Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ɓangarorin da ke adawa da juna a Libiya sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta
Ɓangarorin da ke adawa da juna a Libiya sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, bayan shafe kwana biyar ana tattaunawa a Geneva.
Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta tsara tattaunawar cimma yarjejeniyar tsakanin shugabannin soji daga gwamnatin Libiya, da kuma na ɓangaren dakarun da ke hamayya da Janar Khalifa Haftar ke jagoranta.
Wakiliyar MDD a Libiya Stephanie Williams ta ce yarjejeniyar ''wata muhimmiyar alama ce ta kyakkyawan fata ga al'ummar Libiya.''
Tun bayan hamɓarar da gwamnatin Kanal Muammar Gaddafi da dakarun ƙungiyar tsaro ta Nato suka jagoranta a 2011, Libiya ta faɗa cikin rikici.
Ƙasar mai arziƙin man fetur ta zama babbar hanya ta wucewar 'ƴan ci rani zuwa Turai daga Afirka, kuma an tursasa wa ƴan Libiya da dama barin matsugunansu.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wakiliyar MDD na cewa tsagaita wutar zai bai wa mutanen da suka rasa matsugunai da ƴan ci rani da ke ciki da wajen ƙasar damar koma wa gidajensu.
Wakilin BBC Imogen Faulkes daga Geneva ya ce Ms Williams ta kuma yi gargaɗin cewa akwai jan aiki a gaba na ganin an yi amfani da abubuwan da aka cimma a yarjejeniyar.
Gwamnatin da ƙasashen duniya suka yarda da ita na iko da babban birnin ƙasar Tripoli da yankunan da ke kewaye da shi, yayin da dakarun da ke goyon bayan Janar Haftar suke iko da gabashin ƙasar daga Benghazi.
A ƙasashen duniya kuwa, da Turkiyya da Qatar da Italiya na mara wa gwamnatin da ke iko da Tripoli baya, yayin da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa wato UAE da Masar da ke goyon bayan Janar Khalifa Haftar.
MDD ta zargi Rasha da Turkiyya da UAE a watan da ya gabata kan yin fatali da umarnin dokokin ƙasa da ƙasa na shigar da makamai da aka sa wa Libiya.
Libiya ce ƙasar da take ma'adanan man fetur da iskar gas mafi girma a Afirka.
A baya-bayan nan aka ɗage takunkumin wata takwas da sojojin da ke goyon bayan Janar Haftar, wanda ya janyo wa Libiya asarar biliyoyin daloli na fitar da man ƙasashen waje.