Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bambancin mafi ƙarancin albashi a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka
'Yan Najeriya da dama sun zaƙu su ga adadin abin da gwamnati ta yanke a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi, amma idan aka duba tarihi za a ga cewa irin wannan jan-ƙafar ba sabon abu ba ne.
Sai dai 'yan ƙasar sun wayi garin ranar Laraba - ranar ma'aikata - da sanarwar cewa gwamnatin tarayya ta ƙara wa ma'aikanta kashi 25 zuwa 35 cikin 100 na albashinsu. Amma haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar ta ce wannan ba shi cikin tattaunawar da suke yi da gwamnatin a yanzu.
Yanzu haka dai ƙungiyar na neman gwamnatin ta mayar da mafi ƙarancin albashin N615,000 daga N30,000 da yake a yanzu, kuma ta ba ta wa'adin ranar 29 ga watan Mayu.
Tun a watan Afrilun 2019 gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ta amince da fara biyan N30,000 ɗin - wanda bai wuce dalar Amurka $21.50 ba.
A wannan maƙalar mun duba yadda mafi ƙarancin albashin Najeriya yake da wasu ƙasashen Afirka 11.
Afirka ta Kudu da Gabon sun ninninka Najeriya fiye da sau 11
Duk da cewa Afirka ta Kudu ce babbar abokiyar gogayyar Najeriya wajen girman tattalin arziki a Afirka, ƙasar mai yawan al'umma kusan miliyan 60 ta ninninka takwarar tata wajen biyan mafi ƙarancin albashi.
Kamar yadda doka ta tanada, mafi ƙanƙantar albashi a Afirka ta Kudu shi ne R4,405.80, wanda ya kai kwatankwacin naira 325,365.93 - ko kuma dala $235.98.
Hakan na nufin mafi ƙarancin albashi a Gabon ya ninka na Najeriya sama da sau 11.
A ƙasar Gabon kuma da ke tsakiyar Afirka, ma'aikata na karɓar mafi ƙarancin albashi mai yawan gaske idan aka kwatanta da saura.
Gwamnati ta ƙayyade mafi ƙarancin albashin kan cfa150,000 - kwatankwacin naira 335,960 (dalar Amurka 244.70).
A nan ma, mafi ƙarancin albashin ya ninka na Najeriya kusan sau 12.
Idan kuma muka duba ƙasar Ivory Coast - ko kuma Cote d'ivore - da ke Afirka ta Yamma, doka ta tanadi cewa mafi ƙanƙantar albashi zai kama cfa75,000 - kwatankwacin naira 167,978 (ko kuma dala $122.35).
Wannan adadin ma ya ninka na Najeriya kusan sau shida.
Haka ma lamarin yake a Senegal - ƙawa kuma mamba tare da Najeriya a ƙungiyar Ecowas. Ƙananan ma'aikata kan karɓi cfa70,000 - kusan naira 156,780 ke nan (ko dala $114.19). Adadin ya kai kusan ninki shida a kan na Najeriya.
Ya abin yake a Nijar da Kamaru?
A ƙasa mafi maƙwabtaka da Najeriya ma wato Nijar, lalitar ƙananan ma'aikata ta fi cika idan aka kwatanta da babbar maƙwabciyar tata.
Mafi ƙarancin albashi a Nijar ya kai cfa30,000, kwatankwacin naira 67,191 - ko kuma dalar Amurka $48.94 - aƙalla ninki biyu kenan na albashin Najeriya.
A Kamaru kuma, doka ta tsara mafi ƙanƙantar albashin kan cfa43,969, abin da ya kai kusan N98,478 - kwatankwacin dala $71.73. Adadin ya zarta ninki uku idan aka kwatanta da na Najeriya.
Ƙasashe 11 da mafi ƙarancin albashinsu:
- Nijar cfa30000 = $48.94
- Senegal cfa70,000 = $114.19
- Ivory Coast cfa75,000 = $122.35
- Gabon cfa150,000 = $244.70
- Kamaru cfa43,969 = $71.73
- Kenya Sh15,202.00 = $114.69
- Uganda USh130,000 = $ 34.21
- Tanzaniya TZS150,000 = $57.89
- Rwanda RF29,000 = $22.46
- Somaliya SOS39,600 = $28.92
- Habasha ETB1,150 = $19.86
- Afirka ta Kudu 4,405.80 = $235.98
Ƙarin albashi ko daƙile hauhawar farashi?
Dakta Bashir Muhammed Achida malami ne a Sashen Tattalin Arziki na Jami'ar Usmanu Ɗanfodio da ke Sokoto kuma yana ganin ƙarin mafi ƙarancin albashi ba shi ba ne mafita daga matsalar tsadar rayuwar da ake fuskanta.
"Yana iya yiwuwa a buga kuɗaɗen, amma babu daraja. Yanayin zai iya zama sai ka kashe kuɗaɗe masu yawa wajen sayen abu ƙalilan," in ji shi cikin wata hira da BBC a kwanakin baya.
Ya buga misali da gwamnatocin da suka wuce daga ta Obasanjo zuwa Jonathan, da Buhari, dukkansu sun yi ƙarin albashi mafi ƙaranci, amma zuwa yanzu ma'aikaci na cikin wani hali.
Haka kuma akwai buƙatar ƙungiyoyin ƙwadago su zauna da gwamnati domin neman mafita ba wai batun samar da albashi mafi ƙaranci ba, a cewar masanin.
"Kamata ya yi bangaorin biyu su duba matakai da za su taimaka wajen magance tashin farashin kayayyaki ta yadda ma'aikaci zai iya tafiyar da rayuwarsa cikin sauƙi."
Abubuwa uku da ya ce suke lashe kaso mafi tsoka na albashi su ne: ilimi da lafiya da kuma abinci, "waɗanda idan gwamnati ta samar da su cikin sauƙi rayuwar ma'aikaci za ta inganta".