'Yadda na tsira daga kisan ƴan sintiri a Uromi'

HUSAINI TORANKAWA

Asalin hoton, HUSAINI TORANKAWA

    • Marubuci, Abubakar Maccido
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist, Kano
  • Lokacin karatu: Minti 5

"Ƴaƴanmu ba masu laifi ba ne. Su ba ɓarayi ba ne, su mafarauta ne da ke fafutikar neman na kansu'', a cewar Sadiya Sa'adu mahaifiyar Haruna Hamidan, ɗaya daga cikin matasan da ƴan sintiri suka kashe a garin Uromi.

Kisan gillar da aka yi wa matasan – wanda aka ɗauka a bidiyo sannan kuma aka yaɗa shi a shafukan sada zumunta – ya haifar da zazzafar muhawara da suka daga masu ruwa da tsaki a faɗin ƙasar.

A ranar Alhamis 27 ga watan Maris ɗin 2025 ne, aka kashe mafarautan a lokacin da suke kan hanyar su ta komawa Kano daga Farautar da suka je jihar Rivers.

Sadiya ta ce ɗan nata shi ke ɗaukar ɗawainiyar gidansu tun bayan rasuwar mahaifinsa.

"Shi ke ɗaukar ɗawainiyata da ta ƙannensa, don haka yanzu ba mu san yadda rayuwa za ta kasance da mu ba ."

Sadiya ta ce magana ta ƙarshe da ta yi da ɗan nata, ita ce kwana hudu kafin kisan, lokacin da ya aika mata da kuɗi domin sayayyar kayan sallah ga ƙaramin ɗansa.

"Na yi magana ta ƙarshe da shi ranar 22 ga watan Maris, lokacin da ta aiko mana da kuɗi domin sayen kayan sallah ga ƙaramin ɗansa, har ma na ce masa kuɗin ba za su isa ba, ya kuma ce zai yiwo ciko. Ya ma fa ce min ba zai zo gida sallah ba, a maimakon haka zai aiko mana da kuɗin sayayyar kayan sallar.''

Sadiya ta ce ta samu labari a cikin garinsu cewa mafarautan na cikin hatsari, kafin daga baya a sanar da ita labarin kisan ɗan nata.

Sadiya ta ce ƴaƴansu ba ɓarayi ba ne, ba kuma masu aikata laifi ba ne.

"Ƴaƴanmu ba ɓata-gari ba ne, ba su taɓa yin sata ba, su farauta ne da ke fafutikar neman na kansu," kamar yadda ta bayyana a yayin da take roƙon gwamnati ta yi musu adalci.

Shida daga cikin mutanen 16 da aka kashe, ƴan asalin garin Toronkawa ne a jihar Kano.

Tun bayan faruwar lamarin, ƙauyen Torankawa na cikin alhini da jimami kan batun.

Ƙauyen ya yi fice a sana'ar farauta, inda suke amfani da sana'ar wajen gwanda ƙarfi da jaruntar mutanensu.

BBC ta ziyarci ƙauyen inda ta tattauna iyalan waɗanda suka mutu da kuma ɗaya daga cikin mutanen da suka tsallake rijiya da baya a harin.

Mutanen Toronkawa shida da suka mutu a harin

Mafarauta

Asalin hoton, HUSAINI TORANKAWA

  • Abdulƙadir Umar – Ya bar mata biyu da mahaifiyarsa.
  • Zaharaddeen Tanko – Ya bar mace guda da ƴaƴa huɗu.
  • Haruna Hamidan – Ya bar mace guda da ƴaƴa huɗu.
  • Usaini Musa – Ya bar mata biyu da ƴaƴa biyu.
  • Abdullahi Harisu – Ya yi aure wata huɗu da suka gabata.
  • Ya'u Umaru & Abubakar Ado – Waɗanda samari ne da ba su yi auren fari ba
Torankawa

Asalin hoton, HUSAINI TORANKAWA

"Ya bar ni da ƴaƴa uku" – Hadiza Muhammad

Torankawa

Asalin hoton, HUSAINI TORANKAWA

Hadiza Muhammad, wadda ɗaya ce daga cikin mata biyu da Abdulkadir Umar ya bari, ta bayyana irin halin da take ciki.

Ta ce a ranar da aka kashe mijin nata ma ta yi magana da shi, a lokacin da ya kira ya ce buƙaci a sanya shi cikin addu'a.

"Ya faɗa min cewa suna kan hanya, su sanya su cikin addu'a. Daga nan ban sake ji daga gare shi ba."

Ta ce kusan ƙarfe 4:00 na maraice, wasu mutane suka faɗa mata cewa motarsu ta yi hatsari, amma ba su faɗa mata cewa farmakarsu aka yi ba.

"Daga baya ne suka faɗa mana cewa wasu mutane ne suka kashe su. Tun daga lokacin na fita a hayyacina. Ba za mu taɓa yafe musu ba. Muna fatan Allah ya yi mana sakayya da waɗanda suka kashe mana mazajenmu.''

"Mijina mutumin kirki ne. Yana iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya sanya mu farin ciki," kamar yadda ta bayyana a lokacin da take neman adalci.

Yadda na tsallake rijiya-da-baya – Abubakar Shehu

Abubakar Shehu

Asalin hoton, HUSAINI TORANKAWA

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Abubakar Shehu, ɗaya ne daga cikin mafarautan da suka kuɓuta a harin, ya kuma bayyana yadda ta tsallake rijiya da baya daga harin masu ɗaukar doka a hannun.

Ya ce wannan ne karonsa na farko da ya je farauta a Fatakwal, kuma a lokacin da suka isa Uromi, ƴan sintiri sun tare su.

"A lokacin da muka isa Uromi, sun tare mu a kan titi, suka ce mu sauko daga cikin mota.''

"Yayin da muka sauko sai suka fara dukanmu ba tare da sun tambaye mu komai ba."

Da ya ga yanayin zai ɓaci, sai ya gudu ya ɓuya.

"Da suka fara dukanmu, wasu mutanen da ke wurin sun ce mana mu gudu."

"A lokacin da na yi yunƙurin gudu, biyu daga cikinsu sun yi ƙoƙarin dakatar da ni, amma Allah ya ba ni sa'a ba su kamani ba.''

"Na ɓuya a wani kango, daga nan na riƙa jin duk abin da ya faru da ƴan'uwana."

Daga baya cikin dare, kusan ƙarfe 10:00 na dare ya samu wani direban tankar mai ya taimake shi ya kai shi Kabo, daga nan ya iso Kano.

Shehu ya ce tun kafin ya tsira abokinsa Abdulkadir Umar, ya riga ya jikkata a hannun ƴan sintirin.

"Tun kafin na gudu, tuni Abdulkadir ya faɗi a ƙasa, abokaina sun samu munanan raunuka.''

Ya ce ƴan sinitirin ba su tambaye su, ko su wane ne su ba, kawai sun far musu ne.

"Muna da katunan shaidarmu da ke nuna cewa mu mafarauta ne, amma ba su tambaye mu komai ba.''

"Kuɗin da suka gani a hannunmu na mafarautan da ba su samu damar aika kudi gida ba ne."

"Bindigogi da karnukan da muke tafiya da su, duka suna da takardun lasisi. Mu mafarauta ne ba ƴan fashin ba.''

Ya ce bai taɓa tsammanin zai rayu ba.

"Na yi tunanin cewa tawa ta ƙare, amma da ikon Allah na kuɓuta,'' in ji shi.

'Dole gwamnati ta ɗaukar mana fansa'

HUSAINI TORANKAWA

Asalin hoton, HUSAINI TORANKAWA

Bayanan hoto, Shugaban Mafarautan Torankawa

Shugaban ƙungiyar farautan Torankawa, Mustapha Usman, ya ce dole gwamnati ta hukunta waɗanda suka kashe musu mutane.

"Dole gwamnati ta kama tare da hukunta waɗanda da suka kashe mana mafarauta 16 a Uromi."