Kashe matafiya a jihar Edo take haƙƙin ɗan'adam ne - Gwamnonin Arewa

Asalin hoton, Edo State Government
Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta yi tir da kisan matafiya 'yan asalin yankin a jihar Edo da ke kudancin ƙasar, inda ta kwatanta shi da "take haƙƙin ɗan'adam".
Gwamnatin jihar ta Edo ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin da ya faru a garin Uromi da ke ƙaramar hukumar Arewa Maso Gabashin Esan ranar Alhamis, inda ta ci alwashin hukunta "masu laifin".
Wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga kudanci zuwa arewacin Najeriya.
Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce mutanen da aka kashe 'yan asalin jihar Kano ne kusan 16.
"Yan sa-kai sun tare matafiyan, suka fito da su daga motarsu, suka yi musu duka, sannan suka cinna musu wuta," a cewar wani saƙo da Amnesty ta wallafa a shafukan sada zumunta.
Ta ƙara da cewa matafiyan na kan hanyar komawa garinsu na asali ne "domin yin bukukuwan sallah tare da iyalansu".
Wata sanarwa da fadar gwamnatin jihar ta Edo ta fitar ta tabbatar cewa maharan 'yan sa-kai ne.
"Binciken farko-farko ya nuna cewa matafiya ne da suka taso daga Fatakwal na jihar Rivers suka ratso ta garin, sai ƴanbanga suka kama su da tunanin cewa ɓatagri ne," kamar yadda sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar, Fred Itua, ya bayyana.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana adadin mutanen da aka kashe ba a harin, amma ta ce Gwamna Okpebholo ya ziyarci garin a ranar Juma'a, inda ya yi alƙawarin gano waɗanda suke da hannu domin su fuskanci hukunci.
Amnesty ta yi kira da a gaggauta gudanar da bincike kan lamarin tare da tabbatar anhukunta masu hannu a cikinsa.
Shi ma jagoran jam'iyyar adawa ta NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi tir da kisan, inda ya nemi a gudanar da bincike.
Yayin ziyarar da ya kai wurin da lamarin ya faru, Gwamnan Edo Monday Okpebholo ya yaba wa shugabannin 'yan arewacin Najeriya game da yadda "bisa yadda suka kwantar da al'amarin cikin hikima", in ji sanarwar.
'Dole ne a yi bincike'
Ƙungiyar gwamnonin ƙarƙashin shugabancin Gwamnan Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ta buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin hukunta waɗanda suka aikata "wannan ta'asar".
Ƙungiyar ta kwatanta harin a matsayin "ƙeta hakkin ɗan'adam", inda ta ce ba za ta lamaunci ɗaukar doka a hannu ba.
Ta kuma jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa ƴan uwansu a lamarin.
"Mun damu matuka kan kisan bayin Allah da ba su aikata komai ba, da kuma irin yadda aka kashe su," in ji Inuwa Yahaya.
"Abin da aka aikata ya saɓa wa doka, don haka ya zama dole hukumomi su gudanar da cikakken bincike kan yadda aka kashe mutanen ta hanyar cinna musu wuta."
Gwamna Inuwa Yahaya ya nanata cewa kowane ɗan Najeriya na da ƴancin yin tafiya zuwa ko'ina, ba tare da nuna bambancin addini ba.
Ya buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakin da ya dace don hana afkuwar irin haka a nan gaba.











