Yadda tsadar man fetur ke tilasta mutane yin tafiyar ƙafa

Wasu mazauna Kano
Bayanan hoto, Mutane da dama sun ce sun gwammace su yi tafiyar ƙafa saboda tsadar kuɗin mota
Lokacin karatu: Minti 2

Ƙarin farashin man fetur da aka yi a Najeriya ranar Laraba ya ƙara jawo guna-guni daga fasinjoji, da direbobi waɗanda ke cewa da ma can ba wata ribar kirki suke samu ba kafin yanzu.

Yanzu kamfanin mai na Najeriya NNPCL kan sayar da kowace lita ɗaya kan naira 1,030 a Abuja babban birnin ƙasar, yayin da ya zarta hakan a gidajen mai na 'yankasuwa. Kazalika, tun kafin ƙarin na yanzu mazauna jihohin arewaci da gabashin ƙasar ke sayen sa kan sama da N1,000.

Ƙarin na kimanin kaso 15, shi ne na biyu a cikin wata ɗaya, kuma ya zo ne ne bayan bayanan da suka nuna NNPCL ya zare hannunsa daga dillancin fetur tsakanin matatar mai ta Ɗangote da 'yankasuwa.

Matakin na nufin kamfanin ya daina cikasa giɓin N133 (a matsayin tallafi) da ake samu idan ya sayi man daga Dangote kan N897. Sannan yanzu 'yankasuwa za su dinga sayen man kai-tsaye daga Dangote.

Gwamnatin Najeriya ta bakin ministan yaɗa labarai ta ce babu hannunta a ƙarin kuɗin man fetur, yayin da Shugaba Bola Tinubu ya kare ƙarin da aka yi a watan Satumba da cewa "ya zama dole" saboda a "samu kuɗin gina ƙasa".

'A ƙafa na je kasuwa yau'

Wasu mazauna Kano - birni mafi girma a arewacin ƙasar sun bayyana yadda ƙarin ya ƙara jefa su cikin halin matsi.

Wani ɗankasuwa ya ce tsadar kuɗin mota ta sa ya yi tafiyar kusan kilomita 10 a ƙafa zuwa kasuwa ranar Alhamis.

"Ina kashe N1,200 daga gidana zuwa kasuwa, amma yau a ƙafa na zo tun daga Rijiyar Zaki zuwa Kasuwar Kurmi," kamar yadda magidancin ya shaida wa wakilin BBC a Kano Zahraddeen Lawan.

"Gaskiya an shiga wani hali na takura, ya kamata shugabanninmu su duba halin da talakawa ke ciki, su nema mana sassauci," a cewarsa.

Ita ma wata ɗaliba ta bayyana cewa kuɗin da ke hannunta N2,000 bai zama lallai su kai ta inda za ta je ba kuma ta riga ta fito titi.

"Daga Mandawari na hau zuwa nan amma wai N200, kuma yanzu motar Gwarmai zan hau. A baya a kan N1,000 nake zuwa amma yanzu sai ka ji ana cewa N2,000, kuma ni ɗaliba ce," a cewar ɗalibar da ba ta bayyana sunanta ba.

'Idan na ga babu riba ajiye motar zan yi'

Tun kafin ƙara farashin a yanzu mazauna jihohin Kano da Jigawa kan sayi litar mai kan sama da N1,000.

Amma a yanzu masu ababen hawa kan ce akan samu man a NNPCL kan N1,070, yayin da 'yankasuwa kan sayar a N1,050 zuwa N1,250.

"Gidajen mai da dama da na zagaya a Kano na gan su a kulle a ranar Alhamis, kuma bayanai na nuna cewa wasu na da man amma suka rufe," in ji wakilinmu Zahraddeen Lawan.

Bisa al'ada, kuɗin zirga-zirga na ƙaruwa nan take da zarar an ƙara farashin fetur ɗin, kuma a wannan karon direbobi ma sun koka cewa lamarin ya shafe su sosai.

Wani direban hayis (bas) a Kanon ya ce abubuwan dai sai addu'a kawai.

"Idan na kammala jigila a yau [Alhamis] na lissafa na ga babu riba zan duba yiwuwar ajiye motar kawai," kamar yadda direban ya shaida wa BBC.