Jam'iyyar APC ta rabu gida biyu a Sokoto

Lokacin karatu: Minti 3

Jam'iyar APC mai mulki a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya ta dare gida biyu, sakamakon wani sabon rikici da ya kunno kai a cikinta, har ta kai ga samun wani ɓangare da ke hamayya da ɓangaren da ke biyayya ga gwamnatin jihar.

Wasu daga cikin ƴaƴan jam’iyyar na goyon bayan ɓangaren gwamnan jihar da sanata Aliyu Magatakardar Wamakko ke jagoranta, yayin da dayani bangaren kuma ke goyon bayan Sanata Ibrahim Lamiɗo.

Rikicin dai ya yi ƙamarin da har takai ga wasu da ke goyon bayan ɓangaren sanata Lamiɗo ajiye muƙaman da suke riƙe da su a jam’iyya da kuma waɗan da ke riƙe da shi a gwamnatance jihar ta Sokoto.

Hon Yakubu Sani Alhaji, daya ne daga cikin ƴan majalisar wakilai daga jihar ta Sokoto, da ke goyon bayan ɓangaren Sanata Ibrahim Lamiɗo ya ce sabuwar tafiya ce ta ɓulla a jam’iyyar APC a jihar Sokoto.

Har ila yau, ya ce, "An tsinci kai a wani yanayi na siyasa wanda mutane da kansu suka fahimci gaskiya, kana Sanata lamido wanda shi ne wanda Allah ya bai wa wanna matsayi na shugabanci da ya ke yi, ya zo da salon ci gaban al'umma da tafiya da kowane ɓangaren, shi yasa wadanda ke aiki a wasu wuraren suka ajiye aikinsu suka ga dacewar komawa ƙarkashinsa, saboda kishin jama'ar da ya ke da shi'' inji shi.

Haka kuma ya ce kafin yanzu gwamnan jihar shi ne uba a jam'iyya, amma yanzu da aka samu matsala sai wannan sabon shugabanci ya bullo.

"Mu ma mun yarda da abin da mutane da dama suka fada na cewar lallai abin da ake ba dai dai bane, mun yi magana cewar a sauya ba a yi ba, kuma mun ga abin da ake bai dace ba''

Ya ce suna nan a jam'iyyar APC ba za su sauya sheka ba, illa ma kirkirar wani sabon bangare a jam'iyyar da zai kalubalanci jagorancin gwamnan jihar a jam'iyyar ta su.

Sai dai a martanin shugabancin jam’iyyar APC a jihar Sokoto ya ce rikici ne da bai dauke shi komi ba duk da guguwar da ta ja wasu yan jam’iyyar har suna ajiye mukamansu, amma shugaban jam’iyyar a jihar sokoto Sadik isa Achida ya ce kofa a bude take ga duk mai son fita.

"Mu bamu san da wanna rikici ba, sannan babu wani da ya aiko mana takardar cewar ya ajiye mukaminsa, sannan kuma wai wanene Sanata Ibrahim Lamiɗo ma? Sanata ne kawai da aka zaɓa a Sokoto, bashi da wani muƙami a Sokoto ko a jam'iyya, amma kuma ya sani jam'iyya ce ta yi masa yaƙin neman zaɓe har ya yi nasarar samun kujerar da ya ke a kanta'' inji shugaban jam'iyyar APC a jihar ta Sokoto.

Haka kuma Sadik Isa Achida shugaban jam'iyyar APC a jihar Sokoton ya ce "matsayin Sanata Lamido a wajensu shine dan jam'iyya ne shi kwai, kuma bai sanar da mu cewar an masa wani abu ba''.

Yanzu dai kallo zai koma ga yadda jam’iyyar za ta ɗinke wannan ɓarakar da wasu ke ganin rikicin na iya kai jam’iyyar kasa.