Abin da ya sa za a ƙayyade wa mutane amfani da ruwa a Birtaniya

Asalin hoton, DANNY LAWSON/PA WIRE
Ingila da Wales sun fuskanci matsanancin yanayi na ƙarancin ruwa mafi muni tun shekarar 1976 - lokacin da aka fara auna wa mutane ruwan da za su yi amfani da shi.
Lamarin ya sa ana fargabar ko Birtaniya za ta sake faɗawa cikin fari.
Me ya sa ake gargaɗin faɗawa fari a 2022?
Kwamatin Ƙiyasta Fari na Ƙasa ya saka Ingila a ma'aunin "yanayin fari mai tsayi" - mataki na ƙarshe kafin faɗawa cikin ƙrancin ruwa - yayin wata ganawar gaggawa.
Cikin wata uku na farkon 2022, ruwan sama na Ingila ya ragu zuwa kashi 26 cikin 100, a Wales kuma ya koma kashi 22.
Hakan na nufin tun kafin a shiga lokacin bazara, yanayin motsawar koguna ya yi ƙasa da yadda aka saba.
An ga kuma yadda watan Yuli ya zo da matsanancin zafi da ba a taɓa gani ba, sannan ruwan sama ya ragu zuwa kashi 76 cikin 100.
Kazalika, ofishin kula da yanayi ya yi hasashen ƙruwar bushrwa da kuma zafi. Lamarin ya ƙara ta'azzara ne ta hanyar ƙaruwar yawan amfani da ruwa.
An yi amfani da fiye da kashi 28 cikin 100 na ruwan da ke ƙarƙashin ƙsa fiye da kima, a cewar gwamnati.
Ko za a iya ƙayyade wa mutane ruwan da za su yi amfani da shi?
An bai wa kamfanoni damar saka dokar ƙayyade amfani da ruwa don daƙile ƙarancinsa.
Ana saka dokar ce idan aka ga koguna na ƙafewa. Southern Water zai kafa dokar ƙayyade ruwa ranar 5 ga watan Agusta ga kwastomominsa na Hampshire da Isle of Wight.
Zuwa yanzu sauran kamnfanoni ba su sanar da ƙayyade amfani da ruwan ba - amma an nemi mazauna kudancin Ingila da na tsakiyar ƙasar da su dinga amfani da ruwa kaɗan.
Mene ne tasirin fari?

Asalin hoton, Reuters
Tasirin fari ka iya ƙunsar abubuwa kamar haka:
- mutuwar kifaye
- haifar da gurɓacedwar kogi
- wutar daji
Ƙungiyar Manoma ta Ƙasa na bins sawun lamarin ƙafa da ƙafa.
Tuni manoman 'ya'yan itatuwa suka fara ba da rahoton asarar amfaninsu. Kayan marmari kamar dankalin turawa - wanda za a fara girbinsa a wata mai zuwa - na cikin haɗari saboda buƙatar ruwa mai yawa da suke da ita.
Za a ci gaba da jin raɗaɗin abin har cikin shekara mai zuwa, yayin da wasu manoma ke jinkirta shuka saboda har yanzu ƙasar a bushe take.
Me ya faru a lokacin fari na 1976 da 2018?
Birtaniya ta fuskanci tsananin ƙarancin ruwa na tsawon watanni a 1976 da 2018.
Hakan ta faru ne sakamakon bushewar yanayi da aka ɗauki ana yi, tun daga kaka har zuwa bazara mai tsananin zafi.
A 1976, Dokar Fari ta amince a kashe famfunan ruwa na cikin gari da ma'aikatu.
A 2018 kuma, ƙarancin ruwan da aka sha fama da shi ya jawo lalacewar amfanin gona, abin da ya haddasa tashjin farashin kayayyakin abinci. An saka dokokin amfani da ruwa iri-iri a lokacin.
An ga irin wannan yanayi a wannan shekarar, ƙarancin ruwan sama da kuma tsananin zafi a watan Yuli.
Yanayin a watan Agusta zai zama mai tasiri matuƙa game da ko Birtaniya za ta faɗa cikin fari.
Ko za a fuskanci wasu farin a nan gaba?
Hukumar Ayyukan Raya Ƙasa - wadda ke bai wa gwamnati shawara - ta faɗa a kwanan nan cewa za a iya samun ƙrancin ruwa nan gaba saboda ƙaruwar al'umma da kuma sauyin yanayi.
A Birtaniya, ana yin asarar litar ruwa biliyan uku a kowace rana - adadin da zai ishi mutum miliyan 20 ke nan.
Dabarun gwamnati na shekara 25 kan muhalli na fatan daƙile waɗannan matsaloli ta hanyar zuba kuɗi kan ayyukan kyautata rayuwar mutane a gidaje da wuraren kasuwanci.











