MDD ta bukaci a gaggauta dakatar da bude wuta a Libya

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci da a gaggauta dakatar da bude wuta a Libya bayan da aka kwashe kwana guda ana ta mummunar arangama tsakanin bangarorin 'yan siyasa a babban birnin kasar, Tripoli.

Ma'aikatar lafiya ta ce an kashe akalla mutum 23 tare da jikkata gommai a lokacin fadan.

Daga cikin wadanda aka kashe har da wani matashi mai wasan barkwanci Mustafa Baraka.

Libya na fama da rikici tun bayan juyin-juya halin da kungiyar Nato ta mara wa baya a shekara ta 2011, wanda ya yi sanadiyyar kawo karshen mulkin Kanar Muammar Gaddafi.

Duk da haka kasar ta dan samu sa'ida ta kwarya-kwaryar zaman lafiya a shekara biyu da ta gabata.

A ranar Asabar sojojin gwamnatin kasar da duniya ta amince da su suka yi kokarin kora wani jerin-gwanon motocin mayakan da ke biyayya ga Fathi Bashagha, mutumin da majalisar dokokin kasar a bangaren gabashi wadda ke zaman kishiya ga ainahin majalisar kasar, ke dauka a matsayin Firaminista.

An samu rahotannin musayar wuta da fashe-fashe a sassa da dama na babban birnin, inda ake ganin bakin hayaki na ta tashi a fadin birnin na Tripoli.

Hukumomin aikin agaji sun ce hare-haren sun fada kan asibitoci, sannan an kwashe mutane a sassan da ake fadan.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Libya ya ce a fadan ana ta kai hare-hare da makamai ta sama a unguwannin farar-hula ba tare da bambancewa ba.

Abin da ya sa ofishin ya yi kira da a gaggauta dakatar da bude wuta.

Kasar ta arewacin Afirka, mai arzikin mai a da ta kasance daya daga cikin kasashen da jama'a suka fi jin dadin rayuwa, inda ake da tsarin kula da lafiya da kuma ilimi kyauta.

To amma an kawo karshen wannan zaman lafiya da kwanciyar hankali da suka kai ta ga bunkasa.

Babban birnin kasar, Tripoli na fama da rikicin tsakanin mayaka masu gaba da juna tun shekara ta 2011.