Gaske ne matatar Ɗangote ta kori ma'aikatanta fiye da 1000?

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Rahotanni sun nuna cewa kamfanin na Dangote ya sallami ma'aikatansa fiye da guda 1000 bisa zargin shiga ƙungiyar ma'aikatan kamfanonin mai da iskar gas ta Najeriya, PENGASSAN.

Bayanai da BBC ta samu daga wasu ma'aikatan kamfanin na Ɗangote sun nuna cewa kamfanin ya kore su ne saboda sun ce za su shiga ƙungiyar.

Sai dai kamfanin na Ɗangote a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a ya musanta dalilin da suka bayar inda ya ce ya yi korar ne bisa tuhumar ayyukan zagon ƙasa.

Sanarwar ta ƙara da cewa har yanzu akwai ma'aikata fiye da 3,000 da ke ayyukansu a kamfanin.

'Na kasa barci ko cin abinci'

Wata ma'aikaciyar kamfanin man na Ɗangote wadda korar ma'aikatan ya shafa ta shaida wa BBC yadda ta ji bayan da aka sanar da su cewa an sallame su duk da cewa har lokacin da ta yi magana da BBC ba a ba su takardar sallama.

"Tun da aka sanar da mu batun dakatarwar a jiya (Alhamis), a lokacin da ta fara aiki, na kasa faɗa wa mamanmu.

"Na kira ƙanwata cewa ta kira ta faɗa wa mamanmu. Ina ta tunani me zan yi kenan, daga ina zan fara, abu ne wanda ya zo mana kwatsam, ba zato ba tsammani. Na kasa barci ko cin abinci ma sai a hankali.

"Sun ce sun kore mu ne saboda mun shiga ƙugiyar PEGASSAN. Sanarwar da kamfanin Ɗangote ya fitar da ke cewa wajen ma'aikata 3000 za su ci gaba da aiki, kuma wai suna yi wa kamfanin garambawul ne ƙarya ne kawai suna son samun tausayin al'umma ne, kuma babu maganar ko za a biya nu kuɗin sallama."

'Yadda kamfanin Ɗangote ya yi mana tarko'

..

Asalin hoton, Getty Images

Shi ma wani matashin wanda ya yi digirinsa a Mechanical Engineering daga jami'ar Ahmadu Bello University da ke Zaria wanda kuma ya fita da sakamako mai kyau.

"Zancen cewa wai sun kore mu ne saboda muna yi wa kamfanin zagon ƙasa ƙarya ne saboda idan ka yi zagon ƙasa to ai abin kanka zai koma. Misali, idan ka haddasa wuta ta tashi, ba kai ne za ka fara ƙonewa ba?

"Kawai dai hukumar matatar ba ta so su mu shiga ƙungiyar Pengassan ne. Bayan mun yi yunƙurin shiga ƙungiyar, sai aka kawo musu takarda a kamfanin cewa su zaɓi ko dai za su shiga ƙungiyar ko a'a, da suka ce za su shiga, sai kawai muka ga sako cewa za a sallame mu saboda zargin mu da yunƙurin cin dunduniyar matatar." In ji ma'aikacin.

Sai dai ya ce sun gana da ƙungiyar ta PENGASSAN, inda ta ce musu tana kokari kan lamarin kuma za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an bi musu haƙƙinsu.

Waɗanne ma'aikata aka sallama?

..

Asalin hoton, Getty Images

Wata majiya daga matatar ta ce mafi yawancin mutanen da kamfanin ya sallama wadanda suka shiga ma'aikatar ne a matsayin ma'aikata masu neman horo wato trainee, da aka zaɓo daga jami'a, inda suka zama ma'aikatan matatar.

"Yawancin ma'aikatan sun fara aiki ne a kamfanin tun daga fitowarsu daga jami'a. Mafi yawancinsu su ne ɗaliban da suka yi fice wato suka fita da sakamako wanda ya fi na kowa." In ji wani ma'aikacin da bai so a ambaci sunansa ba.

Sai dai kuma a sanarwar da kamfanin na Ɗangote ya fitar, al'amarin ya shafi masu son yi wa kamfanin zagon ƙasa ne kawai.

Mece ce PENGASSAN?

PENGASSAN ita ce ƙungiyar manyan ma'aikatan mai da iskar gas a Najeriya da ke kare muradun masu aiki a kamfanonin mai.

Galibin mambobin ƙungiyar suna aiki ne da kamfanonin hako ɗanyen man fetur a tudu.

Yana daga cikin hakkin ƙungiyar tabbatar da mambobinta suna samun dukkan abubuwan da ya kamata a wurin aiki kamar lafiya da tsaro da albashi mai kyau da dai sauransu.

A shekarar 1979 ne aka kafa ƙungiyar ta PENGASSAN.