaye wadda babu tababa, wato biyu bisa uku, ne kaɗai za a bayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
A bisa al’ada, batun shugabancin majalisun tarayya shi ne ya fi tayar da ƙura a siyasance, bayan kammala zaɓuka.
Kuma a mafi yawan lokuta, irin shugabannin da aka zaɓa, su ne za su nuna salon yadda dangantaka za ta kasance tsakanin ɓangaren zartarwa da masu yin doka.
Duk da cewa an fi jin amon masu neman muƙamin shugaban Majalisar Dattijai, da kuma na Majalisar Wakilai, to amma akwai sauran muƙamai waɗanda suna da matuƙar muhimmanci kuma ana gogoriyo wajen neman su.
Mataki da tanadin doka kan zaɓen shugabannin majalisa?
A tattaunwarsa da BBC, Hon Abdurrahman Kawu Sumaila, wanda ya shafe shekara 20 yana harkokin majalisa, kuma zaɓaɓɓen sanata a majalisa ta 10 ya shaida cewa dukkanin 'yan majalisa ke haɗuwa a zauruka su gabatar da sunan wanda suke so.
Ya ce daga nan kuma shi wanda ake so ko aka bayar da sunansa sai ya tashi ya amsa takarar.
Sannan bayan tabbatar da yawan mutane ko adadin masu takara, sai a shiga batun zaɓe.
Zaɓen na kasancewa iri biyu, ko a bayyane ko a boye, a cewar Kawu Sumaila.
Ɗan majalisar ya ce bayan duk waɗannan tsare-tsare sai a shiga batun rantsuwa da soma aiki bayan kammala jefa kuri'a.
Ya ce a tsawon shekarun da ya kwashe a majalisa an samu lokacin da aka yi zaɓe, wani lokaci kuma sasanci, ya bayar da misalin majalisa ta biyar, lokacin da Aminu Bello Masari ya zama shugaban majalisar wakilai bayan an tatattauna tare da sasantawa da ƴan majalisa na ɓangaren adawa.
Sannan ya ce a lokacin Patricia Etteh an yi yunƙurin hakan, sai dai daga baya an cire ta, wasu suka tsaya takara a zamanin da aka zaɓi Bankole.
Haka lokacin Aminu Waziri Tambuwal da Mulikat Adeola Akande zaɓe aka gudanar.
Babu batun shiyya a kundin tsarin mulki kasa
Hon Kawu Sumaila ya shaida cewa a tsari da tanadi na kunɗin tsarin mulki babu dokar da ta ce dole a ware shugabanci majalisa ga wata shiyya ko ɓangare na ƙasa.
Abin da kundin tsrain mulki ya ce shi ne a zaɓi ɗaya daga cikin 'yan majalisa ba tare da la'akari da jam'iyya ko addini ko ɓangarensa ba, dama ce da kowa ke da ita.
Kawai ɓangaren zartarwa a kowanne lokaci yana son ya mallaki majalisa ne saboda ita ce 'ƴar sandansu', a cewarsa.
Kuma sau tari duk lokacin da ake ce hakan abin ba ya yin nasara, shi yasa a lokuta da dama majalisa ke tutsu ta kori wanda aka sa, idan ɓangaren zartawa ya yi tasiri.
Kullum ɓangare zartwarwa idan ya mallaki majalisa, ana samun matsala a kasa tsakanin ɓangarorin biyu, in ji Kawu Sumaila.
'Bangaren rinjaye na tasiri sosai'
Dan majalisar ya tuno da majalisa ta bakwai, lokacin da marasa rinjaye suka tabbatar da naɗa wanda suke so.
Ya ce a wannan lokaci an saɓa ra'ayin masu rinjaye, shi ne aka tsayar da Aminu Tambuwal da Emeka Ihedioha, sannan a majalisa ta takwas marasa rinjaye ne suka tsayar da Bukola Saraki.
Sauran muƙamai a Majalisar Dokokin Tarayya
- Shugaban Majalisar Dattawa/Wakilai
- Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa/Wakilai
- Shugaban masu rinjaye
- Mataimakin shugaban masu rinjaye
- Shugaban marasa rinjaye
- Mataimakin shugaban marasa rinjaye
- Babban mai tsawatarwa
- Mataimakin mai tsawatarwa
- Mai tsawatarwa na marasa rinjaye
- Mataimakin mai tsawatarwa na marasa rinjaye