Dalar gyaɗa: Tarihi da tasirinta ga tattalin arziƙin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Aisha Babangida
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Idan aka tambayi matasa da dama a Najeriya – musamman a Arewacin ƙasar – mece ce Dalar Gyaɗa? Da wuya ka samu wanda zai iya ba da amsa mai gamsarwa.
Amma a da, kafin a gano man fetur a Najeriya, noma da fitar da gyaɗa na daga cikin manyan hanyoyin da ƙasar ke samun kuɗin shiga. Wannan ne ya haifar da abin da ake kira da "Dalar Gyaɗa" a arewacin ƙasar musamman a jihar Kano.
"Dalar gyaɗa ita ce tarin gyaɗa da ake ginawa a cikin kwando ko buhuna a Kano har ta yi tudu da tsiri-tsiri makamancin Dutsen Dala, musamman a lokacin turawa inda ta zama wata alama ta bunƙasar noma da arziki." Kamar yadda Dr. Junaidu Danladi, masanin tarihi a sashen tarihi a Jami'ar Bayero Kano ya bayyana BBC.
Yaushe aka fara yin Dalar Gyaɗa a Kano?

Asalin hoton, Getty Images
A cewar Dr. Junaidu, ba za a iya fadin takamaiman ranar da aka fara yin Dalar Gyaɗa ba, domin ba abu ba ne da aka fara a rana ɗaya ba. A maimakon haka, ya kamata a kalli tarihin gyaɗar kanta.
"Gyaɗa dai tana cikin amfanin gona da ake nomawa a Kano da yankin Hausa tun kafin zuwan turawa. A wancan lokacin, ana nomanta ne don buƙatun gida, ba don kasuwanci ko fitar da ita zuwa waje ba." In ji shi
Sai dai zuwan turawa a shekarar 1912 ne ya haɓaka noman gyaɗa da cinikayyarta. Turawan mulkin mallaka sun buƙaci kayan sarrafawa don masana'antunsu, inda suka fi mai da hankali kan gyaɗa da auduga daga yankin Arewacin Najeriya.
"Dalilin hakane Kano ta zama cibiyar hada-hadar gyaɗa, duk da cewa yawancin gyaɗar ba a nan kaɗai ake nomanta ba. Ana shigo da ita ne daga Katsina, Zazzau da sauran yankuna." Masanin tarihin ya ƙara da cewa.
Me ya janyo aka kafa Dalar Gyaɗa?
Masanin tarihin ya ce gyaɗar da ake tarawa a Kano ana tara ta ne kafin a ɗauke ta zuwa bakin teku don a fitar da ita zuwa ƙasashen waje. Wannan ya haifar da gina layin dogo don ɗaukar gyaɗa da sauran amfanin gona.
Kamfanonin turawa da wakilansu sun zauna a Kano saboda mashahuran 'yan kasuwa da ke gudanar da harkokin gyaɗa. A haka ne aka fara gina manyan tarin gyaɗa – wato dalar gyaɗa – wanda ake ɗiba daga nan a kai bakin teku
'Yadda muka rinƙa gina Dalar Gyaɗa'

Asalin hoton, Getty Images
Malam Adamu Liman, tsohon ɗan dako ne wanda yanzu shekarunsa sun haura 80, ya ba da labarin yadda rayuwa take a lokacin dalar gyaɗa.
"Na fara aikin ɗaukar buhunan gyaɗa tun ina saurayi. A kullum da sassafe muke shiga fili muna ɗora buhuna muna gina dalar gyaɗan," in ji shi.
Ya ce aikin yana da wahala amma akwai albarka. "A rana ka iya samun abin da zai isa ka sayi abinci da tufafi, har ma ka ajiye."
"A lokacin, noma yana da daraja, ba kamar yau ba da komai ya ƙara tsada, matasa suna jin daɗin aikin gona. Duk wanda ya riƙe asusun gyaɗa, ana ganinsa a matsayin wanda ya yi arziƙi," in ji shi
"Haka fa za ki ga mutane daga sassa daban-daban na ƙasa suna zuwa kallon dalar gyaɗa, kamar yawon buɗe ido haka." in ji shi.
Yanzu kuwa, a cewarsa, dalar gyaɗa ta zama tarihi.
Sai dai irin su Malam Adamu ba za su taɓa mantawa da irin ƙoƙarin da suka bayar don gina wannan tarihin ba.
Rawar da Dalar Gyaɗa ta taka a tattalin arzikin Najeriya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Gyaɗa da kanta, ko kuma Dalar Gyaɗa, ta taka rawar gani a tattalin arzikin Najeriya da Kano baki ɗaya.
A lokacin turawa, gyaɗa na daga cikin manyan abubuwan da ake fitarwa zuwa kasashen waje. Wannan ya haɓaka tattalin arzikin ƙasar ta fuskar kudaden shiga da samar da ayyukan yi.
"Haka kuma tsarin haraji da turawa suka kafa ya sa mutane da dama suka koma noman gyaɗa saboda shi ne ke samar da kuɗin biyan haraji. Wannan ya rage noman abinci amma ya bunƙasa kasuwar gyaɗa.” Dr Junaidu ya ƙara da cewa.
"A cikin gida kuma, an samu mashahuran 'yan kasuwa kamar su Alh. Alhasan Dantata (1877-1955) da Alh Umaru Sharubutu Koki (1853-1947) da Adamu Jakada (1943) da kuma Maikano Agogo." waɗanda suka taka rawa wajen kasuwancin gyaɗa a Najeriya da wajen ƙasa." kamar yadda farfesa Masur Ibrahim Muktar, wani masanin tarihi shi ma ya shada wa BBC.
Baya ga 'yan ƙasa, akwai kuma 'yan Lebanon kamar El-Khalil, Rizk, George A. Debbas da Joseph Farhat waɗanda suka kasance cikin manyan masu hannu a harkar gyaɗa da yadudduka a Kano da kewaye.
Haka zalika, 'yan Syria kamar dangin Saba, Farhat, Salem, da Antoun sun taka rawa a ciniki da safarar gyaɗa daga arewa zuwa kudu.
Kamfanonin Turai kamar Royal Niger Company da United Africa Company (UAC) ne suka mamaye fitar da gyaɗa zuwa ƙasashen waje.
"Gwamnati a lokacin ta kafa kwamitin cinikin gyaɗa domin tsara farashi da tabbatar da tsari" in ji farfesan.
Kuɗaɗen da aka samu daga harkar gyaɗa an yi amfani da su wajen gina makarantun firamare da na gaba da firamare da asibitoci da hanyoyi da wutar lantarki, da sauran abubuwan more rayuwa, Dr Junaidu ya yi ƙarin haske.
Wannan ya nuna muhimmancin da gyaɗa ta taka a rayuwar tattalin arzikin ƙasa.
Me ya janyo ɓacewar Dalar Gyaɗa?
Dr Junaidu ya bayyana cewa dalilai da dama ne suka haddasa bacewar Dalar Gyaɗa. Babban dalili shi ne gano man fetur a Najeriya a shekarar 1958 wanda daga baya ya mamaye harkokin tattalin arziki.
Bayan samun 'yancin kai, Najeriya ta mai da hankali kan man fetur wanda ya rage muhimmancin noma, musamman noman gyaɗa.
Sauran dalilai sun haɗa da sauya tsarin haraji, da rage buƙatar tara gyaɗa a wuri ɗaya bayan kafa masana'antun cikin gida da ke sarrafa gyaɗa, wanda ya rage buƙatar tura gyaɗar zuwa waje kamar a baya.
"Amma a ƙarshen mulkin turawa aka fara kafawa da kuma haɓaka kamfanoni na ƴan ƙasa da waɗanda suka fara sarrafa gyada wanda hakan ya sa ba sai an tura gyada zuwa bakin teku ba kamar da, saboda ana iya sarrafa ta a gida. Wannan ma ya rage buƙatar tara dalar gyaɗa a wuri ɗaya," in ji Junaidu.
Yanayin noman gyada yana raguwa sosai yanzu, amma akwai ƙananan kasuwanni a gida da ake sarrafa gyada kamar Dawanau, da kuma kamfanoni da mata masu sana'ar ƙuli-ƙuli.
Ko akwai yiwuwar Dalar Gyaɗa ta dawo?
Dr Junaidu Danladi ya bayyana cewa yana da wuya a dawo da dalar gyaɗa kamar yadda take a baya saboda sauye-sauye da suka faru a tsarin tattalin arziki da noman zamani.
Amma kuma Farfesa Mansur Muktar ya ce idan aka ɗauki matakai kama haka za a iya samun dawowar wani irin cigaba da ya yi kama da zamanin dalar gyaɗar.
- Saka jari mai yawa a harkar noma,
- Farfado da masana'antun sarrafa man gyaɗa,
- Tallata kayan gyaɗa a cikin gida da ƙetare,
- Amfani da na'urorin zamani wajen noma,
- Bayar da tallafi ga manoma,
- Da kuma rage shigowar kayan waje –

Asalin hoton, Getty Images
A tarihi, gyaɗa da dalarta sun taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka tattalin arzikin Najeriya da Kano musamman a lokacin mulkin Turawa. Ko da yake dalar gyaɗa ta zama tarihi yanzu, akwai darussa da za a iya koya daga tarihin ta – musamman game da muhimmancin noma da sarrafa kayan cikin gida.
Kamar yadda Malam Adamu Liman ya ce:
"Da gwamnati za ta dawo da tallafi ga manoma, ai da an sake ganin dalar gyaɗa, ko da a ce ba za ta kai irin yadda take a da baya."











