Dalilai huɗu da suka sa Dangote ya rage farashin man fetur

Matatar mai ta Dangote

Asalin hoton, Dangote Refinery

Bayanan hoto, A watan Oktoban 2024 matatar mai ta Dangote ta fara sayar wa 'yankasuwa kaya kai-tsaye
    • Marubuci, Daga Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Kasuwar man fetur a Najeriya na ci gaba da fuskantar sauyi musamman a ɓangaren farashinsa tun bayan da gwamnatin Bola Tinubu ta cire tallafi a shekarar 2023.

Sauyi na baya-bayan nan da masu sayen fetur ɗin ke gani shi ne yadda matatar fetur ta Dangote ke rage farashin man zuwa mafi araha tun bayan da ta fara aiki a shekarar da ta gabata.

A ranar Laraba ne kamfanin Dangote ya sanar da rage wa dillalai abokan hulɗarsa farashin litar man zuwa N825 daga N890, ragin naira 65 kenan.

Karo na biyu kenan kamfanin yana rage farashin man a watan Fabrairun 2025, abin da dillalan man suka bayyana da "abin a yaba".

Janye tallafin man da gwamnatin Najeriya ta yi a watan Mayun 2023 ya sa farashinsa ya tashi daga ƙasa da N200 har zuwa sama da N1,000, kafin ya ragu zuwa ƙasa da haka a Legas da Abuja.

Rage farashin ya sa man na Dangote ya zama mafi araha idan aka kwatanta da wanda ake shiga da shi ƙasar daga ƙasashen waje.

Sabuwar dokar man fetur ta Petroleum Industry Act (PIA) da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya saka wa hannu a 2022 ta sauya harkokin mai a ƙasar, ciki har da sayar wa matatun cikin gida ɗanyen mai domin tacewa da kuma sayarwa a naira maimakon dalar Amurka.

Farashin man Dangote a gidajen mai

Gidan mai

Asalin hoton, Reuters

Tun bayan fara sayar wa 'yankasuwa mai kai-tsaye a watan Oktoban 2024, matatar Dangote ta shigo kasuwar fetur gadan-gadan a Najeriya.

Fara sayar wa 'yankasuwa man na zuwa ne bayan kamfanin mai na gwamnatin Najeriya ya sanar da zare hannunsa a matsayin mai shiga tsakanin matatar da 'yankasuwa, inda shi ma ya zama dillali mai zaman kansa.

Matatar ta fara rage farashi ne a daidai lokacin hutu na watan Disamban 2024, inda ta rage naira 70.50 - daga N970 zuwa N899.50.

Shi ma kamfanin mai na NNPC ya rage nasa farashin zuwa daidai da na Dangote; daga N1,020 zuwa N899.

Sai kuma a ranar 1 ga watan Fabrairu, inda da ta bayar da sanarwar rage farashin da naira 60.00 zuwa N950 kan kowace lita ɗaya.

Kamfanonin da ke safarar tataccen mai daga ƙasashen waje zuwa Najeriya kan yi hakan a kan naira N927, bambancin naira 102 kenan.

Sanarwar rage farashin da matatar Dangote ta bayar a yanzu ta zayyana yadda dillalanta za su sayar a gidajen man su kamar haka:

  • MRS: N860 - a Legas
  • AP: N865 - a Legas
  • Heyden: N865 - a Legas
  • MRS: N870 - a kudu maso yammacin Najeriya
  • AP: N875 - a kudu maso yammacin Najeriya
  • Heyden: N875 - a kudu maso yammacin Najeriya
  • MRS: N880 - a arewacin Najeriya
  • AP: N885 - a arewacin Najeriya
  • Heyden: N885 - a arewacin Najeriya
  • MRS: N890 - a kudu maso kudu da kudu maso gabashin Najeriya
  • AP: N895 - a kudu maso kudu da kudu maso gabashin Najeriya
  • Heyden: N895 - a kudu maso kudu da kudu maso gabashin Najeriya

Dalilan da suka jawo rage farashin

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Duk shikashika da za su jawo rage farashin man fetur an cika su a yanzu," kamar yadda Farfesa Ahmed Adamu - masanin tattalin arzikin man fetur a jami'ar Nile University da ke Abuja - ya shaida wa BBC.

Gasa

Tun bayan sauye-sauyen da aka samu a kasuwar hada-hadar man fetur ta Najeriya, aka fara samun gasa tsakanin masu shigo da man da kuma matatar Dangote.

Wannan gasa na ɗaya daga cikin dalilan da suka jawo raguwar farashin, ko kuma sanadiyyar hana farashin ya ƙaru.

"Da ma amfanin gasa kenan. Shi Dangote yana ganin yanzu yana yin takara ne da wasu matatun man fetur ɗin na duniya, kuma babban burinsa shi ne ya riga kowa sayarwa," in ji Farfesa Ahmed.

"Da zai yiwu ma, zai so ya haddasa yadda za a yi wasu 'yankasuwar ma su ji ba za su iya ci gaba da harkar ba, ta yadda duk masu sari za su tsallake kowace matata su saya a wajensa.

"Shi ya sa ma shi kansa kamfanin NNPC yakan sayi man a wajen Dangote, duk da cewa yana shigo da man daga waje."

Ɗaya daga cikin sharuɗɗan kasuwanci tsakanin Dangote da 'yankasuwa shi ne dole ne dillali ya sayi abin da bai gaza lita miliyan biyu ba, kuma babu mamaki wannan ne ya sa ƙananan 'yankasuwa ba su iya sayen man nasa.

Farfaɗowar darajar naira

'Yar farfaɗowar da darajar kuɗin naira ya yi na daga cikin abubuwan da ka iya jawo raguwar man fetur ɗin na Dangote.

Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa an fara ganin raguwar darajar dalar ne tun daga farkon watan Fabrairu a hukumance da kuma kasuwannin bayan fage a Najeriya.

"Harkar canjin kuɗin ƙasashen ƙetare na cikin manyan abubuwan da suka fi shafar farashin man fetur," a cewar Farfesa Ahmed Adamu.

Dalili a nan shi ne, gwamnatin Najeriya na sayar wa matatar ta Dangote ɗanyen man fetur a naira maimakon dalar Amurka.

"Ba wai sauƙi aka yi masa ba, farashin ɗanyen fetur ɗin ake aunawa a kasuwar duniya, sai a canza shi zuwa naira, shi kuma Dangote ya biya da nairar," kamar yadda Farfesa Ahmed Adamu ya yi bayani.

"Hakan na nufin nairar da Dangote zai biya wajen sayen ɗanyen man ta ragu, wanda zai sa shi kuma ya rage farashin da yake bai wa masu sari."

Karyewar farashin ɗanyen mai

Wani dalilin shi ne na karyewar darajar ɗanyen man fetur a kasuwar duniya.

Bayanai sun nuna cewa samfurin Brent da Najeriya ta fi amfani da shi kuma take jingina farashi a kansa ya karye zuwa dala 73.92 kan kowace ganga ɗaya daga 74.29 a makon da ya wuce.

"Tun da aka shigo wannan shekara bai taɓa yin ƙasa ba kamar yanzu. A watan Janairu ya kai kusan dala 81," in ji Farfesa Ahmed.

"Da a ce mutum ɗaya ne a kasuwar, babu gasa, sai ya yi shuru kawai ya ci gaba da cin kasuwarsa yadda yake so."

Azumin Ramadana

A nata ɓangaren, matatar mai ta Dangote ta ce ɗaya daga cikin dalilan da suka sa ta rage farashin man har da shirin da al'ummar Musulmi ke yi na fara ibadar azumin watan Ramadana.

Ana sa ran za a fara azumin a ranar Asabar ko Lahadi, inda Musulami kan shafe tsawon wuni babu ci babu sha tsawon kwana 29 ko 30 a jere.

"An ɗauki matakin ragewar ne domin sauƙaka wa 'yan Najeriya saboda shirin fara azumin Ramadana, da kuma tallafa wa gwamnatin Tinubu game da tsarinta na farfaɗo da tattalin arziki...," a cewar sanarwar da ta fitar ranar Laraba.