Yaushe tsuguno zai ƙare dangane da farashin mai a Najeriya?

A ranar Laraba ne ƴan Najeriya suka wayi gari da sabon farashin mai na naira 1,030 a gidajen man NNPCL a da ke Abuja maimakon 897, inda a Legas kuma farashin ya koma 998 daga 885.
Duk da cewa cewa kamfanin na NNPCL bai faɗi dalilin ƙarin ba amma ana danganta shi da bayanan da suka nuna kamfanin ya zare hannunsa daga dillancin man kamfanin Ɗangote.
Zare hannun NNPCL daga dillanci dai na nufin kamfanin ya daina cikasa giɓin da ake samu ko kuma biyan tallafi na naira 133.
Tuni kuma gidajen mai na ƴankasuwa a Abuja suka ƙara farashin su ma inda yake farawa daga naira 1,040 zuwa sama.
A sauran jihohi kuwa musamman na arewacin Najeriya farashin man ya kan kai har har zuwa kusan naira 1,300, sannan kuma har yanzu akwai dogayen layukan ababan hawa a gidajen man.
Wannan ne dai ƙarin farashin mai na biyu a cikin wata ɗaya.
Hakan ne ya sa ƴan Najeriya ke tambayar ko wannan farashin shi ne na ƙarshe ko kuma haka za a yi ta tafiya duk wata ana samun ƙari? Sannan kuma ko cire tallafin da NNPCL ke bayarwa zai kawo ƙarshen dohayen layukan mai a Najeriya?
Yaushe farashin mai zai daina hauhawa?
"Ba a taɓa yin haka ba a duniya kuma ba za a fara daga Najeriya ba. Farashi ba zai daina tashi ba. Da ma shi cire tallafi ya gaji haka domin yanzu farashin zai dogara ne ga yadda kasuwa ta kama musamman ma farashin dala." In ji Dr Ahmed Adamu, malami a jami'ar Nile University kuma masanin harkar makamashi a Abuja Najeriya.
Dr Ahmed ya ƙara da cewa "duk kuwa da cewa yanzu gwamnati za ta rinƙa sayar wa da Ɗangote ɗanyen man a naira to amma ita kanta naira ɗin ai sai an canza dalar saboda darajar naira ta dogara ne ga dalar Amurka.
Saboda haka darajar naira ce abin dubawa. Idan naira ta karye to farashin mai dole ne ya tashi. Sannan akwai batun dakon man da kuma kai shi wuri mai nisa. Duka waɗannan abubuwan dubawa ne da za su iya haddasa hawa da saukar farashin na mai."
Ko akwai yiwuwar daina dogon layi a gidajen mai?

Bisa la'akari da yadda aka yi ta alƙawarta wa ƴan Najeriya cewa idan aka cire tallafi to mai zai wadata sannan kuma dogayen layuka a gidajen man za su zama tarihi, ya sa muka tambayi Dr Ahmed Adamu ko yaya al'amarin yake?
"Ba na tunanin idan aka tafi a haka za a daina samun dogayen layuka a gidajen mai saboda ai sayo man ma na masu kuɗi sosai ne. Hakan na nufin har yanzu bai zama lallai man ya zama a kwai shi a kowane gidan mai ba.
Sannan kasancewar farashi zai rinƙa banbanta daga wannan gidan man zuwa wancan zai sa mutane su rinƙa layi a inda suke tunanin man zai fi sauƙi da kuma kyawun lita." In ji Dr Ahmed Adamu.
Sai dai kuma masanin ya ce hanyar samun sauƙi daga tsadar man da kuma samun dagayen layi ita ce "idan gwamnati ta tabbatar da cewa ta saka ido a harkar yadda ƴankasuwa ba za su rinƙa tsawwala wa ƴan ƙasa ba."
Shawarwari biyu ga ƴan Najeriya

Asalin hoton, Ahmed Adamu/Facebook
Dr Ahmed Adamu ya ce bisa la'akari da cewa rayuwar ƴan Najeriya ta riga ta sauya ta yadda ba za a koma yanayin araha na man fetur ba, ya bai wa ƴan ƙasar shawarwari guda biyu domin samun sauƙin rayuwa:
- Sauya fasalin rayuwa : Zamanin da za a ce kowa sai ya mallaki motarsa ya riga ya wuce. Ya kamata a samar da hanyoyin sufuri domin amfanin ƴan ƙasa domin rage musu dogara ga amfani da man fetur.
- Amfani da iskar gas: Lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su rungumi iskar gas ɗin nan musamman bisa la'akari da cewa Najeriya ta fi kowacce ƙasa arziƙin iskar gas. Adadin iskar gas ɗin da Najeriya ke da shi ya ninka na fetur sau fiye da huɗu. Sai an samu sauyi na makamashi mai araha shi ne za a ce za a iya samun sauƙi da arahar makamashin.











