Rashin sayen mai daga wurina ne ya jawo ƙarancinsa a Najeriya - Ɗangote

..

Asalin hoton, X/DANGOTE

Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Aliko Dangote, ya ɗora alhakin ƙarancin man fetur da ake samu a Najeriya kan dillalan man da ya ce ba su saya daga gare shi.

Dangote ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da kwamitin shugaban ƙasa kan sayar da ɗanyen man fetur a naira ga kamfaninsa.

Hamsahƙin attajirin ya ce rashin sayen man a wurinsa ne ya sa ake samun dogayen layuka a gidajen man Najeriya.

"Ina so NNPCL da sauran dillalan mai su daina shigo da man fetur, su zo wajenmu su saya. Amma idan suka zo suka saya man a matatarmu, za a daina ƙarancin man da ma dogon layi a gidajen mai." In ji Ɗangote.

To sai dai ya ce bai san dalilin da ya sa suka ƙaurace sayen man daga wurinsa.

"Shugaban ƙasa ya amince kuma mun shiga yarjejeniya da masu gidajen man. Amma ban san me ya sa ba sa zuwa su saya daga wurinmu. Mun ce musu ma su zo su saya a irin farashin da NNPC ke sayar musu"

Ya ƙara da cewa a shirye matatarsu take ta samar da lita miliyan 30 ga ƴan Najeriya.

"Mun ƙiyasta cewa Najeriya na buƙatar lita miliyan 30 zuwa 32 a kullum. Wannan ba matsala ba ce saboda yanzu haka muna da lita miliyan 500 a tankinmu, wanda ke nufin ko ba mu tace wani man ba, muna da man da zai wadatar da Najeriya na sama da kwana 12," in ji Ɗangote.

A shirye muke mu sayi mai daga Ɗangote kai tsaye - IPMAN

A wani abu mai kama da kwangaba-kwanbaya, shugaban ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya, IPMAN, ta ce idan dai har Ɗangote a shirye yake ya sayar musu da man kamfanin nasa kai tsaye to su ma a shirye suke su saya.

"Akwai kuɗaɗenmu fiye da naira biliyan 40 da muke bin NNPCL. Na yi mamaki lokacin da na ji Dangote ya ce yana da litar mai fiye da miliyan 500. A shirye muke mu sayi man daga Ɗangote idan shi ma ya shirya sayar mana kai tsaye." In ji Abubakar Garima, shugaban ƙungiyar IPMAN ta Najeriya a wata hira da shirin gidan talbijin na Channels mai suna "Sunrise Day" ranar Laraba.

Wannan dai na zuwa ne ƙasa da makwanni uku bayan kamfanin NNPCL ya ce ya zare hannunsa a matsayin mai shiga tsakanin 'yankasuwa da Dangote bayan yarjejeniyar da suka ƙulla tun a watan Agusta.

Yarjejeniyar ta ƙunshi cewa NNPCL ne kaɗai zai dinga sayen man Dangote, inda su kuma 'yankasuwa za su saya a hannun kamfanin.

Ƙasashen duniya za su fara sayan manmu - Ɗangote

Hamshaƙin attajirin na Afirka ya nuna cewa tuni sun shiga yarjejeniya da wasu ƙasashen duniya domin fara jigilar man daga kamfanin na Ɗangote.

"Akwai Angola da Saudi Aramco amma wani wurin za su kai. Mun yi magana da su da Ghana da Angola. Akwai ƙasashe da yawa da yake sun nuna buƙatar za su yi. Wannan zai zama wani abin tarihi a Afirka domin ba taɓa yi ba. Ƙasashe biyu ne kawai suke yi Libya da Algeria. Idan ban da su dukkannin sauran ƙasashen shigar da mai suke yi ƙasarsu."

Wannan dai na zuwa ne ƙasa da wata ɗaya bayan da gwamnatin Najeriya ta fara aiwatar da sayar da ɗanyen mai da kuɗin gida wato naira maimakon dalar Amurka kamfanin na Ɗangote.

Gwamnatin dai ta ce ta yi hakan ne na manufar daidaita farashin man fetur da kuma ɗaga darajar naira a ƙasar.