Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yamal zai zama mai karancin shekaru da ya yi wa Barca wasa
Kociyan Barcelona, Xavi Hernandez ya saka matashi, Lamine Yamal cikin 'yan wasan da za su kara da Atletico Madrid a La Liga ranar Lahadi.
Atletico Madrid ta ziyarci Barcelona domin buga wasan mako na 30 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya a Camp Nou.
Yamal mai taka leda a The La Masia, wanda zai cika shekara 16 da haihuwa a cikin watan Yuli, watakila ya zama matashin da ya fara yi wa Barca tamaula.
Shine mai karancin shekaru a tarihi da Barcelona ta fita da shi a babban wasa a tarihi.
Yamal wanda mahaifinsa dan Morocco, mahaifiyarsa daga Equatorial Guinea, wanda aka haifa ranar 13 ga watan Yulin 2007, ya fara makarantar koyon tamaula ta Barcelona tun yana da shekara biyar.
Idan har Barcelona ta saka shi wasa ranar Lahadi a karawa da Atletico, zai zama mai shekara 15 da kwana 285 da ya fara yi mata tamaula, mai karancin shekaru a tarihin kungiyar kenan
Wanda keda karancin shekara da ya buga wa Barca tamaula a tarihi a baya, shine Armand Martinez Sagi mai shekara 15 da wata 11 da kwana biyar.
Martinez ya kafa wannan tarihin a lokacin da ya yi wa Barcelona tamaula a fafatawa da Real Gijon ranar 2 ga watan Afirilun 1992.
Barcelona tana matakin farko a kan teburin La Liga da maki 73, sai Real Madrid ta biyu mai maki 65 da kuma ta uku Atletico Madrid mai maki 60.