'Har yanzu muna cikin wahala': Shekara ɗaya bayan ambaliyar Maiduguri

    • Marubuci, Chris Ewokor
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
    • Aiko rahoto daga, Maiduguri
  • Lokacin karatu: Minti 6

Ana cikin fargabar sake samun ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri, da ke arewa maso gabashin Najeriya, shekara ɗaya bayan mamakon ruwan sama da ya haifar da ɓallewar madatsar ruwa, kuma ya haɗiye unguwanni da dama.

Mutane da yawa waɗanda har yanzu ke ƙoƙarin farfaɗowa daga ambaliyar ta bara, tunanin cewa abin zai iya sake faruwa ba ƙaramin tashin hankali ba ne.

Aƙalla mutum 37 ne suka mutu sanadiyyar ambaliyar sannan mutane miliyan biyu suka bar muhallansu bayan gagarumar ɓarnar da ambaliyar ta yi a kan gidaje da kasuwanni da kuma gonaki.

Sa'adatu, mai shekara 42 a duniya ta rasa ɗanta mai shekara biyu.

"Ya mutu ne sanadiyyar yunwa da kuma zazzaɓi a lokacin da ambaliyar ta faru. Saboda a lokacin ba mu da abinci, babu maganai kuma babu wuri mai kyau da za mu zauna."

Ta faɗa wa BBC yadda hankalinsu ya tashi a lokacin da ambaliyar ta fara a cikin dare, yara suka riƙa kuka, suka fice daga gidajensu babu shiri, suka bar komai, "sai ƴan kayan sawa ƙalilan".

Ta ce ta samu tallafin tallafin naira 10,000 daga gwamnati bayan faruwar ambaliyar.

Sai dai ta ce tun daga wancan lokacin gwamnati ba ta ƙara taimaka musu ba: "Tun wancan lokacin, ba mu ƙara ganin wani abu daga cikin alƙawurran da gwamnati ta yi mana ba. Har yanzu muna jira, muna kuma shan wahala."

Gwamnatin jihar Borno ta ce ta taimaka wa mutanen da bala'in ya rutsa da su.

Ta ce ta samar da sansanoni ga waɗanda suka rasa muhalli, da abinci da kuma tallafin kuɗi.

Sai kuma abu mafi muhimmanci, gwamnati ta fara gyaran madatsar ruwan ta Alau - wadda ke a kusa da birnin Maiduguri - wadda ɓallewarta ce ta haifar da ambaliyar.

An fara aikin gina madatsar ce a shekarar 1986, kuma hukumar kula da ci gaban yankin tafkin Chadi ce ke kula da shi.

To sai dai rikicin Boko Haram da aka shafe sama da shekara 10 ana fama da shi a yankin ya sanya ba a iya kula da madatsar yadda ya kamata, kamar yadda shugaban sashen kula da na'urori na hukumar, Mohammed Shettima ya shaida wa BBC.

"Madatsar ruwan tana a gefen dajin Sambisa ne - kimanin kilomita huɗu daga dajin, wanda ya zama sansanin ƙungiyar mayaƙan," in ji shi.

"Dirkokin madatsar sun yi rauni saboda rashin kula, a lokacin da aka samu ruwan sama mai ƙarfi a bara, sai katangun suka ɓalle, lamarin da ya sa ruwan mai yawan gaske daga madatsar ya malale birnin.

A watan Agusta an kashe sojoji biyu kusa da madatsar sannan kuma wasu da ake zargin masu iƙirarin jihadi ne sun kashe jami'an tsaro haɗu.

Ɗaya daga cikin mutanen da ambaliyar ta shafa wadda kuma rikicin Boko Haram ya rutsa da ita, ita ce Maryam Jidda.

Ta tsere daga garinta na asali, Damboa, tare da ɗiyarta da jikokinta biyu lokacin da mayaƙan Boko Haram suka kai hari, shekara huɗu da suka gabata.

"Ba zato ba tsammani. Suka faɗo garin kamar guguwa, a cikin dare," in ji ta.

Barowar ta daga Damboa, ta yi tunanin cewa ta ga wurin zama a birnin Maiduguri, amma sai aka samu ambaliyar ruwa wanda ya sake tayar da ita daga inda ta samu matsuguni.

Lokacin da BBC ke tattaunawa da ita, tana zaune a kan sauran bangon gidanta da ambaliya ta rushe, matar mai shekara 72 a duniya, fuskarta na nuna cewa ta sha wahala a tsawon shekaru.

Ta ce: "Lokacin da ambaliyar ta zo ruwa ya kawo har ƙuguna, ina tsaye ina kuka," a cewar Jidda, lokacin da take bayar da labarin yadda ruwa ya cika gidan da take zaune.

Yanzu tana zama ne a wani sansani, inda babu isasshen abinci kuma babu ruwan sha mai tsafta.

Baya ga gidanta da ambaliyar ta lalata, ta kuma yi asarar kayanta da kuma hotunan iyalanta, wadanda ke tuna mata rayuwar da ta yi a baya.

Shekara ɗaya bayan ambaliyar ruwan har yanzu akwai mutanen da suke zama a tantuna bayan rasa gidajensu.

Akwai matasa waɗanda karatunsu ya samu matsala sanadiyyar haka, haka nan ma wasu sun rasa sana'o'insu.

Ali Kadau, wani matashi ɗan shekara 21, ya shaida wa BBC cewa ambaliyar ta raba shi da duk abin da ya mallaka.

"Kafin ambaliyar ina ririta rayuwata, ban yi karatu mai nisa ba, amma na iya sana'ar hannu - ina aikin kanikanci da gyaran taya," in ji shi, yayin da yake zaune kan wata ɓallaliyar kujera yana kore ƙudaje.

Kadau ya ce abin ya fara ne kamar yadda akan samu ruwan sama a lokacin damina, to amma a lokacin sai ruwan ya ƙi tsayawa. Ruwa ya fara shiga gidajen mutane, nan da nan ruwa ya mamaye unguwar Gwange, inda a nan yake zama.

Iyalansa sun kwashe kwana uku suna kwana a waje kafin suka samu mafaka a wata makaranta da aka mayar da ita matsuguni ga waɗanda ambaliyar ta tarwatsa.

Haka nan abin ya shafi wurin da yake aikin kanikanci, inda ambaliyar ta kwashe musu kayan aiki tare da lalata wasu.

"Yanzu haka nan nake zama. Ba aiki. Ba makaranta. Ba ni da kuɗin fara wata sana'a. Wani lokaci nakan yi turin baro a kasuwa domin samun abin da zan ci, wasu ranakun kuwa ba na komai sai dai na zauna ina tunane-tunane.

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayyana aikin gyara barnar da ambaliyar ta haifar a matsayin abu mai wahala, ganin yadda jihar ta yi fama da rikici tsawon shekara 16.

"Mun kafa kwamiti da muka ɗora wa aiki," in ji gwamnan, inda ya ce kwamitin ya riƙa yin aiki ba dare ba rana domin tabbatar da ganin mutanen da lamarin ya shafa sun samu tallafin da ya kamata, ciki har da samun muhalli da abinci.

Samar da muhalli ga mutum miliyan biyu a Maiduguri, birnin da yana ƙunshe da mutane sama da miliyan ɗaya wadanda rikici ya tarwatsa ba ƙaramin aiki ba ne.

"Babban abin da muka mayar da hankali a kai shi ne hana sake ɓallewar ruwa zuwa cikin birnin, mun samu nasarar hakan ta hanyar sauya akalar ruwa da kuma gina kwatoci," in ji gwamnan.

Rahoton kwamitin ya ce an tara kudi naira biliyan 28.2 daga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi, da kuma gudumawa daga ƙungiyoyin bayar da tallafi kamar hukumar kula da ƴan gudun hijira ta duniya da kuma Shirin samar da abinci na duniya.

An raba wani ɓangare na kuɗin ga iyalai sama da 101,330, tare da tallafin abinci da kuma sauran kayan agaji.

Haka nan an bayar da tallafin kuɗi ga ƴan kasuwa sama da 7,000 a kasuwannin da lamarin ya rutsa da su, da wuraren ibada da kuma makarantu masu zaman kansu.

Duk a cikin koƙarinta na sake farfado da yankunan da lamarin ya shafa, gwamnatin jihar Borno ta buƙaci ƙarin kuɗi naira biliyan 61 domin gyara abubuwan da suka lalace, kamar gadoji da hanyoyi da kuma asibitoci.

Sai dai akwai fargabar cewa ba za a iya samun waɗannan kuɗaɗe ba.

An dai samu wasu kuɗaɗen waɗanda za a yi amfani da su wajen gyrawa da inganta rijiyoyin burtsatse a birnin na Maiduguri domin maganace matsalar ƙarancin ruwa da ambaliyar ta haifar.

Yayin da damina ke ci gaba da nutsawa, fargabar mutane kamar su Sa'adatu ita ce "Ta yaya za su farfaɗo kasancewar sun yi asarar komai?"

Yayin da Jidda ke ci gaba da jimami, a cikin yaranta 10, yanzu uku ne kawai ke a raye.

Ta ce "Babu wani abin da ya rage min a rayuwa face tuno abubuwan da suka faru a baya da kuma takaici."