Gwamnatin Najeriya ta musanta daina sayar wa Dangote ɗanyen man fetur da naira

Aliko Dangote

Asalin hoton, X/Dangote Refinery

Lokacin karatu: Minti 3

Bayan wasu rahotanni da suka karaɗe jaridun ƙasar, gwamnatin Najeriya ta yi ƙarin haske kan abin da ya shafi batun sayar wa matatar man fetur ta Dangote ɗanyen man fetur.

Raɗe-radin sun taso ne bayan da aka shiga watan ƙarshe na wa'adin wata shida da aka ɗiba na sayar wa matatar ta Dangote, mai ƙarfin tace lita ɗanyen man fetur 650,000 a rana, na sayar mata da ɗanyen man fetur na ƙasar cikin kuɗin naira.

Yarjejeniyar ta fara aiki ne a watan Oktoban 2024, lokacin da matatar Dangote ta koka kan shan wahala wajen samun ɗanye man fetur.

Lamarin ya haifar da zazzafar muhawara, musamman bayan taƙaddamar da aka samu tsakani kamfanin mai na Najeriya (NNPC) da matatar bayan fara aikinta.

Yayin da ake cikin watan ƙarshe, wasu jaridu sun ruwaito cewa tsarin zai ƙare ne ba tare da an tsawaita shi ba.

Sai dai a cikin wata sanarwa da ta samu sa hannun shugaban ƙaramin kwamitin kula da sayar wa mamatun man fetur ta hanyar amfani da takardar naira, Zacch Adedeii, ya ce ba tun ba haka ya ke ba.

Ya tsarin ke aiki?

A cewar sanarwar "tsarin da ya sayar da ɗanyen man fetur ta hanyar amfani da naira ga matatun man fetur na cikin gida na ci gaba da aiki.

"Babu wata matsaya da aka cimma kan batun dakatar da tsarin kuma ba a tunanin yin hakan. Bayan gudanar da tsarin na wasu watanni, an gano cewa wannan hanya ita ce ta fi dacewa, kuma zai ci gaba da taimakawa wa tattalin arziƙi."

Tsarin, wanda ya aka samar domin kawar da wahlahalun da matatun man fetur na cikin gida ke samu wajen samun ɗanyen man fetur, ya bai wa irin waɗannan matatu damar sayen ɗanyen man fetur daga NNPC ta amfani da takardar kuɗi ta naira a maimakon dalar Amurka.

A ƙarƙashin tsarin, NNPC ya ce ya samar da ɗanyen man fetur ganga miliyan 48 ga matatar man fetur ta Dangote.

Duk da cewa tsarin ya ƙunshi wasu ƙananan matatun man fetur guda bakwai, amma bayanai sun nuna cewa matatar man Dangote ce kawai ta ci gajiya.

Sai dai bayanin da kwamitin ya fitar ya ce: "Ba a tsame matatun man fetur na cikin gida daga tsarin ba, sai dai ya dogara ne a kan samuwar ɗanyen man fetur ɗin da kuma halin kasuwa.".

Saɓanin da matatar Dangote ta samu da NNPC a baya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Akwai yarjejeniya tsakanin matatar Dangote da kamfanin NNPC tun kafin soma aikin matatar, amma matatar Dangote ta ce kashi bakwai kawai kamfanin ya biya na hannun jari kafin cikar wa'adin yarjejeniyar maimakon kashi 20.

Matatar man Dangote ta ce tana fatan samar da gangar mai 550,000 a bana, amma kuma kamfanin Dangote ya ce dole sai ya nemi wasu hanyoyin samun ɗanyen mai daga ƙasashen waje saboda rashin wadatarsa a cikin gida.

Matatar ta ce jirgin ruwa biyar na ɗanyen man fetur kawai ta samu tun fara aikinta daga kamfanin NNPCL, maimakon 15 da ta yi tsammani.

Matatar Dangote kuma ta yi zargin cewa ana shigo da gurɓataccen mai a Najeriya.

Wannan ne ya sa kamfanin mai na ƙasar ya mayar da martani kan dalilin ƙaurace wa bai wa matatar isasshen ɗanyen mai:

NNPCL ya ce sinadarin sulfur ya yi yawa a ɓangaren man dizel da matatar Ɗangote ke samarwa.

A makon da ya gabata shugaban hukumar kula harkar man fetur ta Najeriya (NMDPRA) Farouk Ahmed, ya faɗa wa taron manema labarai cewa "man fetur ɗin matatar Dangote bai kai ingancin wanda ake shigowa da shi ba".

Sai dai a martaninta, matatar Dangote ta ce an samu matsalar sinadarin sulfur mai yawa ne lokacin da ta fara aiki a farkon shekarar nan, amma yanzu an rage sinadarin da kuma zai ci gaba da raguwa yayin da aiki ke ci gaba da tafiya.

Matatar ta ce yanzu ta daidaita sinadarin na sulfur da ke inganta mai daga wari ko nauyi, kamar yadda kamfanin Dangote ya bayyana cikin wata sanarwa bayan ziyarar da kwamitin harakokin man fetur na Majalisar wakilan tarayya ya kai a matatar a ƙarshen mako.

Matatar Dangote ta kuma ce tana tattaunawa da ƙasashen Libya da Angola domin samo ɗanyen mai bayan rashin samun wadatarsa a Najeriya, ƙasar da ta fi arziƙin mai a Afirka.