Dalilin da ya sa Majalisar Dattijan Najeriya za ta yi muhawara kan hukuncin kotun da ya soke ingancin sashe 84

Majalisar Dattijan Nijeriya ta ce za ta tafka muhawara kan hukuncin babbar kotun tarayya ta Umuahia wanda ya rushe ingancin sashe na 84 ƙaramin sashe na 12 na dokar zaɓen 2022 a ranar Laraba.

A ranar Talata ne wani ɗan majalisar dattijai Sanata George Sekibo ya bijiro da batun a zauren Majalisar, amma ta jingine muhawara kansa zuwa yau Laraba.

Matakin na zuwa ne bayan kotun ta mai shari'ah Evelyn Anyadike ta umarci Atoni Janar na Tarayya ya goge sashen.

Sashen ya bukaci ministoci da kwamishinoni da shugabannin hukumomi da mataimaka na musaman a dukkanin matakai su ajiye aiki kafin su iya shiga duk wani zaben fitar da gwani da kuma tarukan fitar da shugabannin jam'iyyu a kasar.

A ranar juma'ar da ta gabata ne wata kotu a Umuahia ta ce sashen ya saba wa tanade-tanaden tsarin mulki Najeriya sai dai kuma Sanata George Sekibo ya ce dokar zaben ta fito ne daga majalisunsu na tarayya don haka kamata ya yi a shigar da su a matsayin wani bangare na wannan shari'a.

Shugaban masu rijnjaye a majalisar dattijai Sanata Yahaya Abdullahi ya yi shaida wa BBC cewa sun dage zaman ne saboda ba su da yawa a zauren majalisar lokacin da aka gabatar da kudurin

"Lokacin da aka kawo wannan kudurin, mutane ba su da yawa a cikin majalisar sai mu shugabannin muka ga cewa wannan ba karamar magana ba ce kuma bai kamata mu daidaikun da ke cikin majalisar mu kawo wannan maganar alhali mafi yawacin wadanda suke da hakki a cikin wannan almarin ba sa cikin majalisar", in ji shi.

Ya kuma kara da cewa " Shi ya sa muka ce tun da wannan babbar magana ce ya kamata a bari a jira a gaya wa kowa cewa za a yi wannan mahawara domin duk wanda yake son ya tofa albakarci baki zai samu damar yin haka kuma a zartar da kuduri wanda kowa zai amince da shi".

Sai dai Sanatan ya ce bayan sun tafka mahawar ne sannan za su san ko majalisar za ta daukaka kara kan hukuncin kotu

Tuni dai Antoni Janarar na Najeriya kuma Ministan Shari'a Abubakar Malami ya ba da sanarwar cewa zai tabbatar da cika umarnin da kotun ta bayar a kan wannan sashe.

Tun farko Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi majalisar dokokin tarayya ta cire wannan sashi daga ciki sabuwar dokar zabe ta 2022 amma ta yi watsi da wannan bukata.

Daga bisani ne kuma wani lauya kuma jigo a jam'iyyar Action Alliance Nduka Edede ya garzaya kotu inda ya shigar da kara yana kalubalantar ministan sharia kan wannna batu

Wasu gwamnonin sun umurci masu rike da mukaman siyasa a jihohinsu da ke neman tsayawa takara a kan su sauka daga kan mukamansu