Ba don na tsokani Ronaldo na yi salon murnar sui ba - Hojlund

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan gaba na Manchester United Rasmus Hojlund ya kare salon murna da ya yi irin na Cristiano Ronaldo da ake kira "su" bayan ya ci Portugal a wasan gasar Nations League ranar Alhamis.
Hojlund ya zura a guje kuma ya yi tsalle tare da wurga hannaye ta baya a kan idon Ronaldo bayan jefa ƙwallon da ta bai wa ƙasarsa Denmark nasara a kan Portugal.
"Ban yi domin na tsokane shi ba, na sha faɗa cewa yana da tasiri sosai a harkokin ƙwallona," a cewar ɗanwasan.
"Ina wasa ne da ɗanwasa mafi hazaƙa a duniya, abin kwaikwayona, ba ƙaramin abu ba ne na ci kuma mu yi nasara.
"Cin su ƙwallo da na yi abu ba ne muhimmi. Na taɓa zuwa wajensa a 2009 bayan ya ci ƙwallo daga bugun tazara kuma tun daga nan na zama masoyinsa."
Tsohon ɗanwasan Real Madrid da Man United ɗin da ke taka leda yanzu a Al Nassr ta Saudiyya, Cristiano ya buga minti 90 na wasan sai dai bai taɓuka komai ba.
Hari ɗaya da ya kai shi ne wanda ya saka w ƙwallo kai amma ta yi faɗi zuwa waje.
Ƙwallon da Hojlund ya ci ce ta biyu da ya zira a raga sau biyu a jere bayan ya shafe wasa 21 ba tare da yin hakan ba.











