Najeriya: An kai ruwa rana kafin cimma ₦30,000 mafi karancin albashi

    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Bayan jan-kafa daga bangaren gwamnatin tarayya, a ranar Alhamis 18 ga watan Afrilu Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa dokar karin mafi karancin albashi a Najeriya hannu bayan shekara biyar da ya kamata a duba dokar.

Hakan yana nufin daga waccen rana karamin ma'aikaci a Najeirya ba zai karbi wani albashi ba kasa da naira dubu 30,000 kamar yadda kudirin dokar ya tanada.

Sai dai kafin a kawo wannan gabar an sha fama a baya da barazana da yajin aiki iri-iri daga kungiyoyin kwadago, duka don neman a kara wa ma'aikaci mai karamin mataki albashin da a yanzu wasu ke ganin tasirinsa kadan ne.

Tanadin dokar

Jim kadan bayan shugaban kasa ya sanya wa dokar hannu ranar 18 ga watan Afrilu, Ita Enang mai taimaka wa shugaban kan harkokin majalisa ya shaida wa manema labarai cewa dokar ta shafi kowace ma'aikata mai dauke da ma'aikata sama da mutum 25.

Da aka tambaye shi ko yaushe ne dokar za ta fara aiki?

Sai ya ce: "Ai yau ne (Alhamis, 18 ga watan Afrilu) ya kamata ta fara saboda yau shugaban kasa ya saka hannu. Sai dai akwai 'yan matakan da ya dace a bi daya bayan daya kamar yadda dokar ta tanada."

Ya kuma ce sabon tsarin albashin ya shafi dalibai masu yi wa kasa hidima wato NYSC, wadanda ake bai wa N19,800 a matsayin alawus duk wata.

Har wa yau, ma'aikaci zai iya yin karar wanda ya dauke shi aiki a kotu domin neman hakkinsa muddin aka gaza biyansa naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Da me aka fara?

An rabbata wa dokar albashi mafi karanci ta farko hannu a Najeriya a shekarar 1981 kuma tsohon Shugaban Kasa Shehu Shagari ne ya sanya mata hannun bayan wata yarjejeniya tsakanin gwamnati da kungiyar kwadago karkashin jagorancin Hassan Sunmonu.

Dokar a wancen lokacin ta tanadi naira 125 ne a matsayin albashi mafi karanci ga ma'aikata.

Tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Shehu Shagari a shekarar 1983, ba a sake yin wata doka ba game da mafi karancin albashin, sai a shekarar 2004 inda gwamantin tarayya karkashin mulkin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo ta kaddamar da ita a matsayin doka.

Dokar a wancen lokaci ta tanadi naira 5,500 a matsayin albashi mafi karanci.

A shekarar 2011 ne aka yi wa dokar kwaskwarima, wadda ta tanadi N18,000 ga ma'aikatan tare da kirkirar wani gurbi da ya ce ya kamata a rika dubawa tare da yin kwaskwarima ga dokar duk bayan shekara biyar.

An yi yarjejeniyar ne tsakanin kungiyar kwadago karkashin jagorancin Abdulwahid Umar da kuma gwamnatin tarayya karkashin mulkin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, wanda shi kuma ya sanya mata hannu shekara guda bayan haka.

Ta yaya aka cimma ₦30,000?

Jim kadan bayan zabensa a matsayin shugaban kasa a shekarar 2015, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa ma'aikatan kasar alkwarin duba dokar karamin albashi, wadda dama take daf da shiga lokacin da aka ayyana na sake duba ta.

Yayin da 'yan kwadago suke jiran shugaban ya cika alkawarinsa, sai kawai suka ji cewa gwamanti ta cire tallafin man fetur tare da kara farashin man daga ₦87 zuwa ₦145.

Wannan ta sa kungiyoyin kwadago na NLCda TUC da takwarorinsu suka fara matsa wa gwamnati lamba domin ta duba dokar ko a samu karin albashi, ganin yadda aka samu hauhawar farashin kayayyaki saboda tashin farashin man fetur.

Kungiyoyin sun bukaci da ₦56,000 a matsayin sabon albashin mafi karanci maimakon ₦18,000 da ake biya a lokacin.

Har sai a ranar 2 ga watan Nuwamban 2017 Ministan Kwadago Chris Ngige ya bayyana cewa ya sahhale sunayen wasu mutane a matsyin 'yan kwamitin da zai samar da sabon albashin mafi karanci.

Bayan matsin lamba daga 'yan kwadago, an kaddamar da kwamitin a ranar 27 ga Nuwamban 2017 karkashin jagorancin tsohuwar shugabar ma'aikata ta tarayya Misis Ama Pepple, wanda zai yi aiki da rahoton wani karamin kwamiti da aka kafa kafinsa.

Bayan fara tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, gwamnati ta yi nasarar shawo kan 'yan kwadagon, inda suka sassauta bukatarsu daga ₦56,000 zuwa ₦30,000.

Daga baya kuma 'yan kwadagon suka zargi gwamnatin da kin mayar da hankali, inda suka tafi yajin aiki a ranar 27 ga watan Satumbar 2018.

An jingine yajin aikin ne bayan da gwamnati ta bayyana cewa za ta ci gaba da aiki kan batun.

Jadawalin abubuwan da suka faru daga Oktoba zuwa Nuwamban 2018

  • 30 ga Oktoba gwamnonin kasar suka yi tayin biyan ₦22,000
  • 31 ga Oktoba kungiyar kwadago ta yi watsi da shi kuma ta yi barazanar shiga yajin aiki daga 6 ga Nuwamba
  • 6 ga Nuwamba aka sanar da cimma yarjejeniya tsakanin kwamitin gwamnati da 'yan kwadago
  • 6 ga Nuwamba 'yan kwadago suka dakatar da yajin aikin da suka shirya farawa kuma shugaban kasa ya karbi rahoton kwamitin

Nawa aka amince da shi tsakanin bangarorin?

Ana tsaka da sabatta-juyatta, sai ga wata sabuwa ta kunno kai kan hakikanin adadin albashin da aka kayyade tsakanin kungiyar kwadago da kuma kwamitin da gwamnati ta kafa domin samar da sabuwar alkibla ga kananan ma'aikata a Najeriya.

Shugabar kwamitin ta ce dama can suna aiki ne da adadi guda biyu: ₦24, 000 wanda gwamnati ta yi tayin biya, da kuma ₦30,000 da 'yan kwadago suke nema.

Ita kuwa kungiyar kwadago cewa take ₦30,000 ne aka cimma kuma a kan haka ne ta janye yajin aikin da ta yi niyyar farawa.

"Babu takaddama, mun gama mun kuma mika rahoton. Sai dai mun jaddada cewa lallai sai an janye yajin aiki. Har yanzu dai farashi biyu muka nazarta: ₦24,000 da ₦30,000," kamar yadda aka ruwaito Misis Pepple tana cewa.

Sai dai 'yan kwadagon sun hakikance cewa ₦30,000 ne aka amince kafin su janye yajin aikin.

A gefe guda kuma, kungiyar gwamnonin kasar ta fito ta ce ba ta san zance ba, domin babu ita aka yi waccen yarjejeniyar saboda haka ₦22,000 za su iya biya.

A wata sanarwar bayan taro a ranar 14 ga watan Nuwamban 2018, gwamnan jihar Zamfara kuma shugaban kungiyar gwamnonin ta NGF Abdulaziz Yari, ya ce indai ana so su biya ₦30,000 to fa, sai dai su rage yawan ma'aikata.

Kungiyar kwadagon ba ta yi wata-wata ba ta yi Allah-wadai da furucin nasu kuma ta ce ba za ta yarda da wani adadi ba kasa da dubu 30,000 kamar yadda kwamitin ya bayar da shawara.

Ta kuma sanya Disamba a matsayin wa'adi ga gwamnati da ta fara aiwatar da sabon tsarin ko kuma ta dauki matakin yajin aiki.

Ko gaskiya gwamnonin ke fadi?

A ranar 2 ga watan Fabarairun 2018 jaridar Daily Trust ta ruwaito kungiyar malaman makaranta ta kasa NUT na cewa jihohi 13 a Najeriya ba su biya albashin malaman ba, ciki har da wadanda suka shafe wata 28, ba tare da albashin ba.

Bugu da kari, yayin da ake daf da yin babban zaben 2019 Shugaba Buhari ya yi wa masu jefa kuri'a gargadi a wata kafar yada labarai da cewa kada su zabi gwamnonin da suka gaza biyan albashin ma'aikatan jihohinsu.

Duk wannan yana faruwa ne kafin a kara yawan albashin mafi karanci daga ₦18,000 zuwa ₦30,000.

Me ya jawo jan-kafa?

Shekara 10 aka shafe kafin gwamnati ta kara yawan mafi karancin albashin a Najeriya.

Babu mamaki hakan ya faru ne saboda babu wata doka a kundin tsarin mulki da ke tilasta wa gwamnati kan kara yawan albashin ma'aikata.

Wannan dalilin ne ya sa wakili daga jihar Legas a Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya kaddamar da wani kudiri a gaban majalisar a watan Mayun 2017 yana neman a yi dokar da za ta tilasta wa gwamnati kan mafi karamin albashin.

Gbajabiamila ya fada wa zauren majalisar cewa sashe na 173 na kundin tsarin mulki ya tanadi a rika duba fansho duk bayan shekara biyar, amma bai tilasta hakan ba ga albashin ma'aikata.