'Muna kira ga 'yan Najeriyar da suka zalinci ɗanmu ta hanyar amfani da tsiraicinsa su tuba'

    • Marubuci, Angus Crawford da Tony Smith
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Sashen Bincike na BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 6

Iyayen matashi ɗan Birtaniya wanda ya kashe kansa bayan ya faɗa hannun masu damfara ta hanyar amfani da tsiraici sun yi kira kai-tsaye ga masu aikata laifin daga Najeriya da su daina muzguna wa mautanen da ke da rauni.

Murray Dowey na da shekara 16 kacal a lokacin da ya kashe kansa a shekarar da ta gabata.

Ana tunanin wasu masu aikata laifuka ne daga yankin Afirka ta Yamma suka yaudare shi ya aika masu da hotunan tsiraicinsa, daga nan kuma suka riƙa yi masa barazanar cewa za su yaɗa hotunan.

Iyayen Murray sun kuma soki mahukunta dandalin sada zumunta kan rashin ƙokari wurin kare matasa, inda suka ce su ma suna da babban kaso cikin laifin.

Galibi laifin damfara ta hanyar amfani da tsiraici yakan auku ne bayan an aika wa waɗanda ake hari hotunan tsiraici kafin su ma a buƙaci su aika da nasu.

Daga baya sai a fara yi masu barazanar cewa za a yaɗa waɗannan hotunan a tsakanin ƴan'uwa da abokan arziki idan har ba a biya buƙatun masu aikata laifin ba - irin wannan matsin lamba ne ake tunanin ya kai Murray ga kashe kansa.

Mark da Ros Dowey yanzu sun naɗi wani saƙon bidiyo game da "mummunan "laifin .

Suka ce: “Kuna cin zarafin yara. Kun katse rayuwar Murray.

“Yaya za su ji idan yaronku ne ko ƙaninsu ko abokinsu? Ina nufin wannan zalinci ne, kuma wannan yara ne, kuma ba ƙaramin cin zarafi ba ne.

"Kuna tayar wa da mutane hankali, ƙananan yara, saboda wasu ƴan kuɗi, kuma ba na tunanin akwai al'ummar da za ta lamunci aikata hakan."

Irin wannan damfara ta zama babban abin kasuwanci a Najeriya wanda ya kasance aikin yi ga dubban samari da ake yi wa laƙabi da "yahoo boys".

Ana sayar da dabarun yadda za a shiga aikata laifin a fili a shafukan intanet, kamar yadda binciken BBC ya gano a farkon wannan shekarar.

Yayin gudanar da binciken BBC, an shafe watanni ana tattaunawa da wani mutum a Najeriya da ke da hannu a harkar damfarar, inda aka shawo kansa ya ba da ƙarin haske kan abubuwan da ke faruwa a wannan duniyar.

Ya zanta da abokan aikinmu a Legas bisa sharaɗin sakaya sunansa.

Ya shida masu cewa: “Na san cewa abin ba shi da kyau, amma dai lamari ne na idan ba ka yi ba ni wuri.”

Ya bayyana damfarar a matsayin wata "masana'anta" kuma ya yarda cewa yana ɗaukar shi kamar wasa.

Ya kara da cewa: “Ya danganta da kifin da ka kama. Idan ka jefa ƙugiya a cikin teku. Ka na iya kama ƙaramin kifi ko babban kifi."

An nuna masa saƙon Ros da Markus da aka naɗa kuma ya bayyana mamaki kan ganin hakan.

Ya ce ya "kusan yin kuka" ya ji "ba daɗi".

Duk da haka iyayen Murray ba ƴan damfarar kaɗai suke ratayawa alhakin mutuwar ɗansu ba.

Sun ɗaura wani ɓangaren laifin kan kamfanonin fasaha ma.

Masu damfara ta hanyar amfani da tsiraici suna samun waɗanda za su gallaza ma ne ta hanyar kai hari kan ɗaiɗaikun mutane a shafukan sada zumunta sannan kuma su yi amfani da jerin abokansu da mabiyansu domin yi masu barazana.

Ros ya shaida wa BBC cewa: “ A tunani na alhaki ya rataya a wuyarsu. Fasahar tana nan don su dakatar da yawancin waɗannan laifukan."

Mark ya yi imanin cewa Silicon Valley na iya ƙara ƙaimi wurin daƙile lamarin amma ba za su iya ba saboda hakan ya jiɓanci kashe kuɗi .daga ɓangarensu

Ya ƙara da cewa: "Zai hana su samun ƙarin biliyoyin kuɗi kan da yadda suke samu".

'Babu damar shiga tsakani'

Binciken da Hukumar Kula da Laifuka ta Burtaniya ta yi ya gano cewa ana kai hari ga dukkan ɓangagrorin al'umma ba tare da nuna bambancin shekaru ko jinsi ba, amma yawancin waɗanda abin ya shafa maza ne kuma masu shekaru tsakanin 14 zuwa 18.

Ƴan sanda sun yi imanin cewa ba a kai rahoton laifin ba saboda waɗanda abin ya shafa suna matuƙar tsoro ko kuma suna jin kunyar bayyana kansu.

Mark ya shaida wa BBC cewa ɗansa "da gaske yaro ne mai matuƙar hankali" kuma iyayensa ba su san wani abu na wakana ba.

Ya ce: "Ya haura zuwa daƙinsa, kuma yana cikin ƙoshin lafiya. Kawai washegarisai mu ka same shi a mace".

Mahaifiyarsa Ros ta ƙara da cewa: "Ba mu da damar shiga tsakani, ba mu lura cewa akwai wani abin da ke wakana ba domin mu yi ƙoƙarin daidaita lamarin".

Iyalan Dowey sun ƙaddamar da wani shiri a Edinburgh, wanda ke gargaɗin matasa game da illolin wannan lamarin na damfara ta hanyar amfani da tsiraici.

Shirin ya haɗa rundunar ƴan sandan Scotland da ƙungiyar Crimestoppers da kuma gwamnatin Scotland. Yana nuna haɗarin raba hotunan tsiraici a shafukan intanet kuma yana ba da shawara kan abin da za a yi da kuma inda za a je neman taimako idan masu laifi suka kai wa mutum hari.

Mataimakin babban jami’in ƴan sanda Steve Johnson ya ce abu ne mai wahala amma ba zai gagara ba” wajen gano waɗanda suka aikata laifin – kuma yana da muhimmanci mutane su kai rahoto ga ƴan sanda don taimakawa wajen tattara shaidu da bay7anan da ake buƙata.

Ya ƙara da cewa rundunar za ta riƙa kai hari ga masu aikata laifuka a duk inda suke a duniya.

Mark da Ros sun shaida wa BBC cewa suna da sako ga duk wani matashi da ya samu kansa a cikin wannan mawuyacin hali.

Ma’auratan sun ce: “Ba wani abu da isa ya tunzuraku ku kashe kanku don haka idan wani abu ya same ku, ku ajiye wayar ku je ku kawo wanda kuka amince da shi ku gaya musu abin ya faru.”

"Bai kamata abin da ya faru da Murray ya ƙara faruwa da wasu yaran ba."