Lokuta huɗu da Kemi Badenoch ta yi maganganun da suka 'harzuƙa' ƴan Najeriya

Lokacin karatu: Minti 4

Kemi Badenoch ta yi maganganu da dama kan Najeriya tun bayan da ta zama shugaban jam'iyyar Conservatives a Birtaniya.

Ƴan Najeriya da dama na ta tsokaci a kan abubuwan da Kemi take faɗi a wuraren taruka, wadda mahaifanta duk ƴan asalin Najeriya ne.

Ta yi irin waɗannan kalamai ne a wuraren taruka da rediyo da kuma talabijin.

Yawanci takan yi magana ne a kan rayuwarta ta yarunta, inda ta bayyana cewa ta taso cikin tsoro saboda rashin tsaro a ƙasar wadda ta ce rashawa ta yi wa katutu.

Tuni mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya ce "za ta iya cire Kemi daga sunanta" idan ba ta alfahari da "ƙasarta ta asali".

Badenoch ta bar Najeriya ne shekaru 28 da suka gabata inda ta koma Birtaniya, ƙasar da aka haife ta.

Ta koma Birtaniya ne a lokacin da take da shekara 16 da haihuwa, inda ta zauna tare da wata ƙawar mahaifiyarta domin ci gaba da karatu.

Bayan auren mijinta, Hamish Badenoch, wani ma'aikacin banki ɗan Scotland sai ta fara amfani da sunansa.

Ga lokuta huɗu da Kemi Badenoch ta yi tsokaci kan Najeriya tun bayan zaɓen da aka yi mata a amatsayin shugabar jam'iyyar adawa ta Conservatives a Birtaniya.

'Rayuwa cikin tsoro'

Kemi Badenoch ta yi kalamai da dama a kan Najeriya a baya, saboda haka babu tabbas kan ko wanne daga cikin abubuwan da ta faɗa ne ya yi wa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima zafi har ya mayar da martani da cewa "za ta iya cire Kemi daga sunanta.

A baya ta yi bayani kan cewa ta taso a lokacin yarunta tana rayuwa cikin tsoro a ƙasar, ga kuma rashawa.

A taron jam'iyyar Conservatives na wannan shekarar, Badenoch ta nuna bambancin ƴancin da ta samu tsakanin rayuwar da take yi a Birtaniya da kuma halin da ta shiga a lokacin da take rayuwa a Legas inda ta ce "kowa a tsorace yake a kodayaushe".

Ta ce a za ta iya tuna lokacin da take zama a Legas "za ka ji yadda ake yi wa maƙwaftanka fashi, sai ka riƙa fargabar cewa gidanka za a shigo idan aka gama da maƙwafcinka."

"Ni ba ƴar-koren Najeriya ba ce"

Kemi Badenoch ta kare kalaman da tafurta kan Najeriya a baya.

Bayan sukar da mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya yi mata, an tuntuɓe ta domin jin martanin da za ta yi.

Sai mai magana da yawunta ya ce: "tana kan bakarta kan abin da ta faɗa" sannan "ni ba mai yi wa Najeriya talla ba ce".

'Ni bayaraba ce'

Shugabar ta jam'iyyar Conservatives ta janyo wani cece-ku-cen a kan batun asalinta bayan ta bayyana kanta a matsayin bayaraba sannan ta nisanta kanta daga duk wata alaƙa da mutanen Arewacin Najeriya.

Ta yi wannan kalami ne a baya-bayan nan lokacin da ta tattauna da manema labarai a Birtaniya.

Kemi ta ce ba ta da wata alaƙa da Arewacin Najeriya, yankin da ta ce wuri ne na masu tsattsauran ra'ayin Islama da kuma Boko Haram.

"Abin na ba ni mamaki yadda kowa ke bayyana ni a matsayin ƴar Najeriya. Na fi alaƙanta kaina da ƙabilata [Yoruba] a kan Najeriya," in ji ta.

"Babu abin da ya haɗa ni da mutanen da suka fito daga arewacin ƙasar, wurin Boko Haram, inda masu tsattsauran ra'ayin Islama suke.

"Lokacin da nake yarinya wani ya taɓa faɗa min cewa sunana sunan gwarazan mayaƙa ne. Su ne suke kare sarauta, kuma wannan ne abin da nake kallon kaina.

"Ina a nan ƙasar ne domin na bayar da kariya, zan iya mutuwa domin na kare ƙasar nan saboda na san abubuwan da ke faruwa a wasu wuraren."

'Ƴansanda sun yi mana fashi'

A ranar 12 ga watan Disamban 2024, Kemi Badenoch ta bayyana karonta da ƴansandan Najeriya a wata tattaunawa mai taken 'Honestly With Bari Weiss'.

"Abubuwan da na fuskanta daga ƴansandan Najeriya ba masu daɗi ba ne, amma a lokacin da na zo Birtaniya yadda ƴansandan Birtaniya ke aikinsu abin a yaba ne.

"Kin san cewa ƴansanda sun yi mana fashi a Najeriya, saboda haka nakan yi mamaki idan mutane suka ce wai suka ce idan wani abu ya faru da ni da ƴansanda a nan, ya faru ne saboda ni baƙar fata ce.

"Na tuna lokacin da ƴansanda suka sace takalmi da agogon ɗan'uwana.

"Matalauciyar ƙasa ce saboda haka mutanen na yin abubuwan da suka ga dama kuma idan aka ba mutum bindiga kamar an ba shi lasisin cin zarafin mutane ne - wannan ba shi ne mizanin da ya kamata mu ɗora ƴansandan Birtaniya a kai ba, ya kamata a ce sun fi haka sosai," in ji Kemi.