Taƙaddama ta ɓarke tsakanin Obasanjo da NNPCL kan gyaran matatun man fetur

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo da shugaban kamfanin man fetur na Najeriya, Kolo Mele Kyari

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

A farkon makon nan ne hukumomin Najeriya suka sanar da fara aikin matatar man fetur ta Warri da ke jihar Delta, bayan shafe kimanin shekara biyar ba ta aiki.

Ta dawo aiki ne bayan waɗansu gyare-gyare da aka yi mata, watanni kaɗan bayan tayar da matatar man fetur ta Najeriya da ke birnin Port Harcourt.

Lamarin da shugaban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL, Mele Kyari ya bayyana wa BBC cewa zai kawo sauƙi a ɓangarori da dama na harkar man fetur a ƙasar.

Hatta shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya fito ya taya kamfanin na NNPCL murnar wannan "nasara" da ya ce an samu.

Sai dai tun ba a je ko ina ba lamarin ya fara tayar da ƙura, lamarin da ya sanya ayar tambaya kan sahihancin sauyin da "nasarar" da NNPCL ya ce ya samu a gyarar matatun, zai haifar.

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ne ya furta wasu kalamai a tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels.

Lamarin bai yi wa kamfanin na NNPLC daɗi ba, abin da ya sa ya mayar wa tsohon shugaban martani, har ma ya miƙa masa goron gayyatar zuwa domin duba gyaran da aka yi wa matatar ta Warri.

Me Obasanjo ya ce?

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo

A tattaunawar, wadda kafar talabijin ta Channels ta wallafa a ranar Laraba, Obasanjo ya bayyana abubuwan da suka faru a lokacin da ya yi ƙoƙarin farfaɗo da matatun man fetur uku na ƙasar - ta Kaduna da Port Harcourt da kuma Warri - a lokacin da yake mulki.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya ce "na kira kamfanin Shell domin ya karɓi ragamar tafiyar da matatun man fetur ɗin Najeriya amma ya ƙi."

"Shugaban kamfanin a wancan lokacin ya ba ni hujjojinsu huɗu ko biyar game da dalilansu na ƙin karɓar tafiyar da matatun."

"Hujja ta ɗaya da ya ba ni ita ce: Su, sun fi samun riba ne a ɓangaren haƙo ɗanyen man fetur domin sayarwa ga masu sarrafawa (Upstream).

Hujja ta biyu biyu: Matatun man fetur ɗin mu sun yi ƙanƙanta da yawa, suna tace gangar man fetur 60,000 sai 100,000 sai kuma ina tunanin 120,000.

"Ya faɗa min a wancan lokacin cewa matsakaiciyar matatar man fetur takan tace gangar man fetur 250,000".

"Hujja ta uku: Ya faɗa min cewa ba a kula da matatun man fetur ɗinmu yadda ya kamata.

"Hujja ta huɗu: Ya faɗa min cewa rashawa ta yi yawa a harkar matatun man fetur ɗinmu, kuma ya ce min ba su son tsoma kansu cikin hakan.

"Me ya kamata ka yi idan mutum irin wannan ya faɗa maka haka?"

Obasanjo ya ce bayan hakan ne sai attajirin nan na Najeriya, Aliko Dangote ya kafa kwamitin wasu mutane da suka yi nazari kan lamarin, sannan a ƙarshe ya yanke shawarar tafiyar da matatun man fetur ɗin ƙarƙashin tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ɓangaren ƴan kasuwa.

"Sun biya kuɗi dala miliyan 750 domin yin haɗin gwiwa da gwamnati wajen tafiyar da matatun man fetur ɗin," in ji Obasanjo.

Sai dai tsohon shugaban ƙasar ya ce shugaban ƙasar da ya biyo baya ya mayar wa Dangote kuɗinsa.

Ya ƙara da cewa "na je wurin wanda ya gaje ni, na ce masa ka san yarjejeniyar da aka yi, sai ya ce min 'NNPC sun ce suna buƙatar a bar musu matatun, za su iya tafiyar da su'.

"Sai na ce masa 'amma ka san cewa ba za su iya tafiyar da su ba".

Obasanjo ya ƙara da cewa "na ji an ce an kashe dala biliyan biyu a baya-bayan nan kan matatun, amma duk da haka matatun ba za su yi aiki ba."

A ƙarshen bayanin nasa, Obasanjo ya ce "ramin ƙarya ƙurarre ne."

Martanin NNPCL

Jim kaɗan bayan bayyanar tattaunawar ta Olusegun Obasanjo da kafar talabijin ta Channels, kamfanin man fetur na NNPLC ya fitar da sanarwa, inda ya gayyaci tsohon shugaban ƙasar domin ganin gyaran da aka yi wa matatun man fetur ɗin.

Wata sanarwa daga jami'in yaɗa labarun kamfanin, Olufemi Soneye ta ce: "Muna miƙa ƙoƙon gayyata ga tsohon shugaban ƙasa Obasanjo domin ya duba matatun man fetur ɗin da aka gyara domin ya ga ci gaban da aka samu a ƙarƙashin sabon kamfanin NNPC Limited.

"Muna gayyatarsa ya haɗa hannu da mu a ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da samun isasshen makamashi ga ƙasarmu domin amfanin al'umma.

"Muna tabbatar masa da cewa muna maraba da shawarwarinsa"

Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL, Mele Kyari a lokacin ƙaddamar da matatar man fetur ta Warri a ranar 30 ga watan Disamba, 2024, bayan kammala yi mata gyara.

Asalin hoton, X/NNPCL

Bayanan hoto, Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL, Mele Kyari a lokacin ƙaddamar da matatar man fetur ta Warri a ranar 30 ga watan Disamba, 2024, bayan kammala yi mata gyara

Yanzu haka dai kamfanin NNPCL ya bayyana cewa matatar man fetur ta Warri, wadda ke da ƙarfin tace ɗanyen man fetur ganga 120,000 ta fara gadan-dagan tun bayan ƙaddamar da ita a ranar 31 ga watan Disamba.

Kamfanin ya wallafa hotuna a shafinsa na X, na yadda aka fara loda man fetur a tankokin dakon mai daga matatar.

Sai dai sau da dama, an sha gudanar da gyararraki a irin waɗannan matatu na Najeriya, amma aikin da suke yi ba ya ɗorewa.

A cikin shekara ta 2023, majalisar wakilan Najeriya ta buƙaci a gudanar da bincike kan kuɗaɗen da ƙasar ta kashe wajen gyaran matatun man fetur ɗin a cikin shekara 10.

Wani rahoto na majalisar ya yi zargin cewa Najeriya ta kashe kuɗi dala biliyan 25 a cikin shekarun 10 domin gyaran matatun man fetur, sai dai duk da haka babu wani sakamako na kirki da ake samu.

Obasanjo, wanda ya mulki Najeriya a matsayin soja daga shekarar 1976 zuwa 1979 da kuma a matsayin farar hula daga shekarar 1999 zuwa 2007 ya yi suna wajen tofa albarkacin bakinsa kan lamurran ƙasar, lamarin da ke haifar da rashin jituwa tsakaninsa da gwamnatocin da suka biyo bayan shi.