Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wagner: Yadda aka bankaɗo sojojin hayar Rasha da ke yaƙi a Libya
- Marubuci, Daga Ilya Barabanov & Nader Ibrahim
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Russian & BBC News Arabic
Wani sabon bincike da BBC ta gudanar ya bankado yadda sojojin haya na Rasha suka tsunduma kansu a yakin da ake yi a Libya, ciki har da abubuwan da suke da alaka da laifukan yaki da sojojin Rasha.
Wata kwamfuta kirar Samsung da wani mayakin kungiyar Wagner ya bari tana dauke da bayanan da ke nuna babbar rawar da mayakan suka taka - da kuma sunayen ba-saja da sojojin suke amfani da su.
Kazalika BBC ta gano jerin kayayyakin yaki na soji wadanda masana suka ce sun fito ne daga wajen sojojin Rasha.
Sai dai Rasha ta musanta alaka da kungiyar ta Wagner.
An soma gano kungiyar ce a 2014 lokacin da take goyon bayan 'yan a-waren da ke mara wa Rasha baya a rikicin gabashin Ukraine. Tun daga wancan lokaci, kungiyar ta rika shiga rikici da ake yi kasashe kamar Syria, Mozambique, Sudan, da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Mayakan kungiyar ta Wagner sun shoga yakin da ake yi a Libya ne a watan Afrilun 2019 lokacin da suka hadu da dakarun 'yan tawayen Janar Khalifa Haftar, bayan ya kaddamar da hari kan gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya take goyon baya, wadda ke da mazauni a birnin Tripoli. An kawo karshen rikicin yayin wata jarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla a watan Oktoba na 2020.
Kungiyar ta shahara wajen yin ayyukanta cikin matukar sirri, sai dai BBC ta samu damar tattaunawa da biyu daga cikin mayakanta. Sun bayyana irin mutanen da kungiyar Wagner take dauka aiki - da kuma rashin bin ka'idojinta.
Babu shakka cewa sun kashe fursunonin siyasa - wani abu da tsohon mayakin kungiyar ya bayyana karara. "Babu wanda yake so wani mutum ya zama nauyi a gare shi."
Wannan bayani ya bayyana gaskiyar wani labarin talabijin mai suna - Haftar's Russian Mercenaries: Inside the Wagner Group - wanda BBC News Arabic da BBC News Russian suka wallafa. Wasu daga cikin abubuwan da labarin ya bankado sun hada da shaidu da ke nuna zarge-zargen aikata laifukan yaki, ciki har da kashe farar hula da gangan.
Wani dan kasar Libya ya bayyana yadda ya yi kamar ya mutu yayin da aka kashe 'yan uwansa. Bayanansa sun taimaka wa tawagar BBC wajen gano mutum da ake zargi da kisan 'yan uwansa.
Da yake bayyana wani lamari da ka iya zama aikata laifukan yaki, wani sojan gwamnatin Libya ya tuna yadda wani abokinsa ya mika wuya ga mayakan Wagner amma aka harbe shi sau biyu a cikinsa. Ba a sake ganin sojan ba tun wancan lokaci, da ma abokan mutumin uku da aka dauke a daidai lokacin.
Kazalika kwamfutar samfurin Samsung tana dauke da shaidun da ke nuna yadda sojojin haya suke da hannu wajen hakar ma'adinai da kuma dasa nakiya a hanyoyin da fararen hula suke bi a yankunan.
Dasa nakiya ba tare da sanya musu alama ba laifin yaki ne.
Sakon da ke cikin kwamfuta samfurin Samsung
Wani mayakin Wagner ne ya bar kwamfutar bayan mayakan kungiyar sun janye daga yankunan da ke kudancin Tripoli a 2020.
Abubuwan da ke cikinta sun hada da taswirar Rasha, abin da ke tabbatar da kasancewar kungiyar Wagner a yankin da kuma yadda kungiyar take gudanar da ayyukanta.
Akwai hotunan da jirgi maras matuki ya dauka da kuma sunayen ba-saja na mayakan Wagner, akalla guda daya da BBC ta yi amannar cewa ta gano. Yanzu haka kwamfutar tana wani wuri mai tsaro a ajiye.
'Jerin kayan yakin sojoji'
Wata majiya a hukumar leken asirin Libya ta bai wa BBC jerin kayan yakin sojoji da suka hada da wani littafi mai shafi 10 da aka fitar ranar 19 ga watan Janairun 2020 wanda watakila an gano su ne a wurin da mayakan Wagner suka taba zama.
Littafin ya bayyana masu daukar bai wa kungiyar kudi da kuma tsare-tsaren yaki. Ya jera abubuwan da ake bukata domin "kammala ayyukan soji" - ciki har da tankokin yaki hudu, daruruwan bindigogi kirar Kalashnikov da kuma na'urorin hangen nesa.
Wani mai nazari kan harkokin sojin kasa ya shaida wa BBC cewa rundunar sojn kasa ta Rasha ce kadai take da wasu daga cikin makaman da aka ambato. Wani masanin, wanda ya kware kan harkokin Wagner, ya ce jerin kayan yakin sojin ya nuna hannun Dmitry Utkin a cikin yakin.
Shi ne tsohon jami'in leken asirin sojan kasa na rasha wanda aka yi amanna shi ya kafa kungiyar Wagner sannan ya rada mata suna. BBC ta yi yunkurin tuntubar Dmitry Utkin amma ba ta samu amsa ba.