Dalilai uku da suka sa farashin dalar Amurka ya ɗan faɗi

Asalin hoton, Getty Images
A Najeriya, da alama farashin dalar Amurka na ci gaba da sauka inda a wasu wuraren ake canjar da dalar Amurka ɗaya a kan kusan naira dubu daya da dari biyar da ɗoriya musamman a kasuwar bayan fage.
Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa an fara ganin raguwar darajar dalar ne tun daga farkon makon nan a hukumance da kuma kasuwannin bayan fage a Najeriya.
Farashin dalar ya yi ƙasa idan aka kwatanta da makonnin da suka gabata.
Alhaji Sani Salisu Dada shugaban ƙungiyar masu canjin kuɗaɗen ƙasashen waje a Kano ya shaida wa BBC cewa farashin da suke sayar da dalar da kuma wanda ake sayarwa a hukumance kusan kan-kan suke.
"A makon da ya gabata ana sayar da dala kan naira 1650 har ma 1660 amma a wannan makon dala ta dawo naira 1500 wani wurin kuma da 50.

Asalin hoton, Getty Images
1) Bai wa matafiya dala
Alhaji Sani Salisu Dada ya ce akwai dalilai da dama amma babba shi ne sakin mara da gwamnati ta yi.
"Idan gwamnati ta saka hannunta a komai za a samu sauƙi haka ma idan ta zare hannunta za a samu damuwa. Hakan dai ba zai rasa nasaba da umarnin da gwamnatin ta bai wa babban banki cewa a sayar da dala ga matafiya kuma fara sayarwar da aka yi a makon da ya gabata da ma wannan makon ma shi ne ya kawo sanadiyyar farashin ya sauka a kasuwa.
Idan gwamnati ta dakata to farashin zai ci gaba da hauhawa. Idan kuma gwamnati ta ci gaba da bayar da umarnin sannan ta sake rage farashin, to dala za ta ci gaba da karyewa." In ji Alhaji Sani Salisu Dada.
2) Rashin tabbas na dala a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Dr Abdulrazak Ibrahim Fagge masanin kimiyar kasuwanci a Najeria ya ƙara da cewa tsoron da jama'a ke da shi na rashin tabbas dangane da dalar ta Amurka ya sa mai dala na fito da ita na sayarwa.
"Wani ƙarin dalilin da ke sa dalar na faɗuwa shi ne yadda masu kasuwanni canjin kuɗi ke nuna fargaba na abin da zai iya zuwa ya zo dangane da dalar sakamakon irin matakan da Donald Trump ke ɗauka. Shi ne ya sa ba sa sayen ta sannan wadda suke da ita ma suke fito da ita."
3) Matakin Trump na ƙaƙaba wa duniya haraji

Asalin hoton, Reuters
Dangane kuma da faɗuwar darajar dalar a duniya, Dr Abdulrazak Ibrahim Fagge masanin kimiyar kasuwanci a Najeria ya ce dalilin faɗuwar dalar a duniya ba zai rasa nasaba da harajin da Donald Trump ke ƙakaba wa ƙasashen duniya.
"Barazanar da shugaban Amurka Donald Trump yake yi ga ƙasashen duniya na ƙaƙaba musu haraji ya sa su fito da dalolin su sayi gwal suna ajiyewa. A wannan makon farashin gwal ne yake ci gaba da ɗagawa ita kuma dala tana faɗuwa." In ji dakata Abdulrazaƙ.

Dr Abdulrazak Ibrahim Fagge ya ce idan aka ci gaba da haka to lallai faɗuwar darajar dalar ka iya shafar farashin kaya a Najeriya.
"Gaskiya idan aka je ƙarshen wannan watan sannan aka shiga sabon wata a haka to za a ga sauyi a farashin kayayyaki a cikin gida. Saboda yanzu ƴan kasuwa sun yi amfani da dalar wajen sayen kaya a watan da ya gabata. Idan suka yi amfani da dalar mai sauƙi wajen sayen kayan a gaba to lallai za a ga sauyi a farashin kayan." In ji Dr Abdurrazaƙ.
Tun dai bayan sauya manufofin gwamnatin Najeriya a harkar kuɗi, da gwamnatin shugaban ƙasar Bola Tinubu ta yi a 2023, darajar naira ta riƙa karyewa.
Al'amarin kuma ya ya ƙara jefa tattalin arziƙin ƙasar cikin matsi sanadiyyar tashin farashin kayan masarufi.











