Abin da ya sa tun asali Hausawa suka yanke shawarar zama a Kano

Asalin hoton, Getty Images
Hausawa na daga cikin ƙabilu mafiya yawan al'umma a nahiyar Afirka, waɗanda suka fi yawa a ƙasashen Najeriya da Nijar da Ghana da Saliyo da kuma sauran ƙasashen yammacin Afirka.
A yanzu yawan al'ummar Hausawa a duniya ya kai kimanin miliyan 150, sai dai ana da yaƙinin cewa a yanzu mafi yawan Hausawa 'barbarar yanyawa ce' ta ƙabilu daban-daban sanadiyyar auratayya da baƙin kabilu, musamman Fulani.
Dakta Raliya Zubairu Mahmud, malamar tarihi a Najeriya ta ce "da Bafulatani da Bahaushe yanzu an zama abu ɗaya, ni ma Bafulatana ce amma yanzu babu Fulatancin, Bahaushiya ce kawai."
Kano, jiha mafi yawan al'umma a Najeriya na daga cikin yankunan Bahaushe mafiya shahara a duniya, inda ake wa, musamman birnin Kano kallon tamkar cibiyar ƙasar Hausa.
A yanzu birnin, wanda ya shahara a harkar kasuwanci
Zuwan Hausawa Kano
Dakta Raliya ta ce an tabbatar da cewa Bahaushe ne mutm na farko da ya fara zama a Kano a wani yanki da ake kira Dala.
"Babu wani marubuci a tarihi da ya iya gano asalin lokacin da ɗan'adam ya fara zama a Kano, amma dai ko mene ne an tabbatar da cewa Hausawa ne suka fara zama a yankin," in ji ta.
Ta ce a iyakar abin da aka sani shi ne "wani mutum da ake kira Dala, wanda ya fito daga Gaya shi ne ya fara zama a kusa da dutsen da yanzu ake kira Dala."
Daga baya sai mutane suka riƙa shigowa daga Gaya da sauran wasu yankuna suna zama tare da shi, kuma wurin ya riƙa cika.
Daga nan ne sai suka riƙa matsawa zuwa wasu duwatsun da ke kusa, waɗanda su ma aka gano suna da arziƙin ma'adanin tama.
"Suna zama a ƙasan dutsen ne domin ya kare su daga sanyi da kuma mahara - mutane da dabbobi - kuma suna amfani da dutsen wajen farauta."
Dakta Raliya ta ce rayuwar mutanen ta dogara ne kacokan a kan waɗannan duwatsu.
Baya ga dutsen Dala, sauran duwatsun da Hausawa suka riƙa zama a ƙasansu su ne Gwauron Dutse da Magwan da Jigirya da Fanisau da Santolo da Jaba da kuma Tanaga.
A ɓangare ɗaya mutumin, wanda ake kira Dala ya kasance mutum ne da ya shahara a tsakanin mutanensa, inda ya zamo mai ƙarfi da iko, kuma aka zaɓe shi a matsayin shugaba, sannan aka sanya wa wurin sunansa.
Dala shi ne kaka ga mutumin da ya zo daga baya, wanda ake kira Barbushe.
Me ya sa Hausawa suka yanke shawarar zama Kano?

Asalin hoton, Getty Images
Kyawun ƙasar noma da kuma arziƙin tama da ke yankin Kano ne suka ja hankalin Hausawan da suka fara zama a Kano.
"Suna yin noma sannan kuma suna samun tama, wadda suke narkarwa suna mayar da shi ƙarfe, inda suke ƙera fartanyar noma da kayan farauta da kuma makaman da suke kare kansu kuma suke kai farmaki ga abokan gaba," in ji Dakta Raliya.
Haka nan kuma malamar tarihin ta ce dutsen da Hausawan suka fara zama a gefensa ya zama kariya ne ga al’ummar, inda suke hawa suna buya a yayin da aka kawo musu farmaki.
Sannan kuma sukan yi amfani da shi a matsayin wurin da suka hau domin hango namun dajin da suke farauta.
Mulki
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An fara gudanar da mulki irin na sarakuna a Kano ne lokacin wani mutum da ake kira Barbushe, wanda tsatso ne na Dala, mutumin da tarihin da ake da shi ya nuna cewa shi ne wanda ya fara zama a yankin Kano.
Shi Barbushe, a cewar Dakta Raliya ya kasance mutum jarumi wanda ke da alaka ta kut da kut da abin bautar Hausawa a wancan lokacin, wato tsumburbura.
Barbushe ya kasance yana da mutanen da ke kasansa wadanda suke a matsayin hakimai.
Hakiman su ne ke kula da lamurran al’ummar da ke rayuwa a duwatsun da ke yankin na Kano.
Daha cikin hakiman na Barbushe akwai mutane irin su Mazauda da Sarkin makafi da Giji-Giji da Hamburki da Dan butuniya da Tsoron Maje da Jan Dodo da Bakon yaki da kuma wasu da dama.
”Duk wani abu da mutane za su yi suna biyayya ne ga wadannan mutane kuma kowa ba zai so ya yi abin da zai saba musu ba,” in ji Raliya.
A bangare daya kuma hakiman da kuma shi Barbushe na kula da lamurran mutanensu da warware duk wata matsala da ta taso.
Baya ga shugabannin yankuna, Hausawa na wancan lokaci na kuma amfani da shugabanni a harkar sa’o’insu, kamar uwargona da ke kara amfanin gona daga mabarnata.
Sauyin jagoranci
Hausawa a Kano sun ci gaba da bin tsarinsu na bauta da mulki har zuwa lokaci mai tsawo kafin daga baya aka samu sauyi a shekara ta 999, lokacin da Bagauda ya isa kasar Kano.
Bagauda ya yi galaba a kan al’ummun da ke zaune a Kano sannan ya kafa mulki wanda ya shafe daruruwan shekaru.
Bayanai sun nuna cewa tuntuni Barbushe ya yi hasashen zuwan Bagauda, tare da cewa zai zo ya kawar da tsarin shugabanci da sauya tayuwar al’umma.
“A lokacin da ya zo ne aka ga bayan dukkanin mutanen da ke yankin, inda ko dai mutum ya bi ko kuma ya bar gari, in ji Dakta Raliya.
“Yawancinsu sun yi biyayya, inda aka ci gaba da rayuwa, ana kawo tsare-tsare daban-daban har zuwa lokacin zuwan Usman Danfodiyo wanda ya jaddada musulunci.”
Tun daga wancan lokaci an ci gaba da hada-hadar kasuwanci a Kano kuma gari ya faɗaɗa.
A wannan lokaci an shigar da dokoki da dama zuwa Kano daga kasashe daban-daban.
Sai dai a 1807, zuwan Fulani masu jihadi - wadanda ke a karkashin jagorancin Usman Danfodiyo ya sauya lamurra da dama.










