Yadda manyan jam’iyyar APC da PDP ke jayayya a siyasar Sokoto

Manyan jam’iyyun siyasar Najeriya biyu wato APC da PDP na jayayya kan yawan masu sauya sheƙa a tsakaninsu a Sokoto, inda kowane ɓangare ke ganin shi ke kan gaba, kuma nasara na tattare da shi.

Wannan yanayi na zuwa ne yayin da ake daf da shiga yaƙin neman zaɓen shekara ta 2023.

Duk da cewa jam’iyyar PDP ce ke mulkin jihar, jam’iyyar adawa ta APC ke da mafi rinjayen kujerun ‘yan majalisar dokokin tarayya.

Wannan dalilin ya sa ake ganin fagen siyasar Sokoto a wannan marra na cikin halin rashin sanin maci tuwo kafin karewar miya tsakanin manyan jam’iyyun APC da PDP a manyan zabukan da ke tafe.

Me ɓangarorin ke cewa?

Alamomi na nuna sauyin da ake samu fiye da kowane lokaci na zaɓukan baya, domin an samu karfin jam’iyya mai mulki da ta adawa ya zo ɗaya tun kafin a kada kugen siyasa.

Sai dai Alhaji Muhammadu Oroji Wamako, wani jigo a jam’iyyar PDP mai mulki ya bugi kirjin cewa, su ke da ta cewa idan aka yi la’akari da yawan masu sauya sheƙa zuwa jam’iyyar daga APC mai adawa.

Oroji Wamako, ya ce sanin kowa ne duk wani ɗan Sokoto ko jihohin da ke kusa da Sokoto, PDP ce kusan a kullum ke karbar manyan ‘yan takara.

Ya bada misali da Yusuf Sulaiman, Salame da dai sauransu yana mai cewa, APC a yanzu a Sokoto tamkar an tuɓe mata riga ne baki ɗaya an bar ta da wando.

“A kullum karbar mutane muke yi babu safe babu rana.”

Sai dai yayin da jam’iyyar PDP ke wannan tinkaho na karbar jiga-jigan APC kamar ‘yan majalisar tarayya masu ci da tsohon minista, Alhaji Ibrahim Lamido ɗan takarar Sanata a jam’iyyar ta APC ya ce karbar jigan-jigan jam’iyya mai mulki ciki har da sanata da kwamishina da shugaban karamar hukuma mai ci da jam’iyyarsu ta yi kahonnin ne kawai aka gani, san na nan tafe.

“Siyasar ta sauya ba irin ta da ba ce, shi ya sa mutane tun da wuri suke sauya sheka.

“Kafin watan Oktoba muna da karfin gwiwar cewa mutane da dama za su bar PDP su dawo a garemu”, in ji Lamido.

Yadda kujerun suke

A halin yanzu dai jamiyyar adawa ta APC ce ke da dukkan kujerun ‘yan majalisar dattawa uku daga jihar da kuma biyar daga cikin ‘yan majalisar wakilai 11, inda jam’iyyar PDP ke da ‘yan majalisa shida.

A matakin jiha kuwa jam’iyar PDP ce ke da gwamna da ɗan karamin rinjaye a majalisar dokokin inda take da kujeru 16 daga cikin talatin yayin da APC ke da 14.