Matatar Fatakwal ta koma aikin tace man fetur

///

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Matatar man fetur ta Fatakwal da ke jihar Rivers ta dawo aiki, inda ta fara tace man fetur, kamar yadda babban jami'in hulɗa da jama'a a kamfanin NNPCL, Femi Soneye ya bayyana.

A cewarsa, "yau an samu wata gagarumar nasara domin matatar man fetur ta Fatakwal ta fara tace man fetur. Wannan wani sabon babi ne a ɓangaren makamashi a Najeriya, da yunƙurin inganta tattalin arzikin ƙasar," kamar yadda ya bayyana a ranar Talata.

Ya ce za a fara lodin man fetur ɗin daga yau Talata, sannan ya ƙara da cewa kamfanin na NNPCL na yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da ita ma matatar Warri ta fara aiki.

Wannan ya kawo ƙarshen gazawar cika alƙawurra na lokacin kammala gyaran matatar da gwamnati ta sha yi a baya.

Shekaru uku da suka gabata, gwamnatin Najeriya ta amince da ware kuɗi dala biliyan 1.5 domin gyara matatar, wadda ɗaya ce daga cikin matatun man fetur mafi girma a ƙasar.

Komawa aikin matatar ta Fatakwal na zuwa ne bayan fara aikin matatar man fetur ta Dangote mai ƙarfin tace gangar ɗanyen man fetur 650,000 a kowace rana.

A baya-bayan nan dai an ta samun taƙaddama tsakanin kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL da matatar ta Dangote.

Cire tallafin man fetur da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi a ranar farko ta mulkinsa a shekarar 2023 ya shafi ɓangarori da dama na tattalin arziƙin ƙasar.

Kuɗin sufuri ya ƙaru, sannan an samu tashin farashin kayan masarufi yayin da darajar kudin ƙasar ta zube, wata matsala da har yanzu gwamnatin ƙasar ta kasa shawowa.